Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Se dab magrib suka rako su zasu wuce Dukda Fauza ta so su zauna se dare amma akwai inda Faahim ze je kuma ze iya kai dare sossai shiyasa ba zae Barsu yaje ya dawo ba, husna kam kin bin su tayi Fauza na murmushi tace
“yauwa ƴar gidana, ya fadyaa ku hado driver kawai da kayanta pls”

Duk dariya suka yi ganin yadda take ta murna daga ita har husnan, sallama suka yi musu suk fice da nufin za’a aiko mata da kayanta.

Tun a parlorn kasan Faizan ya dubi Fatima yace
“Ashe kina fita daga gidan nan ba tare da izini na ba? A iya sanina baki da lectures yau kuma na barki kina bacci”

“Yaya kayi hakuri wlh bayan fitan ka ne amai da juya ya matsa min nayi ta kiran ka kuma ban sameka ba shine na tafi ganin likita”
Ta faɗa a marairaice.

“Amma ya kamata ko Fauziyya ki sanarwa da zaki fita ba wai kawai ki fita kiyi tafiyar ki ba”

Ta Yi saurin cewa
“da ka dawo bata gaya maka ba? Na fa ce mata in ka dawo ta taimaka ta faɗa maka wallahi”

Fauza da tayi nisa a kan stairs ta dakata tare da juyowa da mamakin rantsuwar da Fatiman ke yi a kan karya, ganin kallon tuhumar da yake aika mata yasa tace
“kayi hakuri mancewa nayi”

Daga haka bata tsaya ba tayi wucewarta, a ɗakinta suka yi sallah da husna nan suka shiririce a kallo tana kuma sauraran surutun husna don husna akwai aikin surutu.

A ranar dae ba’a samu an kawo mata kayanta ba se wani shirt nata dogo ta sanya mata ya kuwa zauna mata suka je kitchen suka dafa pasta ɗan kaɗan a ƙasan suka ci kan suka hauro sama zuwa ɗakin Fauza..

Har sun yi shirin kwanciya don tana sanye da pjamas fari me layi layin baƙi me yauƙi wando da riga ya zauna mata sossai kanta ba dankwali tana kara kakkabe musu shimfiɗa ya shigo da sallama.

“Oyoyo uncle”
Husna ta karasa ta rungume shi

“oyoyo babyn uncle”

Hannunta ya kama suka zauna ya ɗan kalli Fauza da ta gama gyara gadon ta zauna daga baki tana wasa da nails ɗinta yace
“kin ci abinci?”

Kai ta gyaɗa tace
“Aunty Fauza ta yi mana pasta me daaɗi mun ci, it was so yummy uncle kaima ka ci ka ji ko?”

Girgiza kai yayi yace
“ban ci ba baby husny amma zan ci”

“babu wata matsala ko?”
Ya jefa tambayar ga Fauza.

Kai ta girgiza tace
“babu”

Sakin hannun husna yayi yace
“OK, baby go nd sleep karki manta da Adu’a”

Tace
“ok uncle”

Da gudu taje ta hau gadon ta zauna tare da Haɗa hannayenta wai tana Adu’a, murmushi duk suka yi na wayon yarinyar.

Miƙewa yayi ya sanya hannunshi duka biyu cikin aljihu yace
“madam ina wayata?”

Tace
“oh, yi hakuri ina ta zuci zucin baka na mance”

Tahowa tayi wurin kujerun ta ɗauka a inda ya tashi ta san ya gani ko me ya hana shi ɗauka se ya sakata zuwa ɗauka ta mika mai hanu da hanu oho mishi.

Karɓa kawai yayi ya juya, kaman tace mishi saida safe amma tana tsoron dizginshi har ya fice ta rage wutan ta dawo ta hau gadon ta kwanta tare da lumshe idanu tana tuna yinin ta na yau, se kuma ta tuna bata goge hotunan da ta ɗauka ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da taɓe baki ta gyara kwanciyarta.

Shi kuwa yana komawa ɗakinshi Fatima na shiga da shirin bacci, farin takarda ta mika mai tana murmushi, karɓa yayi ya buɗe a take shima fuskanshi ta cika da murmushi Dukda be kwallafa rai ba sanin cikinta baya zama amma shima yana son ganin gudan jininshi kaman yadda kannenshi kusan duk suke da nasu.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya sa wannan me zama ne fatee”

Tace
“in shaa Allahu Ameen”

Nan ta zauna tana gayamishi yadda Dr yace ta kula da cikin don kar a samu matsala, bayan ya gama sauraron ta ta kwanta shi kuma ya zauna tare da jingina bayanshi da gadon airpod ne a kunnenshi take ya shiga wani wuri a wayan yayi connecting ya sake komawa wani wuri ya fara duba voice recording guda biyar da ya gani.

Ba wai yana ghosting ɗinta bane, kawai natsuwarshi har yanzu be kama a kanta ba yana tsoron halinta na baya sossai shiyasa ya zame mishi dole saka idanu a duk al’amuranta.

Wayansu da jadda ya fara saurara, sossai yayi murmushi jin yadda suka drama a kanshi, yadda Fauzan ta zage take ta bada jawabi akan duk abunda jadda ta faɗa mata an yi a gidan yayi ta bashi dariya, bayan ya gama ya saurari nata da mammi, kaɗan yaji darajarta a zuciyarshi jin duk ta yadda mammi ta so taji laifinshi daga gareta ta tare.

“Ashe tana da hankali”
Fatima da ta fara bacci tace

“Na’am?”

Yace
“no yi baccinki maman baby”
Murmushi tayi kan ta sake runtse idanu cikin jin daaɗin sunan da ya kirata dashi.

Shi kuwa cigaba da sauraron Hirar ta yayi da Baba prof,, ya san tunda baba prof yace hakan dole ze fara mata shirye shiryen makarantar babu yadda ya iya.

Hiran ta da Ammi ne na karshe da yaji shi ya saka shi yin shiru ya tafi nazari, duk yadda yake Tunanin Ammin na ƙin shi ya wuce nan, kuma shi tun tashin shi ba ze ce ga abunda ya taɓa yi mata har ta tsane shi ba, akwai shakuwa me yawa tsakanin shi da fadeela sbd da kaɗan ya girmeta, yana sonta sossai matsayin kanwarshi ya kan je sashen Ammin a lokacin don wasa da fadeela saide yana iya tunawa vividly yadda baya barin sashen se da kuka, har ya girma yayi wayau Ammi bata taɓa kaunar shi ba, gashi yanzu ya auri ƴarta.

Fita yayi yana shirin kashe wayan hannunshi ya danna gallery, Jan kalar riganta ne ya saka shi sake kallon hotunan da suke jeren, hannu ya sa ya danna ɗaya, dariya ne ya kama shi ganin yadda ta tura baki wai ita nan tana style amma tayi kyau ba laifi, kallon hotunan yake yana dariya marar sauti daga karshe bayan ya gama ya girgiza kai yace
“this girl is crazy”

Ajiye wayan yayi ya kwanta tare da lumshe idanu bacci ya sureshi.

Washegari da safe aka kawowa husna kayanta, duk inda zata Fauza zata ajiye kafa husna na biye da ita, ga surutu tun tana amsawa har ta gaji, yamma likis husna tace se sun yi game.

“Toh faɗi wadda kike so se ayi”
Fauza ta faɗa don ta addabe ta da maganan game ɗin nan

Husna tace
“muyi wasan ɓuya Aunty”

Dankwalinta ta cire ta daurewa husnar suka hau wasan ɓuya duk sun cika ɗakin da hargowa Dukda su biyu ne kachal, bayan husna ta kamata da rigima da satar kallo itama aka ɗaura mata ta fara laluben husna..

Sam bata ji sallamarshi ba se jin mutum tayi da hanzari ta cabki hannunshi tana cewa
“yeeeeeyyyy wa na kama…?”

Dib dariyar ta ya ɗauke jin taushi da sanyin hannun ba na husna bane, da sauri ta zare kyallen dankwalin tana Kallonshi kaman yadda shima yake kallonta…

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

20

Ihun da husna ta sa na yeeey an kama uncle shine ya dawo dasu daga wata duniyar da suka tafi, da sauri ta matsa baya tana saukar da kanta ƙasa, shi kam basarwa yayi ya riƙe husna dake cewa shima a ɗaura mishi yayi tunda an kama shi yace
“A’a husny zan yi amma Ba yau ba, baki ga yanzu na dawo ba?”

Tace cikin yarantarta
“eh uncle, ina tsarabata?”

Ya kalli Fauxa yace
“Auntynki ta zo ta karɓa miki”
Yana kai nan ya juya ya fice.

Husna taje da gudu wurin Fauza tace
“Aunty fauza uncle wai ki je ki karɓa min tsarabata”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected