Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Mu je kayi wanka bari na samo maka abunda zaka ci”
Tana shirin wucewa ya dawo da ita jikinshi yace
“ke kin ƙoshi?”
Kai ta gyaɗa yace
“fine”
Yana faɗar haka ya ɗauke ta chadak se ɗakinshi, tana ta zillewa haka ya ribaceta duk da irin tsoratar da tayi ya lallaɓata kuma ya bita a hankali ya cika ta da soyayyarsa me tsayawa a rai, tayi ta mishi raki da shagwaɓa… Wannan dare na daga cikin daren da bazasu taɓa mancewa dashi ba.
Sossai ya buɗe musu wani sabon baabin soyayya, har mancewa da karatu take bare ma da ya ɗan kwana biyu be sake tafiya ba, komai da komai tare suke yi, da yamma su fita koyon tuƙi ana yi ana shan love, a cikin kwanakin duk wadda ze gansu se sun bashi sha’awa, kana ganinsu zaka san akwai tsananin soyayya da shakuwa tsakaninsu.
Kwance take kan doguwar kujera a parlorn tana kallon wani series film yayi sallama ya shigo, da sauri ta miƙe ta tare shi suka rungume juna ya bata peck a kumatu tace
“sannu da dawowa Noor”
Yace
“yauwa my queen, je bedside ki ɗauko min 50k zan sallami driver ɗin nan tunda my queen hannu ya faɗa”
Tayi murmushi tare da Juyawa ta nufi ɗakinshi ta buɗe se ta sake cin karo da wayanta, a hannu ta ɗauko bayan ta ɗauko kuɗin Dukda ya ga wayan sede be ce komai ba ya karɓi kudin ya sauka.
Bayan ya dawo ya zauna ta kawo mishi ruwa da lemu ya sha, ta dubi wayan tace
“Yaaya a bedside ɗinka na ga wayan nan”
Yana kallonta yace
“uhmm”
Se ta rasa me zata ce, kawai se ta mike don mayarwa yayi hanzarin riƙo ta yace
“you wanna know me nake yi dashi ko?”
Kai ta gyaɗa tana Kallonshi ya janyo ta ta zauna gefen shi yace
“bude ki shiga gallery”
Ta buɗe tayi yadda yace
Hotunan ta ne masu yawa ciki kasancewar ta me yawan son ɗaukan pics, ta kalleshi ya ɗaga mata gira yace
“su nake kallo a ko da yaushe, ban san taya ba ban san yaushe ba na dae tsinci kaina tsundum cikin ƙaunarki wadda a ko yaushe bani da wani aiki se na kallon hotunanki, na kan yi chargyn wayan musamman don in kallesu, kusan babu wadda ban haddace kalar kayan, tsayuwar da kuma yanayin hoton ba… Believe me I loved you tun kan na san menene so”
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke idanunta cike da hawaye ta rungumeshi tace
“our lives are one even though we are in two different bodies, I love you too”
Shima sake shigar da ita jikinshi yayi a hankali tace
“sweetheart! Meyasa Zubair yace ka mishi mugunta?”
Da sauri ya ɗago ta, tayi hanzarin Kallonshi gabanta na faɗuwa kar fa ya ɗauka da wata manufa ta mishi wannan tambayar..
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
ƘARSHE
“why do you care to know?”
Ya tambaya fuskanshi ba cikakken fara’a.
Mikewa tayi tace
“am sorry”
Ɗakinshi ta shiga ta Haɗa mishi ruwan wanka ta fito tace
“ruwan wankan ka is ready”
Mikewa yayi ya wuce ta ba tare da yace komai ba ya shiga toilet ɗin yayi wanka, ko da ya fito akwai kayanshi marasa nauyi da ta fesa wa turare ta ajiye bisa gadon, dauka yayi ya saka bayan ya shafe jikinshi da mai da turarukan shi, fitowa yayi ya tsaya yana kallonta tana karasa gyara dining ɗin.
