Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Da sauri tayi kasa tana gaisheshi ya amsa cike da kulawa ta wuce, yayinda Fauza ta nufi wucewa ba tare da ta ce mishi komai ba, cikin zafin nama ya miƙe ya taka biyu ya cabke hannunta, juyowa tayi se idanunsu suka sarƙe.. Kallonta yake da gabaɗaya idanunshi, a hankali cikin kasa sossai da murya yace
“Fauziyya ni kike yiwa rashin kunya yanzu?”
Kau da kai tayi tace
“me nayi kuma?”
Yace
“yanzu kin ga ya dace ki wuce ni ba tare da kin gaisheni ba?”
Ba tare da ta kalleshi ba tace
“Good evening..!”
Ta zare hannunta zata wuce ya sake janyo ta,
“Fine and why are you avoiding me?”
Ya faɗa yana riƙe da kafadar ta.
Kanshi ta maida idanunta tace
“Gaskiya kake son sani? Toh ina kaucewa ganinka ne sbd bana so idanunka su cigaba da kallon wannan mashayiyar kuma mazinaciyar fuskar t….”
Bakinta da ya buge ne ya saka ta maida kanta ƙasa hawaye ya fara zuba a fuskanta..
“Baki da hankali ne kike danganta kanki da waennan kalamai?”
“Au wai har ka manta? Ba ni ce na dangata kaina da hakan ba Kaine ka jefe ni da waennan kalamai, akwai saura ma ai cewa kayi bazaka iya cigaba da zama da me bin maza ba…. Nima kuma ba zan iya cigaba da zama da me saurin fushi da zargi ba don haka kaman yadda na yiwa su Baba biyayya a auren nan yanzu ya zama wajibi a dubi lamura na a raba wannan aure Ka sake n….”
Rufff ya rufe bakinta da nashi tare da matsota gabaɗaya ta shige cikin kirjinshi, baze iya cigaba da ɗaukan kalaman ta ba, tayi babban zunubi da kunnuwanshi bazasu juri ji ba bare har ya wassafa aiwatuwarshi..
Takarkarewa tayi ta ture shi da iya karfin ta, jikinshi a mace yake don haka kujera kawai ya zube yana dafe goshi a hankali har muryarshi na cracking yace
“Am so sorry… Pls karki sake faɗar irin wanchan Kalmar yayi min girma zuciyata bazata iya daukarta ba..”
Kuka ta fashe dashi kawai ta juya da gudu tayi ɗakinta, a gado ta zube ta sha kukanta ta more kan ta miƙe ta faɗa toilet tayi wanka ta san kilan ya zuwa yanzu fa’iza ta gaji da jiran ta a ɗakin Jaddah ta wuce…
Fita tayi ga mamakin ta har lokacin yana kwance cikin kujeran parlorn idanunshi a lumshe hannunshi kwance bisa kirjinshi, daga yadda yake karkada kafa zaka san ba bacci yake ba.
Idanun da suka yi laushi ya buɗe ya kure ta da kallo, baki ta taɓe ta wuce ta fice daga sashen gabaɗaya.
Bayan isha tana kwance kan cinyar Amminta dake taje mata kai a hankali Falaq tace
“ji wani sabon iyayi yanzu Fauxa Ammin ce zata miki taza?”
Bakinta ta murguda tace
“Ina ruwan wani? Amminki ko Ammina?”
Tahowa tayi da nufin gwabe mata baki Ammi tayi saurin riƙe hannunta
“Ke Falaq Rabu min da yarinya akan me zaki daketa bayan kece kika fara tsokananta?”
“Laaa Ammi yau bayan Fauzar kike bi? Lallai ma Ammi”
Ammi tace
“eh na bi ɗin”
Ficewa tayi fuu sbd yadda Fauxa ke mata dariya Ammi na murmushi tace
“Auta tashi mu yi magana”
Mikewa zaune tayi tana fuskantar Ammin tace
“Toh Ammina”
“Kowa a gidan nan ya fahimci tsakaninku da Faizan babu daaɗi har ma mahaifinki ya so ajiye ki se kuma baba prof ya hana, nima shawara zan baki a matsayina na mahaifiyarki, ko menene Faizan ya miki kiyi hakuri ki bishi ku koma yana da aiki amma yake ta faking excuses duk sbd ke, ya samu baba prof akan a bashi ke ku koma baba prof kuma ya ce in har ba ke kika shirya komawa ba babu ruwanshi, kin ga dae irin karamci da soyayyar da iyayenshi ke miki ko don wannan zaki duba mafi soyuwar ɗan su ki kyautata mishi sbd su ma su ji daaɗi…”
Fuskanta tayi kicin kicin dashi har hawaye na shirin zuba tace
“Ammi fa zar…”
Ɗaga mata hannu Ammi tayi tace
“bana son jin komai in dae har don abunda ya Haɗa ku ne, shawara ce kawai na baki kiyi tunani”
“ni dae Ammi ba zan iya komawa ba, baya sona nima haka kuma yanzu duk abunda ke boye ya riga ya bayyana kowa ya kama gabanshi kawai..”
Kallonta kawai Ammi ke yi, zata yi magana kenan suka ji an shigo da sallama…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
33
“Sannu da dawowa baba”
Fauza ta faɗa tana ɗaukan dankwalin dogon Rigan jikinta tana ɗaurawa a kanta, Ammi ma sannu da zuwa ta mishi ta mike don kawo mishi ruwa, Fauza bata motsa ba don ta san ko ta tashi Ammi cewa zatayi ta dawo ta zauna kar ta hanata samun ladarta.
Gaisawa suka yi da baban Dukda sun gaisa da safe shima cikin hikima yayi mata hannunka me sanda Dukda be fito kai tsaye yace maganansu da Faizan bane sede ya nuna mata rama Alkhairi da Alkhairi abu ne me kyau, kuma Hausawa sun ce ka gaida me gaisheka ko da kuwa baze amsa ba, shigowar Ammi ne ya katse su.
Abinci da ruwa ta kawo mishi, Fauza ce ta zuba mai yace ta matso su ci rana na farko kenan tun wayaunta ta sanya hannu suka ci abinci kwano ɗaya da mahaifinta Ammi na zaune daga gefe suna hira jefi jefi ranar har kuka tayi, Aunty ba karamin cutar ta tayi ba ta hana mata wananan shakuwa da soyayyar na tsakanin iyaye da ‘ya’yayensu, se da taji bacci kan ta sallamesu bayan tayi waya da husna a wayan Ammi tana ta shagwaɓa akan ita kam zata dawo gidan Fauza, da wayan ta fita parlor ta Haɗa conference da Ya fadeela take ba su labarin abunda ya faru.
Sbd duk bata yi natsuwar magana da yayyun nata ba se yanzu, duk seda suka zub da hawayen jimami, suka yi mata barka sannan suma duk sun roketa ta koma gidan Faizan Dukda sun fahimci haushin abunda ya mata har lokacin yana ranta sede ta ƙi nunawa ne kawai har fadyaa ke rantsuwar ita tun randa suka je gidan ma ita da Ya Faahim seda suka yi gulmar soyayyar da suke yiwa juna a ɓoye.
Ita dae fadeela se dariya take yayinda Fauza ta shagwabe akan lallai lallai ita ba haka bane tana Haɗa ya Fadyaa da Ya fadeelah, sun sha hira kan suka yi sallama don ma what’sapp call ne da ta tabbatar ko biyar baze saura a wayan Ammin ba.
Anan kan stand ta bar mata ta wuce sashen Jaddah, kan ta shige ta hangi fitowanshi daga mota yana waya a natse yake tafiya yayi sashensu na ƴan maza, ta jima tsaye tana Kallonshi seda ya wuce kan ta juya itama ta shiga sashen, ɗakin Jaddah ta shiga suka ɗan yi hira kan taje ta kwanta bayan ta rufe kofan ta.
Washegari da safe ko karyawa bata yi ba ta dae yi wanka ta sanya wani cotton blue shiffon shirt da straight skirt baƙi se ta ɗaura black dan kwali a kanta, se kamshin khumras na sabon gyaran da Jaddah ke mata take zubawa, fitowa tayi ta shiga kitchen ta samu zaliha na yin kosai da koko, baki ta taɓe ta warware gyalen da ta ɗaura a kanta se ta yafa ta fice daga sashen.
Har ta nufi sashensu se ta juya ta nufi na mammi don tun shekaranjiya rabon da su haɗu ta aiko mata da kifi dafaffe ma da rana bata je godiya ba kuma kila abunda ta dafa se ya fi na jaddar nan daaɗi.
Da sallama ta shiga parlorn, Mammi na zaune tana karyawa itama maraba tayi mata fuskanta cike da fara’ar ganin surukar tata, zama tayi suka gaisa sossai kan mammi ta mata umarni ta isa akwai abincin a dining ta ci abin ta.
Tsam ta mike tayi dining ɗin ta diba kuwa me ɗan yawa ta fara ci a hankali.