Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Shi kuwa idanunshi da suka rine gabaɗaya suka sauya ya ɗaga ya zubawa Fauza ko kallon wurinsu bata yi ba, tana dae kwance a kan kafadan Jaddah hannunta na riƙe da nata har lokacin kuma hawaye kan zuba a idanunta ta sa hannu ta goge….

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

31

Tsatsareta yayi da idanunsan nan masu kaifi yana so yaga yanayinta da maganan Fatiman saide ko inda suke bata kalla ba bare ta bashi damar karantar ta, maida idanun yayi kan Fatima yana me kallonta cikin kyamata da tsana yace
“kiyi haƙuri ba zan iya cigaba da zama dake ba, I never loved you. Sannan ko ba don haka ba, ba zan taɓa Haɗa wata macen da Fauza ba she had enough in her life so maganar baƙar kishiya babu shi har Abada, na sawwake miki igiyoyi biyu bisa uku dake kanki”

Ihun kuka take kurmawa tana rokon su baba da su sa baki, babu wadda ya motsa sbd babu wadda ya taɓa kawo Fatima zata iya aikatawa Fauza abunda ta aikata, zama da munafuki me fuska biyu ba karamin hatsari bane don babu abunda bazata iya aikatawa ba.

“Shamsiyya na sake ki saki biyu, ki je ke da Allah zaki girbi duk wani abunda kika shuka, sannan na baki nan da awanni 24 ki gama duk wata ganawar da zaki yi da yaranki ki tattare duk abunda kike buƙata ki bar min gida har abada kuma bana so in sake ganin kafafunki cikinshi”
Ita kam bata yi kuka ba, se wani murmushi da take yi, lallai duk wani ƙarya tata ta ƙare saide bata karaya ba, a ganinta don ka yi farautar Burin rayuwarka ba wani abu bane, mikewa kawai tayi da nufin ɗaga kafa tayi tafiya se kafa yace be san zance ba, ihu ta kurma jin wani azababben ciwon ya tsarga mata a gabaɗaya kafofin nata, “Kaikayi koma kan mashekiya” ta furta tana kallon Mammi da wani irin hanzari.

Se yanzu ta tuna boka ya ce mata duk ranar da aka san itace da hannu kan ciwon na mammi tsab ze dawo mata, se lokacin ta fara kuka jin yadda kasusuwanta ke tauna, haka wai dama Aishar ke ji? Ta tambayi kanta tana kara kure mammi da itama take kallonta da mixed emotions da kallo.

Fatima take kira ta taimaka mata su fice, Fatima na kuka kaman ranta ze fita ta kamata suka fita ba wai don wani abu ba se dae tana Tunanin kila mahaifiyartata ta sama musu mafita don ta saba sama mata mafita, ita wlh bazata taɓa iya hakura da Faizan ba.

Yunkurawa Fauza tayi da niyar miƙewa sbd Baba prof ya sallamesu bayan nasiha da yayi musu me ratsa jiki, duk sauran matan jikinsu yayi matukar sanyi, ganin kowa na shirin fita ne yasa itama ta yunkura saide bata kai ga miƙewa ba ta koma ta zauna tana runtse idanunta da suka kankance don azabar zafin da ya ratsa ta.

Tsab yana hankalce da ita, wani irin tausayinta ne ya tsirga mishi, abunda ta guda kenan amma ta lura kusan kowa ya harbo jirgin duk kunyar Faizan be ji ko dar ba se ma murmushi da ya ɗan saki yana jin daaɗin yadda kowa ya kamata ya san Fauza ɗin ba ƴar iska bace kaman yadda aka mata tambari.

Ammi bata kula ta ba sbd ta san zata samu duk kular da ya dace a wurin Jaddah ko mammi, yayinda ita kuwa ta ma kasa hada idanunta da mammin kwata kwata.

Ji yake kaman yaje ya ɗauke ta chadak ya kaita har sashen na Jaddah, ya san tana wahalar tafiyan ba laifi ta wahala sossai, hannunshi ya cusa cikin kwwantanccen gashin kashi ya shafa yana sakin murmushi sanin se sun kwashi daru da ita alamar ta ya nuna ba karamin fushi take dashi ba.

