Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Kai tsaye tace
“ni kam ba zan yi ba”
Ta karashe da murguda baƙi idanunshi gabaɗaya ya waro yace
“ni kike yiwa rashin kunya da murgude murgude?”
Me makon yaji haushi ma dariya take bashi ala dole fushi take yi.

Tana kunkuni tace
“ni dae ba zan yi ba bana so ai tun farko ba’a nuna ana so ba se yanzu! Ni de babu wani girkin da zan karɓa”
Hannu ya kai ya dalli bakinta

“ni kike yiwa kunkuni?”
Haba ai se ta sakar mai kukan shagwaɓa har da bubbuga kafafu wai zafi…

“Yaa ilahil alameeen”
Ya furta akan lip ɗinshi kawai yana kallonta, yarinyar nan bazata kashe shi ba.

Ganin kaman yayi fushi yasa ta dangwalar da abincin tana tura baki ta zuba mai, ba tare da ya kalleta ba yace
“ɗauke kayan ki ba zan ci ba”

Da sauri ta fara kokarin ɗaukewa yayi hanzarin rike hannunta suka zubawa juna idanu….

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

26

“Wai da gaske ɗaukewar zaki yi?”
Ya faɗa a marairaice, se ta saki ta tsuguna ta zuba mai tare da miƙa mai.

Karɓa yayi yana cewa
“thank you”
Tana shirin magana Wayanshi ya ɗauki ringing, dubawa yayi se yaga Faisal suka gaisa yake tambayar shi me jiki, Seda ya kalleta kan ya amsa da da sauki, faɗa mishi yayi matansu zasu zo su duba ta.

“Zaki iya tarban baƙi kuwa?”
Ya faɗa bayan ya sauke wayan.

Kai ta gyaɗa tace
“Sossai ma, ni da nake so in ga mutane mutane su ganni..”

Yace
“families ɗin Faisal da Jafar ne wai zasu zo”

Tace
“Tohm Allah ya kawo su lafiya”

Ya amsa da ‘Ameen’

Bayan ya gama ci yaje ya shirya ya zo ya tambayeta ko akwai abunda zata buƙata ta amsa da babu kan ya duba Fatima ya faɗa mata tare da umarnin ta fito suyi aikin bibbiyu sbd sauƙaƙawa, ta dae amsa yana fita ta kwanta abin ta ta fara bacci.

Girki me rai da motsi Fauza tayi musu, dukda bata yi yayi yawa ba saide tayi varieties ta tsara shi kuwa yayi kyau sossai, ita da husna suka dinga jigilar kaiwa sama, bayan ta gama ta je tayi wanka.

Bata shafa mai ba se ta shafa magungunan nan da prof ghali ya bata ta shirya cikin lace riga da skirt ne da dinkin yayi matukar amsarta, ga colourn lace ɗin blue da onions se ya haske fatarta, ɗan kwalin irin hular nan ne so gyara parking ɗinta kawai tayi ta sanya ta nemi jewelries da suka yi matching ta saka.

Tana cikin shirya husna ya turo kofanta da sallama, ta amsa tare da ɗagowa.

Gabaɗaya idanunshi ya sake a kanta yana karewa halittar Allah kallo, tambayar kanshi ya fara wai me yake ji a kan yarinyar nan ne takamamme? Ko ta ina ta cike mishi zuciya da Tunaninta, idan ya fita yana marmarin ya dawo ya ga shigarta da kwalliyarta, hancinshi ya shaki sassanyar turarukanta masu saukar da natsuwa, bakinshi a ko yaushe yana marmarin tasting abincin ta…

“Yaaaya sannu da dawowa”
Abunda kenan ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi.

Kasa riƙe compliment ɗin yayi yace
“Masha Allah kin yi kyau”

Tana murmushi tace
“thank you”

Yana kallon husna yace
“Na gama shirye shiryen tafiyar husna fa jibi ne da misalin karfe 5 na yamma jirgin su ze tashi”

Da sauri ta kalleshi kaman zata yi kuka tace
“Wai dama da wuri ne?”

Kai ya gyaɗa yanayinta gabaɗaya se ya sauya, yace
“Ki bar musu nasu ke ki haifi naki tunda dae kayan aro baya rufa asiri”

Yi tayi kaman bata ji ba, se ma tace
“kaman sallama ko?”

Fita yayi ta bi bayanshi aiko iyalan abokanshin ne da su kansu kasancewar Saturday ne, Fauza kaman ta san su kuwa tayi musu tarba na mutunci bata bar matan anan ba ta ja su ɗakin ta bayan sun gaisa da mazan suka mata sannu da jiki.

Yaran Faisal biyu mace da namiji matarshi hafsat da ciki, se na Jafar uku matarshi firdausi tana goyon na huɗu.

Ruwa ta gabatar musu da fruits suka sake Gaisawa sossai hafsa ke gayamata yadda Afnan ke kai mata labarinta nan suka ɓarke da hira kaman sun jima da haɗuwa, mikewa tayi ta fita musamman ta je ɗakin Fatima ta shaida mata da zuwan baƙin amma bata ko tanka ta ba.

Su ɗin sun riga sun jima suna son zuwa gidan Faizan ɗin saide Allah be yi ba ko da suka ji ya ƙara aure ma su suna team uwargidaye ne abun mamaki se suka ga Amarya ke ta ina za’a saka ina za’a aje dasu.

Abincin ta gabatar musu bayan sun yi sallah suka ci suka yi nak suna cewa ita da bata da lafiya ta iya yin girki haka, tana ta murmushi kawai.

Yini sur suka yi amma Fatima bata leko ba se gab zasu tafi ta fito suka gaisa kawai ta koma, Hafsat da Firdausi wayayyun mata ne kuma sun fahimci kishi irin na Fatima a take suka dau yi mata lecture da yadda zata karkatar da hankalin miji kanta ita kaɗai, kaman yadda Burin kowacce macece ace ta zama tauraruwa a gidan mijinta kuma sarauniyar birnin zuciyarsa.

Ta Haɗa su da turarukan wuta kuwa ta zubawa yaran snacks masu yawa da Faizan ya saya musu suka yi ta murna, har mota suka raka su suka tafi.

Juyowa Faizan yayi yana kallonta fuskanshi cike da murmushi na burgewa da jinjina yace
“Allah ya miki albarka”

Murmushi tayi tace
“Ameen”

A tare suka koma be zauna ba shi ya taya ta suka tattare gidan tsab, tana tsaye kitchen tana shirin wanke wanke kenan taji kamshinsa ya bule kitchen ɗin waigawa tayi se ta ganshi tsaye sanye da red riga marar hannu ta shan iska da ya bayyana damatsanshi da suke a murɗe se three quarter milk, hannayenshi zube a aljihun yana kallonta.

Maida kanta kawai tayi ga dauraye kwanukan kan ta zuba ruwan sabulu se ta nufi drawer don ɗauko lemon fresh da ta ɗaura shi chan sama sbd husna dake yawan son wasa dashi.

Hannunta ta miƙar har tana ɗagel don ɗauko wa kawai taji hannun mutum bisa nata, da sauri ta waigo se fuskanta ya kusan dukan kirjinshi sbd kusantota da yayi sossai, idanu suka zubawa juna na seconds kan yayi gyaran murya yana cewa
“Amm jikinki ba wani matsala ba?”

Fuskanshi na kusan kan nata sbd tsawo sossai da ya fita hakan ya sa ta kasa magana se da ya ɗan matsa baya kan ta saukar da kanta ƙasa tace
“Ai na warke”

Wani dogon tsaki da suka ji yasa duk suka kalli kofa, Fatima ce tsaye tana Kallonsu hawaye ne ke zuba a idanunta ta fara cewa
“Wallahi Allah se ya saka min, Allah baze taɓa barinki ba Fauziyya kaman yadda kika yi min kema Allah ya miki, kin zo kin sameni gidana ina zaune lafiya da mijina kika shiga tsakaninmu kika juye hankalinshi gabaɗaya to Wallahi ban yafe miki ba”

“Kai kuma” ta nuna shi.

“Allah kaima se ya bi min hakki na, watana biyar a gidanka ka kara aure, a wata biyar da nayi ban taɓa yin sati ɗaya cikakke da kai ba kana chan gobe kana nan amma tun zuwan Fauziyya gidan nan baka taɓa fita daga Kasar nan ba, kai ka ce min baka iya komai a harkar kitchen ba, zan iya rantsuwa baka taɓa shiga kitchen da sunan aiki ba amma yau gashi nan kana taya ta… A haka kake cewa kana min adalci Toh wlh ban yafe ba idan ina da hakki Allah ya bi min…”

Yadda take kuka duk suka tsaya suna kallo, kan Fauza ta taɓe baki ta nufi gaban kayan wanke wankenta ta fara wankewa, shi kuwa a natse ya isa gabanta ya sa hannu ya riƙe nata ya fusge ta suka fice be tsaya ko ina ba se Ɗakinta ya daka mata tsawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected