Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Chan baya inda haske be cika yawa ba ta je ta tsaya idanunta zube bisa farin robar da aka rubuta sniper da zanen ƙwari a jiki, hawaye masu tsananin zafi ne suka saukar mata maganganun mahaifinta na ƙarshe gareta masu kaifi da ƙuna na amsa kuwwa a kunnuwanta kaman yanzu yake yin su…

“Fauziyya ban san cewa kin tabbata marar kunya fitsararra ba seda kika tsaya gaban su jadda da yaya kina ikirarin kashe kanki saboda abinda yake gata ze miki, kina Tunanin ko wasu iyaye ne zasu yardar ma ɗan su auren mace irinki? Ko ni.. (Ya nuna kanshi da hannu) da Farhan ze zo min da zancen auren mace me makamancin halayenki Fauziyya ina miki rantsuwa ba zan amintar mishi ba, in har kin haifu don Allah ki kashe kan naki in aka ɗaura, jaliha marar tunani.. Daga sadda kika kashe kanki daga sannan ni kuma na zare duk wata alaqa tsakanina dake, zan tsinewa gawarki tun kan a binneki, wanka da sallah ba de a gidana ba don ba zan taɓa yiwa kafira Adu’a ba, kaman yadda kika san hukuncin duk wadda ya kashe kanshi ya mutu kafiri… Don Allah karki faasa, fice ki bani wuri…!”

Kuka take yi sossai tana jin yadda zuciyarta ke mata ciwo, meyasa kowa ya gagara fahimtarta? Meyasa se ita? Hannayenta na rawa ta buɗe roban sniper ɗin ta nufi bakinta, duka jikinta na mugun rawa gwara ta mutu ta bar musu duniyan da wannan bakin cikin, motsin da taji a bayanta yasa tayi saurin juyowa se idanunsu suka sarƙe cikin na juna.

Hannunshi zube cikin wandon Fararen pajamas dake jikinshi masu sulbi da suka fitar da kirarsa na kakkarfan namiji me zaati da charisma, idanunshi masu kaifi ya fara saukewa kan hannunta kan ya ɗago ya tsura mata su na mintuna ya ɗaukesu tare da jan tsiririn tsaki, cikin takunshi na zaratan maza ya nufo ta har kaman ze goge ta kan ya ɗan ja kuta yace cikin muryarsa me rikitar da mata..

“Mutuwa se ta fi miki sauƙi da aurena! Rayuwar ƙabari se ta fi miki jin daaɗi idan kika mutu kafira da irin rayuwar da na tanadar miki muddin kika sake aka shafa Adu’ar aurena dake! Faizan be yi zina ba da yardar Allah ba ze taɓa auren mazinaciya ba, ki saka wannan a bayan thick lunatic skull na ki…”
Yana kai nan ya tsirtar da miyau ya wuce abunshi ba tare da ko waiwaye ba.

Fitinan da Fatima ta dasa mishi kaɗai ya ishe shi, idan ta mutu se ya fi kowa farin ciki wallahi, ihunta yaji hakan kuma be saka shi waiwayawa ba har ya shige sashen samarin gidan inda nan ɗakin shi yake tun kan yayi aure har yanzu.

A kan gwiwowinta ta zube tana kuka me cin zuciya wani irin jarababbiyar kaddara ce wannan? Wadda ake yi mata murnan samun shi kenan a matsayin miji? Wadda shine ya zama duk wani silar taɓarɓarewar farin cikinta, idan da be tsoma kanshi cikin tsarin rayuwarta ba da duk hakan bata faru ba..

Da sauri ta sake kai roban bakinta tana shirin apawa taji an yi chilli da robar, da sauri ta ɗago se taji sauƙan mari bisa fuskanta dake suntume already.

“Fauziyya??? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!”
Ko bata ɗago ba ta san jadda ce daga muryar, fusgo ta tayi suka zagaya zuwa kofan sashenta suka shiga, tsallake mutanen dake parlorn suka yi suka wuce kofar ɗakin Fauza dake sashen wadda shima mutanen su na Maiduguri ne ciki suka shiga ɗakin jaddar, kan gado ta ajiye ta tace

“Fauziyya kina da hankali kuwa? Meyasa kike shirin kashemu tun kwanakin mu be ƙare ba? Ki bar mu muji da abu ɗaya mana! Kin kuwa san hukuncin ki daga sadda kika aikata abunda kika aikata kuwa? Wuta fa! Kin kuwa san menene dawwama a wuta na har Abada? Haba Fauziyya! Ina iliminki? Wani bala’i ne yafi na jefa kai ga halaka? Akan auren ɗan uwanki saboda laifin da ke kika janyo?”

Cikin kuka sossai take girgiza kai hannayenta gabaɗaya a kanta duniyar gabaɗaya yayi mata zafi ji take kaman an rufe ta ne a cikin kurkuku me cike da tsananin duhu da zafi, bata iya magana ba Jaddah ta sake cewa

“ba don naji ihun ki na fita ba da yanzu ba wannan maganan ake ba Fauziyya waye ya kawo miki wannan abu? Taya ya zo hannunki?”

Seda ta daka mata tsawa kan ta faɗa cikin dasashiyar muryarta..

“Sakinah!”

“Yanzu waennan ƙawayen arziki kenan Fauziyya?”
Sassauta muryarta tayi tace

“Fauziyya duk abubuwan nan da suke faruwa ki saka a Ranki Allah ne ya tsara hakan ba wai yin mu ba, ina me tabbatar miki kuma Faizan shine alkhairinki in har kinga an ɗaura auren nan to tun farko rubutacce ne daga sama! Wlh idan na ganki cikin wannan hali hankalina tashi yake”

Tana girgiza kai saboda babu wadda ze iya hango abunda take hangowa ta fara cewa
“Meyasa se Faizan? Meyasa Jaddah? Don Allah ki taimakeni Jadda, aure fa ba wai ana yinshi don gobe a fito bane a’a, ana so in ka yi shi ku kasance abadan abada har se mutuwa ta raba, taya kuke hango min farin ciki da zama na har abada daga Maƙiyi na wadda burinshi ko da yaushe ya ga hawaye bisa idanuna? Mutumin da be taɓa ƙaunata ko da na second guda ba, Jaddah idan kuka hana ni mutuwa tabbas zan gudu!”

Bakinta ta buge cikin faɗa tace
“Haba Fauziyya ke kam meyasa kike da taurin kai ne Haka? Auren nan se an ɗaura tunda har iyayenku sun riga sun zartar, tun farko wa ya janyo? A tarbiyarki ban taɓa Tunanin zaki aikata abunda kika aikata ba, gwara ki sakawa zuciyarki salama ki amshi wannan aure don ko gawarki ne na yarda a kai gidan Faizan da irin watsewar da zaki zauna ki mana, kuma babu uban da ze amince da aurenki in har yayi bincike akanki gwara tun wuri mu rufawa kanmu asiri, daga yanzu in kara ganinki ko da a kofar ɗakin nan ne ki gani…”

Tana kai nan ta hau gado ta kwanta tare da kashe wuta, anan Fauza ta cigaba da zama lokaci lokaci tana share hawaye zuciyarta baƙi kirin har bata san sadda bacci ya sureta ba kanta bakin gado tana zaune daga ƙasa.

Sam bata san an yi asuba ba don Jaddah bata tashe ta ba sanin bata sallah, don seda babanta yayi mata har gwajin ciki da HIV kan ya saduda da hana Faizan aurenta Dukda iyayenshi basu damu da duk wannan ba.

Hayaniyar da take ji daga tsakar gidan da salati ya sakata farkawa Sam bata so tashi ba amma jin hayaniyar kaman tayi yawa ne ya sakata mikewa tana yamutsa fuskanta da ya jeme ya rame saboda tashin hankali ta nufi waje, a iyakar sanin ta in har kaji ana hayaniya a gidan Baba Prof to da Fauziyya ne yau kuma to me ke faruwa?

Daga kofar gate na Jaddah ta ja ta tsaya tana kallon matan dake tsakar gidan wasu kuma sun fi yawa a kofar sashensu, tana shirin Juyawa don bata ga abunda ake ba se ta hangi tahowarsa da Fatima a hannu gabaɗayanshi a rikice kana ganin fuskanshi ka san al’amarin dake nufo shi baya kaunar ta ko na miskala zarratin, da ta kura idanu se taga kaman jini ne ke gangara daga jikin Fatimar alamu wannan cikin ma da ya kwallafawa rai ya tafi.

Baki ta taɓe tana jin burbushin farin ciki a zuciyarta, ko yaya shima ya shiga cikin baƙin ciki kaman yadda take ciki, tana shirin Juyawa ta koma taji wata daga cikin en uwansu na cewa
“khaihh na tausayawa yarinyar nan, kishiya ba karamar abu bace a wannan zamani bare ma irin kishiyar da kuka tashi tare matsayin ya da kanwa, iyayenku mata kuma suna auren miji guda”

Ɗayar wacce ƴar uwar Mahaifiyar Fatiman ce tace
“wannan kam son zuciya ne karara daga gani ai cusa mishi Amaryar aka yi don yadda take ta bore ya nuna komai, Allah sarki Fatima ciki na kusan biyar kenan shima be zauna ba sanadiyar wannan kadararren auren!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected