Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Baya so ne yayi breaking don iyakacin jarumtar hana kanshi faɗuwa yanayi, maganan ya dake shi ne fiye da yadda yake zato ko tsammani… Baba Prof dake rike da kafadan ɗan uwanshi yana ɗan bubbugawa ganin irin yanayin da ya shiga yace

“Duka wannan magana ba na nan bane, mu je parlor bana so in kara jin wani yace tak a cikinku”
Ya bada umarnin tare da janye baba Alhj suka nufi parlornshi.

A hankali hankali kowa ke binshi ciki Fatima na ta kuka cike da baƙin ciki yau kam kila se buzunsu kilan aurenta ya mutu kenan, ya zatayi da soyayyar Faizan?

Jaddah ce ta taka ta nufi Fauza dake tsaye kanta ƙasa tana kuka a hankali, abubuwa dayawa ne suka haɗe mata da kananun shekaru, Zuciyarta, gangar jikinta da kwakwalwarta duka babu wadda yake aiki bisa daidai.

Meyasa Faizan ke min haka? Meyasa a koyaushe fahimtar shi a gareni gurguwa ce? Bata da amsa, kuma a yanzu bata buƙatar sani.

Jaddah da ta riƙeta ta ɗaga kai ta kalla se kawai ta sake rushewa da kuka, jadda ta tsorata ainun da kallon yanayin Fauza ɗin fuskanta ya kumbura sossai kaman wacce ta kwana biyu tana kuka.

“Mu je Fauza”
Ta faɗa tana kokarin jan ta suyi parlorn Baba ɗin saide ta kasa taka kafar ta sbd azabar zafin dake ratsa ta, wani kukan ta sake saki..

“Lafiya me ya sameki?”
Kasa magana tayi se kuka.

“Jaddah su baba, ba hijab jikina”
Se a lokacin Jaddah ta lura ko dankwali babu a kanta gashinta a tufke kuma wlh ta nemi hijab ɗin nata ne bata gani ba gashi ta gigice jin hayaniyar da gidan ya ɗauka sossai.

“A ina kika bar hijabin?”
Kanta a ƙasa ta nuna sashen en mazan.

Ajiyar zuciya Jaddah ta sauke kan ta nufi ɗakin Faizan ɗin don duba mata hijabin.

Abunda ta ci karo dashi shi yayi mugun razana ta, cikin wani irin tsantsar mamaki take karewa beddings ɗin kallo, se kuma hawaye ya fara zarya a idanunta, Juyawa tayi tana kallon bayanta kaman zata ga Fauza a wurin a hankali ta furta
“Allah sarki baiwar Allah!”

Lallai Allah Allah ne, in ba shi ba waye ze iya wanke Fauza daga wannan zargi da aka yi ta mata aka ta shiga hakkinta akan abunda bata aikata ba a idanun dumbin jama’ar gidan nan?
Bedsheets ɗin ta yaye, chan lungun gadon ta samo hijab ɗinta ta fito.

Saida ta kai Bedsheets ɗin toilet ɗinta kan ta dawo ta sanyawa Fauza da har yanzu ke kuka hijab ɗin tare da rungumota
“kiyi hakuri kin ji? Kiyi hakuri Allah ya miki albarka.. Lallai kina cikin masu hakuri Fauziyya sannu.. Ki daure mu karasa na san mu suke jira a parlorn”

Da ƙyar take iya taka kafar da take ji kaman tana takawa ne bisa ƙayoyi, duk taku ɗaya kuwa ita kaɗai ta san zafin dake ratsa ta har cikin kwakwalwarta.

Ilai kuwa sun samu parlorn tsit se kukan Ammi ke tashi, kana jin kukan zaka san na dana sani ne me yawa, ashe hassada ka iya jaza maka bala’in da baka san hawarshi ba bare Sauƙar shi?

Duk da kallo suka bi Jaddah da fauza ɗin kowa na mamakin me ya sameta haka ita kam fuskanta a ɓoye jikin Jaddah ji take kowa ya kalleta ya san me ya faru, shi kam be iya ya ɗaga kai ba har suka zauna.

Bismillah baba prof yayi ya fara da Adu’a kan ya fara da jan hankali akan wannan abu da ya faru a gidan nashi yau wadda ba’a taɓa samun hatsaniya haka ba, ga dae Mammi a sadda aka fitar da ita kaman zata mutu amma yanzu kuma Alhamdulillah da kanta take zaune.

Ammi ya kalla yace
“Ruqayya ke ce babba, don haka dake zan soma, me yake faruwa? Me Shamsiyya ke nufi da kalaman ta? Ko jikina duka kunnuwa ne ba zan taɓa aminta Cewar Fauza zata iya cutar da Aisha ba abunda kuma ba ze yiwu ba kenan so ina so ku faɗa min gaskiya me ke wakana a tsakanin ku?”

Ammi cikin kuka tace
“Wallahi Yaya(prof) ban taɓa sanin cewa za’a iya anfani da ƙi da kuma hassadar da nake yiwa mahaifiyar Faizan a nemi lawye ni ba, lallai duk wadda ya ɗauki hassada abun yi to yayi gaggawar tuba ya kuma kori sheɗan… Ba kowa bane ze nuna yana son ka a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance haka, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin ne ba. Zan fara da neman gafararku ku yafemin don Allah”

Duk kai kowa ya gyaɗa kwarai haka magananta hassada mugun ciwo ne, amma ba wannan tukuna suke son ji ba.

“Ɗazu bayan na idar da sallah, se na duba ban ga redio na ba se na tuna ashe Shamsiyya ta ara da rana taji wani program a ABC don nata ya ɗan samu matsala har ta ba Farhan ma ya kai mata gyara.. Kaman Allah ne ya turani ina zuwa na samu tana yiwa Fatima faɗa akan tana kokarin ɓata mata aiki da tun kan ta shigo gidan nan take ginawa, na so shiga se kuma jin ta ambaci sunana a farkon fari yasa na dakata.. Ga abunda take cewa in na mata ƙarya kar Allah ubangiji yayi min gafara…

‘Fatima kin san abubuwan da na aikata kuwa? Toh buɗe kunnen ki ki jini ina ga baki sani bane yasa kike min wasa da aiki, tun farkon fari Professor na so aure se kuma ya fi karfina da naje aka duba min se aka tabbatar min da Cewar babu aurenmu da professor har duniya ta nade sede ya hangi aurena da Sulaiman har da zuri’a, tun a lokacin na sa ya bincika min matar Sulaiman wato ni kenan(Ammi ta nuna kanta) tashin farko ya faɗa min cewa tana da halin saurin fushi sannan kuma ta kan ji haushin mammi ganin kaman ta fita a komai a gidan har miji, kai natse na mishi umarni da ya kulle zuciyarta, ni kuma zan koma in kashe aurena in dumfari gidan se na tabbatar duk wasu arziki nasu ya kasance cikin tafin hannuna.

Kai tsaye ya samu nasara sbd shaidan dama ya riga ya darsawa Ammin hassada a ranta, Zuciyarta ya zama baya jin komai ƴaƴan da na haifa ma ban damu dasu ba bare miji da surakai…”

Kuka ne yaci karfin Ammi tana tuna yadda take wasarere da rayuwar ƴaƴanta barin ma Fauza da ta fi bukatarta da kowa, Amma ta kan gode Allah dayake ba azzalumin bawa bane ya baiwa Fauza Jaddah da mammi da kuma baba prof.

Auntyn ce ta ɗan sosa kanta kan tace
“Ai baki faɗi komai ba ruqayya, wannan kaɗan ne daga cikin kaidi na.. Bayan na sa an rufe zuciyarki ana kuma anfani da kwakwalwarki se na zo na aure miki miji, tashin farko na fara kokarin cusa Fatima ga Faizan don na san ta hakan ne kawai zan samu abunda nake so, se bokana yace min idan dae har Mahaifiyarshi na da cikakken lafiya burina baze cika ba don ita ɗin a tsaye take a cikin gidanta kan mijinta da yaranta.

Dukda ya tabbatar min da cewa ko an nakasta kafafun nata zata iya cigaba da nemawa yaranta kariya wurin rabba se na ce ya saka mata ciwo me tsanani wadda baze bar ta natsuwar lafiyar nema musu sauƙin ba, kwatsam se muka samu ciki ni da Ruqayya, da na koma ya duba min se ya tabbatar min yarinyar cikin Ruqayya masifa ce ga rayuwata don itace zata yi silar tabarbarewar duka aiki na in ban yi wasa ba, kai tsaye na nemi a ɓarar da ita ta bi rariya yace in bada kwanaki, duk wani hanya da ze bi don zub da cikin babu nasara ko da ya faɗamin nima ban zauna ba, hatta da maganin zubar da ciki na saka overdose na bata a kunu sede cikin nan ya ƙi barewa abun ba daaɗi wai mahaukaci ya ci kashi, duk inda muka buga cikin nan yaki ya lalace se ya kawo shawarar a dasawa mahaifanta tsanar ta musamman uba, suyi ta mata mugun fata ita kuma tun daga cikin za’a sa mata taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected