Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Abun Dukda ya mata banbarakwai kuma gabanta ya faɗi haka ta sa hannu ta karbi wayan ba tare da tace komai ba.
“Ina kwana ya Farhan!”
Yace
“kina lafiya?”
Ta amsa da.
“Eh”
Ba wani magana suka saba ba, don haka yace
“mammi ne ta matsa a zo a ji lafiyarki”
Tace
“Allah sarki! Ina lafiya gobe ma zamu dawo, an fasa sati Ɗayan”
Duk kallonta suke, har ta kashe wayan.
Se a sannan ta fitar da ɓacin ranta
“am so so disappointed in u sakina nd rahama, kun san bana shan giya don Zubair ya bani na bugu na san ba laifin ku bane amma taya Zaku fara barin shi ya tafi dani na kwana gado ɗaya dashi? Me kuke tunani?”
Rahama tace
“kiyi hakuri muma duk sadda ya tafin daken ba a hayyacinmu muke ba bare mu hana shi tafiya dake”
Sakina tace
“to menene ma don ya tafi dake ɗin, ai tunda kika zabi wannan hanyar dolen dole watarana kin sha kayan maye, ita ma abunda kike yiwa gudan dole ne ya sameki so just chill ki sake jiki, ki waye pls”
“tir da wayewar zina da shaye shaye, kun kuwa san azaba da fitinar dake cikin waennan abubuwa?”
Kallon juna sakina da rahama suka yi kan suka washe da dariya, sakina tace
“lallai ashe ƴar gidan malamai ce”
Tafiya tayi gaban kayan ta ta fara Haɗawa ba tare da tace komai ba.
“Haɗa kayan me kike? Cewar rahama
“gidanmu zan koma.”
“Amma ai sati guda muka ce zamu yi”
“ba zan yin ba”.
Tunda ta fara basu amsa a haka sun san in suka cigaba be gameta ba su samu gagarumin matsala se suka kyale ta.
Knocking aka yi, Raham taje ta buɗe, samarin guda uku ne, duk suka janye en matansu suka bar ta ita da Zubair a ɗakin.
Gabanta yaje ya durkusa bisa gwiwowinshi, cikin lalama yace
“am very sorry! Na san ban kyauta miki ba amma wallahi ba da wani mugun nufi na baki ba, na zata kina sha a lokacin ne kawai ba kiyi niyyar sha ba shiyasa na baki don na tsokane ki, zuciyata zafi take min ina ganinki cikin wannan yanayi Fauxa, na tuba please”
“leave me alone zubair”
Ta faɗa calmly Dukda fuskanta a mugun haɗe yake.
Kanshi ya duƙar daidai kafafunta sai digar ruwa taji.
Da sauri ta ɗago, a take yayi deceiving ɗinta da crocodile tear ɗinshi yace
“am sorry please Fauza”
Tace
“Abunda ya faru ya riga ya faru”
“Kin yafe min?”
Ya tambaya cikin murmushi da yayi mata kyau, kanta kawai ta mayar kan wayanta, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani box me kyau daga idanu zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba yace
“accept this as my apologies dear”
Ɗagowa ta sake yi ta kare mishi kallo, ba laifi Zubair kyakyawa ne, sai de kallo ɗaya zaka mishi ka san crook ne, ga kuɗi ga iskanci.
Hannu ta sa ta karɓa ta buɗe, kasa ɓoye excitment ɗinta tayi tace
“isn’t it that necklace..?”
Wadda take kallo jiya har yake cewa ze mata kyau.
Murmushi ya saki ganin ta saki ranta, ta mishi godiya.
Zama yayi a gefenta suna hira jefi jefi, duk yadda suka so su hanata tafiya a washegarin tace ita sam gida zata koma.
Duk abunda take chan Kasar zuciyarta bakin ciki ne fal na kayan maye da ta sha, ga sallar asuba gari ya gama wayewa, se istigrafi take yi haka dae Zubair yayi ta lallaɓata yana yaudararta bata yi wani fushi mai nisa da shi ba..
Washegari da safe da kanshi ya kaisu har Airport ya mata sayayya mai yawa ya hada da kuɗi, duk da ya burgeta, sai de fa bata nuna ba.
Sauri sauri ya shigo Airport ɗin don shi ze tuƙa Max Air ɗin zuwa birnin Yola daga Abuja, gashi ya so yayi letti, a cikin jirgin ya haɗu da sauran crew ɗin da kuma wadda ze taimaka mishi suka gaisa, he supposed to be a mazauninshi tunda har an soma shiga amma se ya tsaya daga bakin kofan, waya yake amsawa lokaci lokaci ya kan ɗaga idanunshin nan ya kalli masu shigowa ɗaya bayan ɗaya.
Gudu gudu suka karaso don ana final announcement ne, Sakina ce a gaba sai Rahama kan ita, loggage ɗinsu bai da nauyi so kowacce na riƙe da nata ne a hannu, Sakina ce ta fara wucewa ta mika ticket ɗinta, aka bata na seat number ɗinta ta shige, rahama ma ta shigo tayi hakan sai Fauza ta sanyo kafafunta cikin jirgin….
*Toh Alhamdulillah! Free pages sun kare saura ni daku da kuka biya paid, na san kaunar da kuke yiwa labarin ne ya saka ku nuna wannan soyayya sai dai har yanzu ina kara jaddadawa ba zan san kuna kaunar littafin ba idan har baku comment, ni karan kaina ba zan ji kwarin gwiwar yi muku typing ɗin ba due to squeezing time kawai nake nake yi don ina aiki, bani da enough time na kaina, sannan typing in kun ga kun samu da rana to shikenan amma ka’ida sai dare in shaa Allah zan din ga yi don nafi samun time between magrib, isha. Looking forward for ur comments and love
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
12
Daidai tana sanyo kafa shi kuma yana Juyawa, an tambayeshi wani code da se ya duba paper ɗin don be riƙe ba, har ta gama ta wuce seat ɗinta chan karshe be dawo ba.
“Ke kinga wani haɗaɗɗen captain da ya tafi da ni? Wlh ya haɗu karshen haduwa ina ma zan samu ko phone number ɗinshi ne”
Rahama dake kusa da ita ne ke maganan cikin koɗa kyaun wadda take magana a kai da ita bata sani ba.
Tace
“ni ban ga wani captaina ba, kuna da matsala ai ku kam”
Ta faɗa jin sakina ma ta karɓa tana taya rahama gulman wadda bata gani ba ita kam.
Har suka sauƙa yola basu daina maganan captain ɗin nan ba, Sakina Dan Tsoho hotel tayi don chan zata karasa satin da tace zatayi a gida, yayinda rahama tayi gida don duk iyayenta basa ƙasar, cab ne ya sauke ta kofar gida ta sauka tare da miƙa mishi kudinshi ta Janyo loggage ɗinta tayi ciki.
Harabar gidan nasu tsabtsab ba kowa ta tabbatar yanzun haka suna school tunda kwata kwata karfe goma ne na safe, sashen jadda tayi direct a parlor ta taddata kan sallaya ta idar da walaha tana tasbihi, da gudu ta zo ta faɗa jikinta tayi shiru tana sauke numfashi.
Ɗago fuskanta Jaddah tayi cikin farin cikin ganinta tace
“oyoyo oyoyo! Maraba da mutanen Gombe kune da safen nan?”
Kai kawai ta gyaɗa ta sake mayarwa tayi lamo, Jaddah ta ɗago ta gabaɗaya tana kallonta
“lafiyan ki kuwa? Ko baki da lafiya ne kike hawaye?”
Hannu ta sa ta share kwallar tare da karya wuya tace a shagwabe
“kewarki nayi Jaddah na”
Dariya Jaddah tayi tace
“to ba gashi kin dawo ba? Ba shikenan ba? Oya tashi je kiyi wanka ki sauya kaya bari na sa zaliha ta sama miki abunda zaki ci”
Mikewa tayi ta nufi ɗakinta tana cewa
“ya yi yaji pls”
Tana shiga ta jefar da Akwatin tare da dogon hijab da daga Airport ta sanyo shi zuwa gidan, ta shige toilet ta sakarwa kanta ruwa tana lumshe idanu, se yanzu take jin wani sukuni na rufe ta, lallai ta zalunci ahalinta tayi fatali da tarbiyar gidansu, tunda ta dawo daidai take jin rashin daaɗi a zuciyarta na abunda ta aikata amma fa wani zuciyar na kwaɗaita mata daaɗin shi.
Bayan ta fito tayi shafe shafenta ta janyo tsarabar da Zubair ya Haɗa ta dashi, chocolates ne daban daban se wasu designers perfume guda biyu se, hoodie ash na kamfanin Fendi.
Boyesu tayi a wardrobe ɗinta kan ta zaro riga ƙarami fari da wando navy blue ta saka, wandon a kaurinta ya tsaya ya kuma matse ta ya fitar da duk wani shape ɗinta, gashinta ta taje ta sake shi, tana shirin kwanciya Call na Zubair na shigowa wayanta, da sauri taje kofa ta rufe da key kan ta dawo ta haye gado tare da shigewa bargo ta amsa.