Takawa yayi ya rungumeta ta baya a kunnenta ya raɗa mata
“I just hate him tun daga sadda na ganki dashi a Abuja, wanchan ganin ya hana mini natsatsen bacci ba tare da na san dalili ba, a sadda na sake ganinku a hotel na ja mishi federal warning amma be daddara ba wai shine har da raba ki da school kina neco at that time ya zo min iya wuya, kuma na san shi dama farin sani sbd miyagun kwayoyi da yake yawan yawo dasu akan kama shi sau da dama a Airport kwana biyu a sake shi, so bayan ya dawo ya tafi Russia, that time nima Ina chan kuma ni zan tuƙo jirgin da ze dawo daga chan zuwa Nijeriya, I clearly saw him with the drugs again.. I then reported him Dukda na so hukunci me tsanani ya hau kanshi sede sun yi anfani da hanya da kuma kuɗi wurin kubutar dashi Dukda ko da ya dawo already you are mine, shiyasa ban kara bi ta kanshi ba”
Kai ta gyaɗa tace
“ga abinci”
Bata so Sam ta nuna interest ɗinta kan labarin kar ya ɗauka da wata manufa sanin yadda yake da zafin kishi a kanta, a tare suke cin abincin cikin plate guda, bayan sun gama ta tattare kwanukan.
“Are you OK”
Ya tambaya yana janyo ta jikinshi.
Kai ta gyaɗa tana ɗan murmushi yace
“menene?”
Ta girgiza kai, da yayi insisting se tace
Kawo kunnenka kaji yana mika mata ta d’an cije shi kad’an tare da Mikewa ta kwasa da gudu da gudu ya bi ta yana kokarin kamata tana zillewa.
Haka suka ta zagaye tana ta mishi dariya da gwalo daga karshe yayi nasarar kamata suka zube kan kujera yana mata jakulkuli da tambayar wa ya kama tana dariya sossai har da hawaye.
Bayan kwana biyu..
Karfe shidda ta fito lectures ta nufi motarshi ta shiga tana cewa
“washhh Allah na, hubby na gaji dayawa”
Yace yana riƙo hannunta
“sorry dear, mu je mu sayi abinci sannan mu wuce gida kiyi wanka se in miki tausa”
Murmushi ta saki, suna ƴar hira har suka isa restaurant bata shiga ba shi ya shiga ya fito daga nan suka yi gida.
Da kanshi ya ɗauko plates da spoons da ruwa ganin da gasken gaske ta gaji ɗin, don tunda ta zube kan kujera bata mike ba, Seda ya gama ajiye komai kan ta miƙe zauna buɗe ledar yayi tare da Fiddo takeaway ɗin yana buɗe psoup na kifin tayi hanzarin toshe hancin ta.
Kallonta yayi kan yayi magana ta mike da gudu tayi wurin dining sbd ɗaki ya mata nisa, a take ta fara kwara amai cikinta na murɗawa, a ruɗe ya riƙeta yana mata sannu ruwa ne kawai cikinta don tun safe da ta ci cips bata kara sha’awar komai ba, ta jigata sossai kan ya riƙo ta suka dawo tana kallon kifin ta sake fara kokarin amai cikin muryar kuka tace
“Don Allah yaya ka ɗauke kifin chan bata son gani”
Taimaka mata yayi ta zauna ya karasa ya ɗauke kifin zuwa kitchen yana mamaki.
Hannunta ya riƙe yace
“baki da lafiya ne shine baki faɗamin ba? Tun yaushe? Me ke damunki?”
Tace
“lafiya ta ƙalau kawai gajiya ce se kuma kifin nan bana son warin”
Yace
“wari kuma? Amma I thought kifi da nama na daga cikin abubuwan da kike so?”
Kai ta gyaɗa, yana ta kallonta se kuma yace
“wait..! Fauza”
Da sauri ta kalleshi, rabon da ya kirata da sunanta tun a yola, tace
“Na’am”
“when last kika ga jininki?”
Idanunta na kanshi ta tafi tunani, da sauri ta sanya hannu a kan cikinta tana cewa
“could it be possible?”
Yace
“sure, When last kika yi period?”
A hankali tace
“tun kan in bar nan in tafi yola, satin da ya kamata na fara kuka je kai da Fatima”
Ai da wuri ya tafi ya ɗauko mata hijab ya zo ya kama hannunta suka yi asibiti, bayan dogon gwaje gwaje Jafar ya musu albishir da ciki na tsawon wata uku bata taɓa sani ba se ranar, farin cikin da suka shiga baya misaltuwa barin ma shi da har Seda yayi hawaye, ze kira gida tayi saurin kwashe wayar tana shagwaɓewa.
“Eyyaaa yaya karka gayamusu don Allah”
Yace
“Meyasa bayan abun farin ciki ne ya same mu love?”
Tace
“Ai to ba zasu san abunda aka yi ba, ni dae bana so”
Dariya sossai ya saki, Fauza har yanzu taɓara irin na yara na damunta.