Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“ni duk babu ruwana da wannan, ko ki nema min mafita ko in koma gidan mahaifina nima in barki ki fama da naki iyayen… Ba zan iya ba wallahi”
Da kyar Aunty ta sakata amincewa zasu je su ga likita, suka shirya da kafa suka je wani asibitin gomnati, sun sha wulakanci kam su da suna zuwa asibiti za’a karɓe su hannu bibbiyu se gashi cleaner ma na asibitin na zagin su, test aka bata bayan sun yi, tashin hankalin da ya ziyarcesu a sadda suka ji sakamakon result ɗin Allah ne kaɗai ya sani.
Ciwon daji ashe take dashi gashi an mata allurai a sadda tayi hatsari shine mafarin hauhawar ciwon. Tashin hankali wacce ba’a sanya mishi rana…
***
Jin yana shirin zarcewa wani babin ya sakata janye jikinta idanunta a ƙasa, hannunta dake cikin nashi take shirin zamewa yayi saurin sake gimtsewa a hankali ya buɗe idanunshi da suka birkice yace
“Fauzaaaa…!”
Ya kira sunan murya a sarƙe, bata iya ta kalleshi ba ta amsa a hankali, yace
“kin yafewa yayanki? Kin huce?”
Shiru tayi kan ta ɗaga kai a hankali, mikewa yayi ya taka ɗaya ya haɗe kirjinshi da bayanta ya sanya hannu ya zagaye kirjinta a kunnenta ya raɗa mata
“thank you wifey! Thank you so much… I LOVE YOU”
Shiru suka yi a haka na sama da mintuna biyar kan a hankali ya saketa, bata iya Kallonshi ba ta fice da sauri tana jinshi yana cewa ta shirya gobe da safe zasu wuce..
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
https://chat.whatsapp.com/BjpWJdHnjtpKNK4iCeqNwh
DƘ
34
Washegari
Kaman yadda ya faɗa da safe ya fito a shirye, sashen Ammi ya fara zuwa suka gaisa sbd weekend ne su baba ma suna gida, ya jima sossai anan kan ya musu sallama ya nufi sashen iyayenshi suma duk ya musu sallama akan zasu wuce yau, duk Kallonshi suke da mamaki saide basu ce komai ba se farin ciki dake shimfide bisa fuskokinsu aka ce tsakanin mata da miji se Allah to shine suke kallo.
Daga nan sashen Jaddah ya wuce, a parlor ya sameta suka gaisa tace
“Ba dae tafiya ba? Na ganka shirye tsab kaman sabon ango”
Tsadaddiyar Murmushi yayi yana kallon jikinshi don be ga wani sabon shiga da ba sabonshi bane, sanye yake da wani ɗanyen bowel sky blue an mishi dinkin boda ya zauna mishi sossai, hula zanna a kanshi ya murza ta da kyau se agogo da wayoyinshi dake a hannunshi banda kamshinshi dake baza parlorn babu abunda kake ji.
“Kika sani ko zan mai dake ɗakinki a yau ɗin?”
Ya bata amsa cike da tsokana, haɓa ta rike tace
“zancen kake nema ai ni na jima da raba gari da kai bana auren nan, ina ni ina zama da miskilin miji ka fi mahaukaci ban haushi? Barni in lallaɓa da su Fahad yauwa…!”
Yana murmushi yace
“ni fito mun da matata mu wuce”
“wai ina Zaku wuce?”
“Dama daga ina muka fito Jaddah? Na kula na zauna jiran ki se mun yi missing flight”
Tsam ya mike ya nufi ɗakin Fauza da kallo baki sake Jaddah ta bishi kan ta fara gyaɗa kai tana jiran ganin ikon Allah.
Tsaye take a gaban madubi sanye da zani da riga na wata Tsadaddiyar super, kanta ba dankwali tayi loose parking wadda ya fitar da wasu daga jikin gashinta ya sassakesu bisa wuyanta da fuskanta, tsayawa yayi Chak hannayenshi zube a aljihu yana kallonta cike da so da ƙauna, ji yake kaman ya tsaga kirjinshi ya sakata ya huta da azababbiyar kaunarta.
Takawa yayi a hankali ya nufe ta ganin yadda take kokawa da zip, bata ji zuwanshi ba se jin hannayenshi masu taushi tayi cikin nata, lumshe idanu tayi sbd yadda sanyinsu suka ratsa har ɓargonta ta shaki kamshi me cike da natsuwa wadda ba tantama daga gareshi ne sbd ita bata taɓa jin irin turarenshi wurin kowa ba, haka suke ne ko combination da yake na musamman ne suka bada wannan sassanyar kamshin bata sani ba.
A hankali ta buɗe idanun ta sauke su tarrr bisa kamilalliyar fuskar shi ta mirror ɗin..
“May I?”
Yayi tambayar yana nuna zip ɗin da idanu, kai ta gyaɗa tare da ɗan murmushi.
Zip ɗin yake ja mata idanunshi kafe a fatar bayantan, bayan ya gama se ya kara taku ɗaya ya haɗe gab ɗin dake tsakaninsu ya sanya hannu ya zagaye ta tare da ɗaura haɓarshi bisa kafadar ta ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke.
“Good morning yaya”
Seda ya ɗan juya idanu kan yace
“morning but the Yaya is not accepted, bana so a bani wani sunan precious”
Murmushi kawai tayi, yace
“an gama da zip, then what?”
Ba tare da ta ce komai ba ta nuna mishi sarka dama ta saka dankunne, hannunshi kawai ya miƙa ya ɗauko gashin da suka zazzame yake ɗan tattarewa da hannunshi yana mai dasu sama kan ya fara saka mata sarkar idanunshi kan wani baƙin tawadar Allah dake ɗige daga ƙasan kunnenta, Sam bata ankara ba taji saukar peck a daidai wurin, bugun zuciyarta seda ya so tsayawa.
Sake komawa jikinta yayi yace chan ƙasan maƙoshi da idanunshi da suka fara sauyawa
“am done baby, sai me?”
Tace a hankali itama
“sauran ba lallai ka iya ba, let me finish”
Be saketa ba ta dauki wani silk black rowsleeke ta mishi ɗaurin Zahra buhari, yana ta kallonta, da idanu ta nuna mishi blue and black embroid lafayarta dake ajiye bisa gado, da kanshi yaje ya ɗauko zata karɓa yace
“let me do it for you sweetheart”
Ta ɗan wara idanu tace
“in ba kana so in je in faɗi bane Yaya bani kayana in ɗaura”
Ɗan dariyar maganar yayi yace
“Haba yarinya tsawon rayuwata tun fa da na tashi nake ganin Jaddah da mammi na ɗaurawa in har ban ɗauka yadda ake ba kenan kwakwalwar kifi gareni”
Dariya sossai ya bata wadda seda ta dara, gyara tsayuwar ta tayi tana jiran ganin ikon Allah, tsab kuwa ya ɗaura mata lafayar ya zagayeta dashi, ba karamin kyau tayi ba.
Kallon madubi tayi tana murmushi kan ta ɗaga mishi hannu alamar jinjinawa ya taɓe baki irin ba na faɗa mikin nan ba, bangles ta saka ta ɗauko black handbag da black shoe ta saka, hannunta ya riƙe yana kare mata kallo.
“Kin yi kyau kaman Fure precious pearl”
Tayi murmushi tace
“thank you yaya, and kaima ka yi kyau”
Murmushi suka sakarwa juna kan suka fito, Jaddah baki sake take Kallonsu, Fauza ta kasa ce mata komai se shine ya sallameta, har suka fice bata ce komai ba seda suka fita ta saki murmushi, lallai a gaida yaran zamani.
Daga mota ya jirata ta shiga wurin Ammi sama sama, tayi ta saka mata albarka kan ta wuce wurin mammi itama albarka ta sha, ta shiga wurin sauran matan a tsai tsaye daga nan ta yada zango wurin iyayenta a parlorn baba prof, nasiha suka mata kan suka sallameta.
Fitowa yayi musamman ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna, kan ya zagaye ya shiga shima bayan ya zauna tare da sanya hannunshi cikin nata, kan kafadar shi ta kwantar da kanta tana kallon gidan tana tuna irin rayuwar da tayi cikinshi zuwa yanzu, Farhan ne ke tuka su har zuwa Airport kan suka yi sallama.
Ko da suka isa ma be barta ta gyara gidan da yayi kura ita kaɗai ba, a tare suka yi aikin tsab suka kamalla suka yi girki marar nauyi kan kowa ya wuce yaje yayi wanka, kusan a tare suka fito ta shirya musu abincin a ƙasa suka zauna suka ci, bayan ta tattare wurin ta nufi komawa ɗaki ya sanya hannu ya dawo da ita jikinshi yana gyara kwanciyarshi yadda itama tayi lub bisa kirjinshi yace