Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

“Babe zan yi tafiya gobe it’s been a while da na ba aikina hankali hakan kuma yana so ya samar min matsala”
Ya karasa yana shafa gashin kanta.

Da sauri ta ɗago kai tana Kallonshi Rau rau tayi da idanu, ya san me take tunani ko bata furta ba, shafa kumatunta yake a hankali kan yace
“da haka kowacce mace ta saba, nan ɗin gidanki ne babu abunda ze kama ki kinji? Sannan u have to catch up with ur studies, zan samar miki driver kan na koya miki driving ɗin”

Ajiyar zuciya ta sauke tana me komawa ta kwantar da kanta, a hankali tace
“is it outside country?”

Yace
“yeah…”
Ganin zata sa mishi kuka ya saka shi kara bakinshi bisa kunnenta ya fara zuba mata kalamai da suka kusa sakata sakin murmushi ba tare da ta shiryawa hakan ba.

Da yamma likis suka fita tare yayi mata sayayya har da sabuwar waya ya saya mata me dankaren tsada tayi ta murna kuwa.

Washegari da sassafe ta tashi ta Haɗa mishi breakfast bayan ta gama taje ta watsa ruwa tana mamakin yadda be takura ta ba da ta tuna mishi da alkawarin da ya ɗauka na baze nemeta ba se in ita ta amince.

Sanye da doguwar riga orange nd black na kanti ta fito, tayi kyau sossai tana shirin knocking mai kofa ya fito sanye cikin uniform ɗinshi da yayi mugun amsarshi, kan ta motsa yayi hanzarin rungumarta yana me bata peck a kumatu yace
“Good morning my moonlight”

Tace
“morning yaya, breakfast ɗinka na dining”

Murmushi ya sakar mata yana rike hannunta suka nufi fita yace
“am already late dear, in na ce zan tsaya karyawa zan ɓata lokaci”

Hannunta ta zame tare da turbune fuska tana juya mishi baya.

“OMG baby ba dae kin yi fushi ba? Believe me zan karya a Airport I promise”

A hankali ta waigo ya kara tabbatar mata tace
“Toh ko tea bazaka sha ba?”

Yace
“uhm uhm ni me daaɗi nake so”

Dariya ta ɗan yi tace
“tea ɗin akwai me daaɗi akwai marar daaɗi ne?”

Kai ya gyaɗa mata yana murmushi

Tace
“Toh ai me daaɗin ne mu je kaji”

Matsota yayi ya manna ta da jikinshi tare da rankwafowa ya haɗe bakinsu saida yayi son ranshi kan ya ɗago yana murmushi yace
“this is sweeter, bye take care”

Yana kai nan ya juya da nufin tafiya, tayi saurin riƙe hannunshi a hankali tace
“bani minti biyu please”

Da sauri ta shiga kitchen ta Haɗa mishi abincin a box me kyau yana tsaye yana duba time ta fito, ita ta mishi rakiya har mota ta saka mishi abincin a gefen baya ta inda yake kan ta sakar mishi murmushi tana mishi Allah ya tsare, cike da farin ciki da ƙaunarta me tsanani ya tafi.

Kaman yadda ya faɗa karfe takwas se ga driver ta shirya ta wuce school sun haɗu da Afnan suka yi ta murnan ganin juna nan da nan ta hau ɗaura mata abunda ya wuce ta a makarantar.

Se yamma lis ta dawo gidan ta ɗan samarwa kanta abun ci kan ta watsa ruwa tana shirin sa kaya se taji wayanta na ringing, dubawa tayi se ta saki murmushi ganin shine ke kiranta, ɗagawa tayi nan fa suka fara hira, jin ta sake sossai ya saka shi ce mata ta kunna data.

Kunnawa tayi se ga video Call Sam ta mance ma towel ne jikinta tayi picking, daga chan ya kura mata idanu yana kallo she’s morethan beautiful ya ayyana hakan a ranshi.

“Ka ci abinci yaya?”
Ya karkata kai kaman ɗan yaro yace
“wa ze bani precious?”

Puppy face tayi tace
“Toh ka je ka saya mana yaya?”

Yace
“ni uhm uhm se an chanza min wannan sunan kan zan ci abinci yau”

Dariya sossai ta saki yana ta kallonta yana murmushi, tace
“tohm faɗamin wani suna kake so?”

Yace
“ko ma wani iri ni dae a chanza min yayan nan”

Tana dariyar abunda zata faɗa tace
“Toh Uncle? Ko mai gida?”

Dariya ya saki yana cewa
“kuttt lallai yarinyar nan Allah karki sake na kama ki, me wani uncle?”

Tace
“tohm am sorry mi carazon suna dae se ka gaji dasu in shaa Allah, now please go and eat”

Yace
“yes my queen, take care of yourself zamu yi magana anjima right?”

Kai ta gyaɗa, yana kallonta yace
“I love you…u are the story that I never want to end”

Tayi murmushi kawai tare da hanging up, ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi he hopes ta so shi watarana.

Haka rayuwa ta cigaba, don seda yayi kusan 2weeks be dawo Abuja ba, tana fama da karatu ita kuma a gefe ɗaya yana kasheta da soyayyarsa me tsayawa a rai, zasu yi voice call, su yi chat su yi video call duka, dukda har yanzu in ze mata kalamai na so da kauna ta kan yi murmushi ne kawai ba tare da ta bashi amsa ba amma in ta hira da shagwaɓa ne haka zata saki jiki tayi ta zuba mai, kusan duk abunda ya faru a rana haka da dare se ta bashi labari.

Shi kuwa ta bangarenshi ko da awa ɗaya baya iya yi idan har be ji daga gareta ba.

“Kin yi sallah? Kin ci abinci? Kar fa ki fita ba hijab, ya lectures kun gama? Ki tabbatar kin yi Adu’a kan ki yi bacci baby, Allah ya miki albarka”
Kusan sune kalamai mafi tsada a gareta wadda ba’a kai dare be yi mata waennan tambayoyi na kulawa ba, wani lokacin in tace suna da CA haka sede ta ga text ɗinshi

“kin yi karatu? Kiyi karatu bana so wanna CA ya wahalar min da ke”

Misalta irin yadda yake kula da ita Dukda distance dake tsakaninsu ɓata baki ne, ta gefe ɗaya matar Faisal ta haihu ya saka driver ya kaita suna da sha tara na arziki don seda ta biya shopping abunda yayi ta bata mamaki sadda ta dawo daga sunan kasa hakuri tayi ta koma ɗakin nashi inda ya ce ta ɗauki kuɗi ɗazu ta je shopping.

Wayan ta ɗauko tana Juyawa a hannunta wannan wayanta ne wadda ta taɓa bari a motarshi, to me yake yi dashi? Ta tambayi kanta Kunnawa tayi se taga akwai chaji alamu ana yawan yin chargynshi dubawa tayi babu sim, mayarwa tayi ta ajiye bayan ta kashe ta mike ta bar ɗakin, hirarrakin matan abokanshi ke dawo mata har ta isa ɗaki.

Dukda bata sa musu baki ba sede ta ɗauki abubuwa masu yawa ciki, wadda dole zata yi anfani da wasu, ita ɗin idan ta duba se taga kaman tana cikin masifa da tsinuwar mala’iku tunda dae gashi ta hanashi abunda ake kira da auren gabaɗaya sbd wani laifi da yayi mata da har ta mance ma, dukda ba haushinshi take ji ba tsoro take ji, tsoron abun ya riga ya mata tasiri, bayan haka shi matafiyi ne yana shiga wurare daban daban yana ganin mata kala kala in ya faɗa halaka sbd ita fa?

Tuna cabin crew na ranan tayi da irin shigar su se taji hankalinta ya tashi, yanzu fa da su yake yawo duk inda zashi, kuka ta fashe dashi tana jin zafin kishi na huda kirjinta.

Kaman kuwa yaji a jikinshi se ga video Call daga gareshi, ɗagawa tayi bayan ta share hawayenta.

Idanu ya zuba mata na seconds kan ya miƙe zaune yana jefar da pillown hannunshi yace
“what happened? Meyasa kika yi kuka?”

Kawai se ta sake sakar mishi kukan.
“OMG darling please! Menene? Me ya faru?”

Ganin tana shirin ɗaga mai hankali ne ya saka ta tsagaita kukan tace cikin wata kalar murya.
“I miss you please ka dawo haka..!”

Ajiyar zuciya ya sauke shima cikin kasalalliyar murya yace
“kukan duk na kewata ne pretty?”

Kai ta gyaɗa tana sake matso hawaye..
“Ya rabb! I wanna hug you so tide right now…but you are too far I also miss you so bad dear.. amma me aka tanadar min da ake so in dawo?”

Yayi maganan yana kwanciya kan pillow ta saki murmushi tace
“Duk abunda kake so”

Yana dage gira yace
“really? Duk abunda nake so? U promised? Zaki bani vitamin K, H da L?”

“Me kuma hakan mi carazon?(My heart in Spanish).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected