Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Romeo and Juliet an gama Zaku iya ɗagowa”
Da sauri ya saketa yana ɗan matsawa ya zabgawa Jafar harara, ita kuma ta dukar da kanta.
An sha gumurzu kan aka cire kwalban tayi kuka sossai wadda har saida yaji a ƙasan ranshi be kyauta ba, bayan an gama ya ɗan Harare ta yace
“taɓararriya kawai”
Bakinta ta tura mishi ya kai hannu kaman ze ɗalle mata bakin tayi saurin saka duka hannunta biyu ta tare tana zare idanu wadda ya saka shi sakin murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko ɗaya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura.
Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa.
Ita kuwa tana zuwa motan ta buɗe baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya ɗauke ta.
Haka ya sa hannu ya ɗauke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buɗe mai gaba ya sanyata.
Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace
“Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?”
Yana gyara Fauza yace
“kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls”
Tace
“in bari mu je gida? Na rasa cikina sbd wannan karuwar….”
“Shutt uppp Fatima!!”
Ya daka mata tsawar da har saida Fauza ta tsorata tare da watsakewa daga baccin da ya cika mata idanu.
Itama cikin kukan baƙin ciki tace
“ba zan yi shiru ba yaya, ba zan yi shiru kayi ta zaluntata ba… Ta ɓarar min da ciki baka ce mata komai ba, asibitin ma ka zo ka ajiyeni kayi tafiyarka wurinta, ni da ya kamata ka ɗauko ka kawo mota baka ɗauko ni ba ka je ka dauko ta a hannu sbd tayi bacci, ni gani ƴar iska marar gata… To Alhamdulillah na gode Allah da baka sameni a watse kaman kofar taxi b……”
Mari yake shirin sauke mata sbd yadda ranshi ya ke tafarfasa Jafar yayi saurin riƙe shi.
Ita dae Fauza bata ko motsa ba banda idanu da take binsu dashi, sbd yadda idanun Fatiman ya rufe bata yi shiru ba tace
“ka barshi ya mareni Jafar, ya mareni tunda ni ce karamar dangarshi me daaɗin hawa, ba se ka mareni zaka nunawa duniya cewa ni ɗin ba jininka bace, ba se ka mareni zan san cewa kana fifita wanchan karuwar ƴar shaye sha….”
Marin da bata sha ɗazun ɗin ba shi ta sha yanzu saida ta kusa kaiwa ƙasa, hannun da ya nuna ta da shi har yana rawa yace
“Ki kiyaye ni Fatima, ki kiyayi ganin ɓacin raina kuma ki rufe min baki ki shiga motar nan mu tafi…!”
Jafar yace
“Haba Faizan in ita ta rasa hankalinta tana faɗar abubuwan da basu dace ba kai be kamata ka biye mata ba, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi har ita ta sauko kan ka nuna mata rashin kyautawar abunda tayi ɗin, zafin kishi ne kawai ke dawainiya da ita da kuma na rashi da tayi ka san dae se ta fi ka jin zafin hakan”
Kallonshi Faizan yayi yace
“zafin kishi? In zafin kishin ne se aka ce a rashin hankali yake zuwa?”
Juyawa yayi kanta yace
“I can tolerate anything but don’t u dare cross ur boundaries… Ki wuce ki shiga mota mu tafi I won’t repeat myself”
Yana kai nan ya buɗe motar ya saka husna da har ta fara kuka, kan ya juya ga Jafar yace
“zamu yi magana”
Daga haka ya zagaye ya shiga motar, ya tayar idanunshi na zube kan hanya, saida yayi kaman mintuna uku da tayarwa har yana shirin jan motan yayi gaba kan Fatima dake kuka ta shiga, ita dae Fauza sannu bata ce musu ba ya tsaya restaurant ya musu takeaway kan suka kofanufi gida.
Yanzu ɗin ma zagayawa yayi ya buɗe ya ɗauke ta, ko Fatiman be kalla ba ya nufi ciki, a kan gadonta ya ajiye ta har ya juya ze fice tayi saurin riƙe hannunshi wadda dukkansu saida suka ji har cikin ƙashinsu.
Fuskanshi ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya tace
“I’m sorry…! Ban san hakan ze faru ba da ban biye mata ba, pls kayi hak’uri”
Ta karashe tana duƙar da kanta ƙasa.
Zama yayi yana ɗan murza hannunta dake cikin nashi Ɗayan kuma ya ɗaura a kan kumatunta da har yanzu yake kumbure ya ɗan shafa dukkansu suka lumshe idanu, wani sanyi ya ji a ranshi wadda be san na menene ba, ɗago idanunta tayi ta kalleshi dasu daidai shima ya buɗe nashi dake lumshe.
Chan ƙasan maƙoshi yace
“it’s not ur fault, haka Allah ya tsara cikin ba me zama bane… Amma me ya Haɗa ku?”
Tiryan Tiryan ta bashi labarin abunda ya faru bata ɓoye komai ba, yadda suke kallon juna a cikin idanu kuma ta bashi labarin ba rawar murya ko wani kame kame ya san cewa babu ƙarya a cikin labarin nata, murmushi ya saki kawai da nufin tsokanarta yace
“Eyye ashe ƴar gurguwa kunnuwanta na ji da kyau tunda har ta ji sadda loudspeaker ke sanar da cewa ita ɗin ta zama matar Faizan”
Da sauri ta zare hannunta tare da kare fuskanta tana murmushi shima yana murmushi yace
“Haba ƴar gurguwa kunya kuma?”
Baki ta turo tana cewa
“ni Allah ni ba gurguwa bace”
Yana miƙewa tsaye yace
“Toh Ladi chogal”
Ihu ta sake tana kukan shagwaɓa ya fice abunshi yana dariyar shagwaɓar tata.
Se bayan ya fita ta saki murmushi ashe ya Faizan haka yake?.
Abincin da ya sayo ya koma ya ɗauko, a plate ya juye takeaway biyu da ruwa ya sa kan tray ya ɗauka ya kaiwa Fauza ɗin, yanzu kam be ce mata komai ba ya ajiye mata ya baiwa husna nata kan ya juya ya fita.
Na Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta dashi Dukda yadda yake jin ɓacin rai na abunda ta mishi ɗin amma be fasa zuwa ba.
Tana zaune tana kuka ya shiga ɗakin, abincin ya ajiye mata kan ya juya shima yaje ya ci nashi, an riga an yi isha so ɗakinshi kawai ya shiga ya watsa ruwa yayi sallah, bayan ya idar ya mike yaje ya duba maganin Fauza ya nufi ɗakinta dashi.
Samu yayi tana sallah daga zaune, toilet ɗinta ya shiga yana yabawa tsaftarta don bayin ta ba zaka ce ana anfani dashi ba ya samu roba ya tare ruwan zafi ya samu Towel ya fito.
Husna tayi bacci ya ɗauke ta ya ɗaura ta kan gado ya sauya mata kaya daidai lokacin ita kuma ta idar.
Da taimakon shi ta koma bakin gado, ya janyo stool ya zauna tare da ɗaukan kafan ya ɗaura kan cinyar shi.
Ruwan da zafi sossai haka yayi ta danna mata tana raki tana yarfa Hannu, da muzurai da komai aka gama dannar ya bata magani ta sha, yace
“dube ta..!”
Baki ta turo kayan bacci yaje ya ɗauko mata ya ajiye mata gefenta kan ya dube ta yace
“akwai wani abu kuma?”
Kai ta girgiza yace
“tohm se da safe Allah ya qara sauƙi”
Tace
“thank you”
Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya maido mata da kofan ya rufe.
Maganin Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta.
Har yanzu tana kuka, zama yayi bakin gadon yace
“Fatima!”
Yadda ya kirata ɗin dole ya sa ta ɗaga idanu, yace tashi zaune.
Mikewa tayi ta zauna, yace
“menene matsalarki? Me yasa kike ganin an miki rashin adalci?”
Kallon tambaya ta ma kake ta mishi, kan ta ɗauke idanunta bata ce komai ba, shima ɗauke nashi yayi yace
“Ki tashi ki ci abinci ki sha magani”
Yana kai nan ya ajiye mata maganin ya tashi ya fice abunshi don ta ƙi magana.
Ya gaji ainun so yana kwanciya bacci ya sureshi, da asuba yana dawowa daga sallah kenan ya hangi ɓacewar mota kaman kuma ta Fatima, me gadinshi ya tambaya ya tabbatar mishi da yanzun nan Fatima ta fice.