Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
16
A natse suke saukowa jirgin, Ya fadila na riƙe da hannunta da kallo ɗaya ka mata zaka san cewa wannan ɗin amarya ce, don kwalliyarta na ban mamaki, ba fa na fuska ba lafayarta kaɗai ka kalla ze tabbatar mata da ita ɗin Amaryar babban gida ce.
Hannunta dake riƙe da jakanta ya bayyana lallenta me kyaun gani, chan jikin mota Faizan da Fatima ke tsaye suna jiran su har yanzu mita take mishi
“habeeby ka san halin Fauza, wlh tsoro nake ta tarwatsa mana gida muna zaman lafiyanmu, ba wai ina ja da shawaran Baba bane amma raba mana gida shi ya fi alkhairi”
Ya ɗan kalleta sbd tausayin da take bashi don ya san fitinar Fauza babu wadda ze shaƙa dayawa irin Fatima duk yadda kuwa yayi, yace mata cikin natsuwar shi
“Na sani Fatima, amma ba mun gama maganan gida ba? Baba be lamunce min raba gida ba tunda tun tasowarku a tare kuka taso da Fauza kowaccenku kuma ba baƙuwar ɗaya ba ce, na san baki da fitina kiyi hakuri ku zauna tare har ku samu fahimta”
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗauke idanunta daga kanshi, se suka sauka kan su Fauza dake tahowa yadda take tafiya kaman ƴar sarki dole ya fusgi hankalin jama’a ga kyau tayi, abunda ta san zata nunawa Fauxa hasken fata ne kaɗai ko tsawo Fauza ta ɗara ta Dukda ta fi ta shekaru, dama kuma Hausawa sun ce tsawo rabin kyau, da sauri ta maida kallonta kan Faizan se taga su yake kallo shima.
A take ranta yayi baƙi kirin, ta tabbatar ba don Fauza bata son Faizan ba da se ta saka mata hawan jini in ta gane tana mutuwar kishin shi, hannunshi ta kama ta rike wadda ya saka shi ɗauke lumsassun idanunshi daga kan su Fauzan ya maida shi kanta.
“Tunda sun taho mu shiga motar habeeby kafafuna sun fara ciwo”
Ya juya cikin kulawa da hakkin shi yace
“so sorry, na barki a tsaye”
Motar ya buɗe mata ta shiga ya rufe, motar bayan wadda na abokin shi ne Faisal shi ya nunawa ya fadila suka shiga, shi kuma ya zagaye suka zauna da Fatima wadda hakan yayi mugun yi mata daaɗi har suka isa gida tana gayamishi abubuwan da likita yace ta dinga yi a kan ɓarin da take yawan yi.
Bayan sun sauƙa a tamfatsetsen gidan nashi dake maitama da kanshi ya musu jagora zuwa ciki Dukda ya fadila da ita aka zo jeren na Fauza, a bakin kofa Fauxa ta ja ta tsaya a hankali tayi ta karanto adu’o’in da Baba prof ya umurceta ta karanta kan ta shiga gidan, bayan ta gama tayi sallama tare da sa kafar dama se ta lumshe idanu, shikenan fa ita kuma wani sabon baabin qaddara ya buɗe mata, Allah kaɗai ya san abubuwan da zasu faru a cikin wannan gida kuma Allah shi kaɗai ya san ko gidan zaman ta ne ko ba gidan zamanta bane, ko a mafarki bata kawo auren mijin Fatima ba, ba ma wannan ba kuma wai Ya Faizan har yanzu kwakwalwanta be gama ɗauka ba bare zuciya da gangar jiki.
Tamfatsetsen parlor ne wadda ya ɗauke set ɗin kujeru har biyu, ya ƙawatu sossai masha Allah, kofofi uku ne a parlorn daga tsakiya wani hadadden staircase ne golden color wadda ya tafi a karkace har zuwa sama, dukkansu shi suka bi zuwa madaidaicin parlorn dake saman wadda na kasa ya fishi girma sede ya fi na kasa haɗuwa, dining section ɗin ma kaɗai abun kallon ne haka TV stand ɗin daga ka ganshi zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba, console har biyu ne a parlorn ɗaya a dining section ɗaya daga tsakiyar stairs in kana haurowa, kofofi huɗu ne a saman, na farko daga dama ya fadila ta buɗe suka shige da Fauza da ya kaka.
Yayinda shi kuma ya shiga na biyun yana cewa Fatima ta duba ko me aikinta ta gama abunda su ya fadilan zasu ci, ta amsa da to tana shiga nata ɗakin wadda yake next to nashi, jakanta kawai ta ajiye ta fito, ta san shi. shi mutum ne me matukar son yaga nashi a gidan shi, yana son en uwanshi har bata san yadda aka yi ya rabu dasu yake ketare kasashe da sunan aiki ba, idan yaga nashi a gidan se abunda babu ne baya saya, ya dinga tambaya kuma ko akwai abunda kake bukata ayi maka, hakan ya sa itama dole take yi don bata son ɓata mishi Sam.
Kitchen na ƙasa ta je don ita kaɗai ke shiga na saman, ta samu me aikin nata ta gama duk wasu abunda ta faɗamata tayi a waya don haka a tare suka kwaso suka hauro sama dashi kwankwasa kofar tayi tare da buɗewa da sallama.
Su ba baƙin juna bane don haka tun tuni ma Fauza ta yaye lafayarta tana kwance a kan tamfatsetsen gadonta tana karewa tsaruwar ɗakin nata kallo, Baba prof da jadda sun yi kokari don su suka mata komai, dukda be so jadda ta sa hannu ba amma tace auren Fauxanta guda in bata fasa asusu ba na wa zata fasa kenan.
Mammi kuwa ita ta zubewa ya fadeela kuɗi akan wadda Faizan ya tura mata da umarnin Baba prof ta Haɗa mata lefe na gani na faɗa, kamshi da kyaun ɗakin kaɗai ze tabbatar maka da lallai nan ɗin na Amarya ne, akwai set ɗin kujeru akwai TV akwai kuma fridge a ɗakin, daga dan lungu window kuma akwai coffee table ɗaya da kujerun shi guda biyu masu kyau se karamin kofa da ze sadaka da madaidaicin balcony ɗinta wadda be wuce na tsayuwar mutum ɗaya ba an tare shi da wani black and gold glass.
Kofan bayi kuma na daga kudu, duk yadda Fatima take Tunanin tsaruwar ɗakinta se taga na Fauza ya fi nata don ko ba’a faɗa mata kudin kayan nan ba ta san ba laga laga bane Dukda natan ma masu kyau ne amma na Fauza sun fi nata, ash ne da gold ɗakin haka labulayen gold da light ash, dressing mirror ɗin yayi mata sossai kaman ta ɗauke, idanunta kafe kan show glass na zamani wadda aka cika shi makil da wasu hadaddun turaruka wuta take rayawa a zuciyarta; lallai an nuna mata wariyar launi a nan wurin, an nuna mata kuma Fauxa ce yar gida kuma er gata.
Da kyar tayiwa su yaya fadilan sannu ta ajiye abubuwan hannunta, daidai lokacin me aiki na shigo da saura tace
“ya fadeela ku ci abinci, bari na ɗan sha magani don har yanzu cikina ciwo yake”
Cikin tausayawa suka mata sannu ko kallonta Fauza bata yi ba har ta fice.
“Fauziyya ya kamata fa a ce zuwa yanzu duk wani baƙin halinki kin baro shi chan yola kin nemi natsuwa da salama kin ɗaurawa ranki, daga Fatima har Faizan yayyunki ne suna da ikon hukunta ki da duk iskancin da zaki yi, kina ƴar fitsitsiyarki har kin san kishiya na ciwo ko sannu bazaki ce mata ba?”
Faɗa sossai take mata wadda wacce ake wan ta lumshe idanunta kawai tana tunanin yadda zamanta ze kasance a gidan, ko sauraron ya kakar dake faɗan ba yi take ba.
Bayan ta gama suka ci abinci wadda Fauziyya bata ci ba, bayi yaya kaka ta shiga don yin alwala yayinda ya fadeela ta ɗago Fauzan ta zaunar da ita.
“Fauza kar mu fara haka dake mana? Kin manta kin ce zaki zauna lafiya dasu bazaki neme su rigima ba in har ba su suka neme ki ba?”
Tace
“ban manta ba, amma dae kin san tun da ba magana nake mata ba me don ta ce cikinta na ciwo zan buɗe baki in ce mata sannu bayan bata kasa dani ba? Yaya fadila don Allah ku Rabu dani in ji da abunda ya dameni, matar nan kuma ta ci darajar Jaddah wallahi”
Tana kai nan ta koma ta kwanta abunta, girgiza kai ya fadila tayi tace
“kina da aiki wallahi, amma ba komai duk sadda kika so zaman lafiya da samun kwanciyar hankali se ki neme ni”
Daidai lokacin ya kaka ta fito, Ya fadeela ma ta shiga suka zo suka gabatar da sallah, suka ɗan kara kakkabe mata ɗakin don akwai injin shara a ciki, kuma ya fadila daman su dashi suke anfani a lokacin ne ma ta mike zaune tana kallon yadda ya fadeelan ke operating, bayan sun gama suka kara gyara mata wardrobe ɗinta da rabin shi glass ne ita kanta bata taɓa ganin ɗakin da ya burge ta irin natan ba, ta kuma sanyawa baba da jadda albarka don sun zuba kudi ba kaɗan ba a kayan nan, abunda kuwa yafi burge ta shine lefe don yadda take son gayu haka ya fadeela ta zaɓa mata isashun kayan gayu da ado.