Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ash trouser ne a jikinshi me taushi se farar shirt wadda ya zauna mishi sossai ya fitar da siffanshi ta kakkarfan namiji, sajenshi ya kwanta lublub a kyakyawar farar fuskanshi ga fuskan cike da haiba Dukda ba murmushi yake ba amma be kama ba, taɓe baki tayi ta maida bisa hanya har suka karasa office ɗin.
Faisal ya fi Jafar wasa haka yayi ta jan ta yana tsokanarta ita kam kanta ƙasa murmushi kawai take tana kuma jin idanun gogan nata jikinta alamu ita yake kallo, wata yarinya Faisal ya kira a waya ba’a yi mintuna biyar ba se gata a ladabce ta gaishesu yana kallonta yace
“yauwa Afnan ga ƙawa nayi miki Dukda dae da hafsa ne kawancen asalin amma a nan kawar ki ce, ku je ki nuna mata wurare sannan Naga kuna da lectures 9-10 duk ku shiga tare kin ji?”
Tana murmushi tace
“Toh Yaya, Aunty mu je”
Murmushi Fauza tayi kan ta miƙe tsaye se ta kalli Faizan da nufin neman izinin tafiya, murmushi me kyau da ya tafi da imaninta ya sakar mata kan yace
“a kula, ina jiranki anan”
Kai ta gyaɗa itama ta ɗan yi mishi murmushi kan ta bi bayan Afnan dake Kallonsu da burgewa tana amsa bye bye ɗin husna.
“Kan uba! Kai fa ɗan iska ne Faizan so kake ka hana yarinya karatu da wannan narke narken?”
Harara ya zabga mishi yace
“ka manta ɗan guguwa ne..”
Dariya suka yi a tare, Faisal yace
“Masha Allah amma Amaryar ka na da hankali gata sweet sixteen shiyasa mana ka makale a gida ka kasa fita outside countries tunda aka kawo maka ita, Haba ai biri yayi kama da mutum”
Duka Faizan ya kai mai yana cewa
“ba da aljani ba?”
Dariya sossai faisal yake mai, daga karshe suka saki hiran Fauza suka kama wani, don sun san Faizan mutum ne da baya so ko a junansu ne suke kawo maganganun iyalansu in har ya zamana sirrinsu ne, ya sha gayamusu girman sirri dake tsakanin miji da mata da kuma tanadin Allah ga me fallasawa walau miji walau matar, lokutta dayawa in sun zauna daga sun fara in ya dakatar dasu zasu fara mishi tsiyar social ustaz ko young sheikh ya hana dole a hanu.
A ɓangaren Fauza kuwa taji daaɗin makarantar fiye da yadda ta zata, Afnan na da hankali ga saurin sabo nan da nan suka saba, a tare suka ɗan yiyyi signings da bata yi a course form ba suka kuma shiga lectures, basu dayawa don haka ba wani surutu kuma for the first time Fauza ta natsu a class har ta saurari malami ba zagi, faɗa ko neman tsokana.
Bayan sun tashi ta same shi a office ɗin kaman yadda ya faɗa suka nufi gida.
“Amm Faahim ya ƙira Visa ɗin husna ya fito zata bisu”
Da sauri ta kalleshi idanunta na cika da hawaye sede bata ce komai ba, ya fahimci kewan husna zata yi to amma ba yadda suka iya dole ne zata koma wurin iyayenta, har suka dawo gida jikin ta a mace, juicy pasta bolognaise tayi musu sharp sharp suka ci yayi daaɗi kuwa sossai, har ya kasa shiru yace
“Ni kam Fauza duk wa ya koya miki abubuwa masu daaɗi haka?”
Murmushi tayi zata yi magana husna ta ɗauki pillown kujera taje bayanshi tana kare mishi tace
“haka fa mommy ke yiwa Daddy idan yana cin abinci yana santi, wai kunnenshi na motsi…”
Duk dariya suka saka Fauza ta kasa tsayar da nata har ya shagala da kallonta for the first time he admits it she’s so cute and beautiful, da kyar ta tsagaita dariyar ganin irin kallon da yake mata tayi gyaran murya tare da cewa
“Na koya wasu wurin friends ɗina though idan na biya wurin koyan kullum se na sha duka amma haka nake zuwa bcs shine abinda ke sani farin ciki time ɗin, se kuma da nayi waya nayi classes masu yawa online”
Kallon tausayi ya mata yace
“then me yake hana ki faɗin ga inda kika je a time ɗin? Me yasa ba zaki ce a saka ki a catering school ba?”
Idanunta ta kaɗa wadda yaji har tsakiyar kwanyarshi tana ɗaga kafada tace
“Taurin kai irin na Fauza”
Kallonta kawai yake yana mamakin ita kuma wannan haka Allah ya yi ta ko kuwa? Tattare wurin da ta fara ne yasa ya ɗauke idanunshi kanta.
A haka suka kwashe kwana bakwai curr kullum ita zata yi musu breakfast ya sauke ta makaranta ya wuce inda zashi wani lokacin kuma ya tsaya wurin Faisal in an tashi ya maida ta ko karfe nawa zata kai baze ci abinci ba ze jira har ta gama su koma ta sama musu abunda zasu ci.
Be taɓa zaton rayuwa da ita in a shade ze zama haka ba, yarinyar tana da tsafta, kunya ga iya girki har ba’a magana, sau dayawa yana mamakin ina wannan kunyar nata yaje har take yawon hotels da shaye shaye, lokuta dayawa idan ya tuna hakan halin da rayuwarshi ke shiga baya mishi daaɗi hakan yasa yake ta kokarin rufe baabin ganinta da yayi a hotels da kuma irin shaye shaye da tayi.
Ranar Sunday bayan ya karya yake sanar mata ze je yola amma gobe da yamma ze dawo, kaman zata yi kuka haka tayi mishi Dukda tana tsoron kwana haka baya nan amma da sauƙi tunda ga husna, Seda ya tabbatar babu abunda suke bukata kan ya wuce bayan ya bata Wayanshi da take yawan anfani dashi ɗin nan.
***
“Na fahimce ki yanzu Fatima, an samu matsala ne girma da daraja irin na aure ya kunce ɗauri masu yawa akan Fauziyya ɗin hakan ne yasa kika ga halinta gabaɗaya kaman sake mata shi aka yi, sannan gidanta akwai kariya sossai amma jikinta da sauƙin kariyar, mijinki ze zo ku koma kawai ki zuba idanu kiyi kallo kaman yadda kika bar gidan haka itama zata bari ba na kwana bakwai ba ita kam na har Abada”
Aunty ta sauke Ayar cikin cin alwashi.
Murmushi Fatima ta saki tace
“yauwa Auntyna maganin kuka na”
Ko da ya iso se dare suka zauna da Baba Prof ya gayamusu duk abunda ya faru, kai tsaye Fatima ta Musa wadda ya saka baba prof kallonta cikin mamaki don tabbas ze iya cewa fauza bata yi karya ba kan yayi magana ma baba Alhj yace..
“Ko ni da ban shaku da fauza ba na san wannan ɗabi’ar tata na rashin ƙarya, ta kan faɗi gaskiya ko hakan ze ja mata dukan mutawa ne”.
Da sauri Fatima ta kalleshi har zata ce kenan ita ɗin an mata shedar karya kenan Aunty tayi saurin cewa
“ai duk maida magana bata taso ba, na yiwa Fatima faɗa sossai akan shiga harkar Fauza tunda an samu tana zaune lafiya karta dinga shiga harkar ta idan har ba mutunci ne ze Haɗa su ba, kuma in shaa Allahu ta ɗauka”
Baba prof yace
“masha Allah, to yayi”
Faɗa ya ɗan mata akan yadda Faizan ya mayar mai yadda take maida mishi magani ya nuna mata girman miji da matsayinshi kan ya sallame su akan gobe zasu wuce.
Faizan wurin mammi ya kusa cinye daren suna hira tsakanin uwa da ɗa, amma fa kusan duk hiran na Fauza ne ita ke mishi yana ji, ta bashi labarin yadda Fauza ke kula da ita da cimarta in bata da lafiya har ta faɗa mai Adu’ar da Fauzan ke mata in kafanta ya tashi yanzu bata nan ne sede tayi da kanta Dukda bata tausan kafan yadda ya kamata.
Tana bashi labarin tana kula dashi da a da ne da yanzu duk wani fara’arshi ya kau kilan ma da ya bar mata wurin amma yanzu har murmushi ya kan yi, se dare sossai ya miƙe yayi mata se da safe, har ranta ta ji daaɗin fahimtar da tayi akwai haske a lamarinsu.
Yana isa ɗaki a kan three seater ya kwanta ya fiddo ainihin Wayanshi ya fara neman layin shi dake wurin Fauza ɗin.
Har Seda ya kusa katsewa kan ta ɗaga
“Assalamu Alaikum warahmatullah”
Ta faɗa ƙasa ƙasa wadda a take muryar ya saukar mishi da kasala yaji gaɓoɓinshi a gajiye.
Shima chan kasa ya amsa ta kan ya ɗora da
“kin yi bacci ne?”