Ruwan zafi sossai da wasu magunguna Jaddah ta Haɗa mata akan ta shiga ta zauna, idan ya huce ta sake saka wani tayi kaman sau uku kan tayi wanka ta fito, duk yadda ta so shigar kasawa tayi tana kuka tana yarfa hannu, Seda Jaddah ta tsaya a kanta sossai kan ta iya shiga duk yadda Jaddah ta so ta dubata ko taji ciwo kiyawa tayi, haka aka yi wankan amma ta sha wahala kuma ita kam bata ji sauƙi ba, banda Allah ya saka mata babu abunda take kira.

Bayan tayi wankan ta sha magani tare da rama sallolin da ake binta ta kwanta saide fa zazzaɓi me zafi ya rufeta har tana fita hayyacinta ba arziki Jaddah ta kira Faizan da shima ya sake wanka kenan bini bini se ya saki murmushi ya ɗan cije leɓe, ganin kiran Jaddah yasa da hanzari ya zura jallabiya me taushi Ash ya fice.

A hannu ya ɗauko ta Jaddah na gaba ta buɗe mishi motar ya sanyata tana ta mishi faɗa, shi dae be ce komai ba ya zagaye ya shiga ya ja da gudu se asibiti, likita namiji suka samu kai tsaye yace a nemo mace don matsalar ba na namiji bane kuma baze iya hakura wani ya duba mishi mata ba.

Haka ko aka nemo Dr mace, ko da ta duba ta taji ciwo kuma wurin yayi tsami dole tana bukatar ɗinki, haka ko aka yi tana kuka don ta sha baƙar wahala, bayan an gama aka sake mata allurai sbd zazzaɓin tuni wahalallen bacci ya ɗauke ta.

Zuwa suka yi suka duba Fa’iza da har lokacin itama bata farfado ba, dama Jaddah ta tura musu zaliha ta taya su kwana, se kuma ga Fauza ma.

Jaddah ce ta kwana da fauzar yayinda mazan suka wuce gida.

Da misalin karfe goma na safiyar washegari ya fito a shirye tsab cikin wata farar ƴar uban sun yadi da aka yiwa ɗinkin zamani kwata kwata da kaɗan ya sauka cinyar shi, fuskanshin nan cike da haiba da wani irin annuri Dukda ba sake take ba, ya saka wata takalmin fata me surkin ja da brown se ya ɗaura jar jaddara a kanshi, sajenshi nan a gyare lub lub haka gashin kanshi dake sheki, agogonshi Iwatch ne wadda kallo ɗaya zaka mata ka san diamond ce sbd walwalinta, hannunshi cushe a aljihu ya nufi sashin mahaifiyar tashi yana taku cikin salon tafiyarsa na ingarman namiji me cike da kwalisa.

Har cikin ɗakinta ya sameta ya ɗan rungumeta ganinta tsaye tana gyara kan dressing mirror ɗin ta, a hankali yace
“Alhamdulillah Mammi lafiya ta samu Allah shine abin godiya”

Tace
“kwarai kuwa Son, ji nake kaman ban taɓa wani ciwo ba”

Yace
“Good morning mom”

Ta amsa cikin kulawa, sannan ta ɗaura da
“akwai abinci basket biyu a kitchen ka fita dashi ina zuwa mu wuce asibitin”

Fita yayi yana murmushi ya zaku iya zakuwa wurin son ganin kyakyawar fuskar ta da idanuntan nan masu kyau da ɗauke hankali.

A mota ya saka baskets ɗin yana tsaye yana jiran mammi se kuwa gata, daga nesa yake ayyana kyaun mahaifiyarshi da iya shigar ta Dukda hijab ne jikinta amma kallo ɗaya zaka mata ka san wannan ɗin ƴar gayu da ado ce, zobunan gwal guda biyu se walwali suke a hannunta na hagu, na damar na riƙe da jaka.

Da kanshi ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya zagaye ya shiga ya ja suka fice, tun asuba iyayensu mazan suka je asibitin suka dawo, da kyar baba prof ya lallaɓa fa’iza ta bar kuka me cin rai da take, ya mata nasihu sossai haka babanta, Fauza kam da kyar ta iya gaida su kunya kaman ta tsaga ƙasa ta shige.

Sun so su dawo tare da Jaddah tace bata san zance ba se Mammi ta zo Farhan da yake ta zirga zirgan asibitin se ya maida ta.

Da sallama suka shiga ɗakin tana kwance ne idanunta kuma biyu ba bacci take ba, har zata amsa sallamar mammin kamshin turaren shi ya cika ɗakin wadda ya tabbatar mata da tare suke da mammin hakan yasa tayi saurin rufe idanun..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected