Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ɗakin Jaddar ta wuce ta ɗauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faɗa Adu’a da lallashi Fauza ke bukata ba faɗa da duka ba.
Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah).
Direct ɗakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key ɗin, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a ɗakin Sam babu tarkace kaman ba ɗakin namiji ba.
Gado ne a ɗakin saɓanin sauran ɗakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai ɗan corridor inda drawer ɗinshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe ɗinshi tare da ɗaukan tsintsiya ta fara aikin ɗakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan.
Tsab ta share ɗakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror ɗinshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take ɗakin ya ɗau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab ɗinta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita.
Tana sanyo kai ɗakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faɗawa, wani irin disgusting look na me kike min a ɗaki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta.
Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta ɗau hijab ɗinta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape ɗinta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa.
Kai tsaye yace
“Ke!”
Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi.
“Ke! Sa gwiwowinki a ƙasa”
Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace
“Amma me na y….”
Ɓas haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace
“kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?”
Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama ɓaci wani tsanar shi na sake mamayarta.
Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts ɗinshi kawai yake son yi..
“Me ya kaiki Abuja?”..
Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, hannayenta suka soma rawa, bata ɗago ba don tana ɗagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta.
“Don’t let me repeat myself… Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?”
Gabaɗaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire
“A…abu…ja kuma?”
Be yi magana ba, tace da sauri
“ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba”
Duk yadda ya so ya firgita ta ta faɗi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba.
Tsaki me karfi ya ja yace
“get out of my sight”
Da sauri ta miƙe tayi kofa ya sake cewa.
“Ke!”
Chak ta tsaya, yace
“this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a ɗakina bana son harka da kazamai kin gane ko?”
Kai ta gyaɗa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata.
Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali.
Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja? Allah ka rufa min asiri.
Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace
“Fauziyya”
Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious.
“Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saɓawa iyaye kaman saɓawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saɓa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saɓa musu alhali ban koyar dake ba?”
Raurau tayi da idanu tace
“me nayi kuma Jaddah?”
“Meyasa zaki yi tafiya baki sanar da mahaifin ki ba? Ba wannan ba meyasa tunda kika dawo nan baki je kin gaida shi ko sau ɗaya ba? Kina son ganin haske a rayuwarki? Ya kamata ace kiyi nadama ki shiga alhini akan korar da yayi miki a sashenshi amma Fauziyya duk babu? Ko don kinga kina dani? Har fa rashin lafiya mahaifin ki yayi cikin wata biyar din nan ashe baki je kin gaishe shi ba?”
Bakinta kaman ze taɓa gini tace
“amma Jaddah kina ji yace ko ganina baya son yi, taya zan kai mishi fuskar da baya son gani da sunan gaisuwa?”
“Fauziyya!”
Jaddah ta kirata ranta na ɓaci.
Hawaye saura kiris ya zuba mata, dama bata dawo ba da wannan damuwar da ta dawo ta riska kuma.
“Naji jadda zan gyara yanzu kullum da safe kan in tafi makaranta zan je in gaishe shi ba shikenan ba? Kin turani ɗakin wanchan ya wulakanta ni kin huta!”
Tana kai nan ta tashi ta wuce fuuuu, girgiza kai Jaddah tayi tana furta
“Allah ya shirya Fauziyya”
Ita kuwa tana shiga ta rufe ɗakin tare da yin wurin pillow ta dauki wayanta ta kira Zubair, shagwabewa tayi tana faɗa mishi abunda Faizan yayi mata.
Lallashinta yayi tayi, dukda duk sun sha mamakin yadda aka yi ya ganta, tace ita bazata kara tafiya wani garin ba kuma amma shi Zubair ya tabbatar mata akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ba me ganinta.
Satin Faizan biyu aka sanya bukin su da Fatima nan da wata biyu, sbd har sun fara waec.
A take duk bangarori aka fara shiri, ita dae Fauza kaman bata san ana yi ba harkokinta kawai take, ko da Fa’iza ta zo mata da maganan anko ma kai tsaye tace bazata yi ba, su karata chan daga Amaryar har Angon babu abunda ya Haɗata dasu..
Jadda ce ta bada kuɗin nata, Zubair ne yake shirin zuwa Dukda ta ƙi ya ki, wai yayi missing ɗinta Dukda sukan yi waya, su yi video call duka.
Gabaɗaya ya lalatata da soyayyarsa, a gefe ɗaya babu abunda ya sauya daga abubuwan da take yi sai giyar da bata sake sha ba tun daga ranar da abunnan ya faru.
Babanta kuwa ta kan je kullum ta gaida shi, iyaka abunda ke hadasu kenan, wurin mammi ne take girke girkenta hakan ya sa mammi fahimtar abubuwa dayawa daga gareta, har yau bata manta wayar da suka yi da Faizan ba, hakan yasa lokuta dayawa ta kan ja ta da nasihu kala daban daban wadda ya kan kashe mata jiki amma daga ta bar sashen shikenan.
Faizan ya koma bakin aikinshi inda ya Haɗa Fadila da haɗe haɗen kayan aure, dukda ta ce bazata samu zuwa ba sede zata turo ta jirgi se ya karɓa.
Wasa wasa buki ya ƙarato, Amarya da mahaifiyarta ana ta shiri, mutanen Maiduguri sun cika gidan kai ka ce bukin farko kenan a zuri’ar, ba karamin takura Fauza suka yi ba Dukda ta tsaya kai da fata tace babu me saukar mata a ɗaki bukin munafuka da azzalumi, hakan ko aka yi sbd gudun jarabar ta babu wadda ya sauka a ɗakin nata.
Walima, saukar Qur’ani se reception wadda maza ne kawai zasu yi bayan ɗaurin aure aka shirya kaman yadda ake kowani buki a gidan.
Zaune take kan dressing mirror hannunta riƙe da waya tace
“ka fa san irin gidan da na fito Zubair, yanzu in bar gidan nan in same ka hotel kana Tunanin babu wadda ze fahimta?”