Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

***

Tun da ta bar garin Abuja yaji garin ya zamar mishi kaman Ƙango, baya jin daaɗin rayuwa, baya iya cikakken farin ciki, 24/7 da tunaninta yake kwana yake tashi, gabaɗaya Fatima ta kasa gane kanshi don ba wani abincin kirki yake ci ba, ko yaushe kuma yana ɗakin Fauza a kwance.

Shi karan kanshi be san Son ta yayi mishi mummunar illah ba seda suka nesanta da juna, ita yake so ta fahimci darajar shi hakan yasa ya ƙi kiranta ko da a waya ne ba tare da haƙarshi ta cimma ruwa ba sbd rana tsaka kawai ya cewa Fatima ta shirya su tafi yola su dan kwana biyu se su dawo gabaɗaya, ya azabtu kwarai da Tsananin kewan girkin ta, shayin ta, rashin kunyar ta in tayi niyya wadda babu abunda ke mai kyau daga gareta irin shi, shagwaɓarta, ƙamshin ta, shigar ta da ma lallausar fatanta… Daren karshe da suka yi spending gabaɗaya ya kasa fita daga kwakwalwarshi.

Ita Fatima ta zama abin kallo ne kawai illa iyaka abun ya ishe ta ta shige ɗaki ta sha kukanta, ta kira Aunty tana mata kuka akan yadda tunda Fauza ta bar gidan irin yadda suke dashi kaman an chanza shi, Auntyn ta tabbatar mata da ta kara hakuri na lokaci kaɗan ne komai ze sauya karta damu.

Hakan yasa ta cire damuwar a ranta kawai kuma wai ta shirya su je yola in zasu dawo su dawo tare gabaɗaya, me yake nufi?

Karfe 3 daidai na yamma jirgin su ya sauka a international Airport na Yola, Farhan da Faraj ne suka je suka ɗauko su, tun daga nesa kuma ya hangesu ita da Fa’iza a sadda suke tafiya.. Da idanu ya bi ta har motar su ta karya kwanan gidan nasu.

Hakan yasa be shiga ciki ba ya samu kan mota ya zauna jiran ta, yana so yaga expression ɗinta a sadda zata ganshi, yana so yaga tayi kewar shi ne kaman yadda yayi mahaukacin kewar ta? Yana so yaga idanuntan nan da yayi kewarsu fiye da komai, ganin sun ɗan jima yasa ya dira ya fita wajen gate a chan nesa ya hangesu da wani guy, be ma gane Zubair bane seda ya matsu dab dasu…

***

“Ashe Abun naki hauka ya koma ban sani ba Fauziyya?? Da Aurena a kanki kike kula wani gardi? Me wanchan Yaron yake dashi da ya fi ni Fauziyya??? Eyee?”
Ya daka mata tsawa yana kallon yadda take ta murza hannunta da ya rike hawaye na zuba a idanunta.

Fuskan nan a murtuke jajazir yace cikin dakakkiyar muryarshi da ya Haɗu da bacin rai..
“How could you? Oh da kin gayamin abunda kike buƙata da na banbance miki tsakanin Aya da tsakuwa… Da na nuna miki cewa wadda kika saba dashi fank…..”

“Don’t…!”
Itama tayi ihu cikin kuka tace
“Karka fara jefana da wannan kalma, karka bari na tsaneka ya Faizan..”
Kuka sossai take tana jin zafi sossai na yadda yake kokarin kawo abunda ba shine ba cikin rayuwar aurenta..

“Shut up!! Just shut the fucking up! Babu abunda zaki ce in yarda dashi.. Babu Fauziyya…”
Zata yi magana da niyyar kare kanta ya riƙo hannunta kawai ya cillata kan gadon ɗakin.

Yunkurin miƙewa take ya bita ya danne, a zafafe ya fara zare mata hijab yana faɗin maganganu da suka saka ta sakar mishi jiki ta Daena fighting kuma, tabbas zata ɗauki mummunan mataki kan wannan abu amma ba yanzu ba, se ya tabbatar ita ɗin ba shashasha bace, lusara, wacce bata san me take yi ba da zata rabe kanta a titi, se ya tabbatar ita ɗin daban take da sauran mata anan ne zata ɗauki matakin da ya dace da rayuwarsu..

A zafafe yake komai tun tana hawaye har ta soma kuka a hankali, daga karshe cikin kuka ta rike hannunshi tana bashi hakuri akan kar ya je mata a haka amma inaaa yayi nisa sossai, kan ta kara furta wani kalma ya haɗe bakinshi da nata yana bata wani irin zazzafar sumba, bakin da ya jima yana tsone mishi idanu…

Saida yayi matukar nisa a tirbar da ya ɗauka kan ya fahimci wani abu da ya so gigita rayuwarshi, saide ba ze iya dakatar da kanshi a wannan yanayi ba, ba ze iya katange kanshi daga gareta ba..

Ƙara me ƙarfi da ta kwala shi ya saka shi kankameta kaman zasu shige cikin juna a take dukkaninsu jikinsu ya ɗauki wani irin mugun rawa, daga ita har shi hawaye suke zubarwa… Ya je mata ne a yadda be yi zato ba se gashi ta shayar dashi ruwan mamaki da baya Tunanin har Abada ze kau daga idanu, zuciya da gangar jikinshi..

Bayan lokaci me tsawo ya mirgina gefe tare da janyo ta ya rungume da karfi kaman wani ze kwace ta
“I’m sorry..! I’m so sorry”
Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan hawaye na zuba a idanunshi..

Ita kam Sam bata san inda kanta yake ba, ba karamin wahala tasha ba, babu inda baya mata ciwo da radadi a jikinta, amma Dukda haka tayi juriya me yawa..

Sallah da yaji ake yi a masallaci na magrib ya sa ya zameta ta kwanta, bayi ya shiga ya watsa ruwa da wuri wuri, zuciyarshi cike da emotions da baze iya tantancewa ba, hawayen tausayi da kaunar ta kuwa sun kasa tsayawa a idanunshi, yarinyar nan ta sha wahala for nothing…. He never thought that. meyasa a sadda take kokarin kare kanta a sannan su kuma suka saka mata wani irin kyara da tsana?

Fita yayi yayi masallaci, duk sallar da yake ɗin ba cikakken natsuwa yake ba..
Ana idarwa ya mike ya fito se ga Farida da be san zuwanta gidan ba ta nufosu da gudu..

“Yaaaya Mammi… Mammi”
Da gudu shi da Farhan suka yi sashen Baba prof ma ya rufa musu baya da sauri ganin yadda duk faridar ta gigice.

Yanayin da suka samu mammi se ya ruɗa su, da sauri suka kama ta suka fito da nufin shiga mota a kaita asibiti… Daidai lokacin da wani irin hayaniya da basu taɓa riska ba a gidan ya ɓarke da buge buge kaman faɗa, ko kan ɗaya daga cikinsu yayi wani yunkuri Aunty da Ammi sun iso tsakiyar harabar gidan ana cin uwar sabada….

Faizan cigaba da kokarin saka mahaifiyarshi mota yayi don be da lokacin su se ta rike hannunshi tace a sanyaye..
“Ku fara sassauta wannan bala’i da ya taso kan mu tafi asibitin Faizan”

Gabaɗaya ilahirin ahalin gidan suna tsaye cirko cirko an rasa wadda ze raba se baba Alhj ne ya daka musu mummunan tsawa tare da rufe su da wani irin faɗa
“Me wannan? Me kuke yin nan a gaban ƴaƴa da jikoki? Wani irin bala’i ne wannan? Shamsiyya!! Ruqayya!!!”

Duk wannan be sa sun dakata ba, Ammi tace
“Na jima da sanin ke ɗin makirar ɓoye ce, Algunguma, munafuka ban tabbatar ba se yau…. Ashe ke ce kike ta kokarin kashe min yarinya? Ashe kece kike ta kokarin haukatata ta bi duniya to wallahi baki isa ba… Na fi karfinki saka idanunki cikin nawa ki gani da kyau”

Aunty ma shewa tayi
“Ahayye nanaye… Wai kura ashe ze ce da kare maye? Duma har yana da bakin raɗan maɗaci karki ɗauka ban san ke kike ɓarar da cikin Fatima ba sbd karta haihu da Faizan…. Karki ɗauka Cewar Ban san ke da Ƴar ki Fauziyya kune silar duk wani wahala da Uwar Faizan take ba…. Ko ba ke ce kika harbe mata kafa ba? Ko ba Fauziyya ke saka mata maganin da yake karya duk wani Magani da aka bata take sha ba…????”

Rassssssss haka gaban kowa ke wani irin dokawa suna kallon sabon abunda basu taɓa zato ko tsammani ba…
“WHAT…..!!!”

Faizan yayi exclaiming da karfi gabaɗaya alakanta komai da Fauziyya da aka yi shi ya gigitashi…

Waige Waige yake se chan ya hange ta tsaye tana kuka me taɓa zuciya, da sauri ya karasa gangar ta yace
“Wai da gaske? Da….gaske..ke ke kike sakawa mammi ma…ga…ni?”

Kai ta gyaɗa tana cewa
“Eh nice Amma……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected