Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Tace
“uhm na soma kenan, ka isa lafiya? Ya ka same su?”

Ya ɗan yi shiru kan yace
“lafiya ƙalau duk suna lafiya, mammi na ta missing ɗinki”

Tana murmushi tace
“Allah sarki mammina nima nayi kewarta sossai”

Yace a ƙasan maƙoshi
“ɗan mammi fa?”

Dariya me sauti tayi tace
“Husna na ta tambayar ka, gidan shiru mu kaɗai shiyasa ma muka kwanta da wuri”

Shima basarwa yayi kaman yadda ya fahimci ta basar da tambayar shi yace
“in Shaa Allah gobe warhaka muna nan Kice mata kar ta damu sannan ki ce mata nayi missing ɗinku”
Yana kai nan ya yanke wayan….

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

24

kaman kuwa yadda ya ce ɗin karfe biyar daidai a bakin kofan gate ɗin gidan ya musu kaman kuwa sun Haɗa baki da wadda ya tuƙo motar Fatima ɗin tun asuba don suna parking shima yayi horn aka buɗe mai ya shigar, hana shi tafiya Faizan yayi yace ya shiga ya ci abinci in ya so ya sama mai wuri ya kwana se gobe ya wuce da sassafe ta tasha.

Godiya sossai mutumin yayi kan suka shiga ciki a tare, parlorn ƙasan ya sha gyara se kamshin turarukan wuta masu sanyi yake zubawa, murmushi ya saki sanin aikinta ne don kamshin a wurinta ya saba ji irin wannan kam, ji yake kaman yana ɗakin mammi ko jadda sbd natsuwa da ya saukar mai.

Kujera yayiwa drivern izinin zama shi kuma ya nufi sama don tuni Fatima ta jima da wucewa..

“Yaaa salaam!” Ya furta a ranshi a sadda idanunshi suka faɗa kanta, itama dakatawa tayi tana sakin murmushi da ya Karasa saukar mai da gajiya, da gudu husna taje tayi hugging nashi hakan ya dawo dashi daga wata duniyar da ya tafi, ɗauke kai yayi saide idanunshi basu koshi da kallonta ba.

Tayi kyau sossai cikin wani material silk da aka yi mata doguwar riga fitted ya fitar da duk wani siffanta ta saka jewelries fashion gyale baƙi a ɗaure bisa kanta, tana murmushi tace
“sannu da dawowa yaya”

Sam wlh babu wadda yake kallo a parlorn bayan ita be san Fatima na parlorn ba har lokacin seda yaji ta ja wani wawan tsaki ta wuce ɗakinta tare da doko kofa.

Duk kallon kofan suka yi kan suka kalli juna yace
“yauwa ƙanwata! Pls zamu samu abinci? Akwai baƙo a parlor yayi tafiya me nisa”

Tace
“kwarai kuwa baza’a rasa abinci ba, bari na duba mishi”

Kallonta yake ya ga ko zata fita a haka saide ga mamakin shi ta shiga ɗaki ta dau hijab ta saka kan ta fito ta nufi ƙasa, fuskanshi kaman gonar auduga ya bita da kallo har ta ɓace mishi.

Hira suke yi da husna tana mai rigimar ina tsarabarta har ta dawo ɗauke da jug da cup ɗinshi me kyau bisa tray, a gefenshi ta tsuguna ta tsiyaya mishi tare da miƙa mai.

Hannu ya sa yana karɓa sanyin abun na aika mishi da zakuwar son ɗanɗanawa Dukda be san me bane, kurbi daya yayi ya lumshe idanu yace
“wannan kuma me sunanshi ƙanwata?”

Husna tace
“laaa uncle kunun aya ne baka sani ba?”

Yace
“Husna uncle be saba shan me daaɗi da kaurin wannan bane but it’s so so giving wlh”

Dariya suka saka mishi, Fauza tace
“Yaaya ya su mammi da Jaddah? Baba prof da Baba Alhj da kowa da kowa dake gidan kowa na nan ƙalau?”
Ta faɗa a marairaice.

Yace
“kowa na lafiya, duk sun gaida ke”
Sossai tayi kewan su.

Bayan ya gama sha ya mike yana ce mata bari ya kai bakon nan masauki, ze yi magrib kan ya shigo. Seda ya gama faɗa kuma se yaji wani iri sbd ba sabawa yayi ba.

Tace
“Allah ya tsare a dawo lafiya”

Seda ya leƙa ya gayawa Fatima da ta amsa da kyar kan ya juya ya fice.

Fitowa Fatima tayi tana kallon Fauza dake kwashe abubuwan da ya sha kunun ayan tace
“mtseww ba girin girin ba dae tayi mai…”

Fauza bata yi niyyar tanka ta ba ta sake cewa
“cushe ba farin jini”

Dariya Fauza ta saki sossai kan tace
“Eyyaaa ai Alhamdulillah tunda ni umarnin iyaye nake bi kuma seda aka ɗaura na zama tashi kan nake cushen wata fa da ta gina komai a ƙarya?”

Matsowa tayi tace
“karki ga kaman kin ci galaba a kaina last week sbd cikina da kika ɓarar wlh yanzu se in nuna miki na riga ki shan iskar duniya”

Fauza ta mata kallon sama da ƙasa kan tace
“ko? Allah sarki abunda kuma aka koyar dake kenan? Iya shi kenan ko har da barbaɗe? Kin San Allah in da nayi niyyar shayar dake bakin ciki marar misaltuwa da nayi tuntuni ki kiyaye ni… Kaman yadda nake faɗa ki tsaya matsayarki sannan Haɗa jiki dake ai zubda aji ne, Allah sarki yayana bana so kayi tsiya, don kin san Haɗa ƙashi da kishiya miji yake janyowa tsiya.. Kuma komai lalacewar masa Fatima ai ta fi karfin kashin shanu”

Tana kai nan ta wuce ɗakinta don husna tuni ta shige, a daskare Fatima take tana bin bayanta da kallo, lallai yarinyar nan ta gama raina ta, ya tana mata kallon biri ita kuma tana mata na Ayaba? Ashe dama Fauzan kura ce lulluɓe da fatar akuya? Waye yake hure mata kunne ta mamaye min gida? Ihu ta kurma kan ta nufi ɗaki tana ji kaman ta sa wa gidan wuta kowa ya huta.

Bayan ya dawo ta gabatar mai da abinci Dukda bata yi niyya ba amma ganin yau suka dawo yasa ta bashi, amma gobe kam matarshi da ta iya girki ita zata cigaba da sama mai abunda ze ci dama taimako tayi.

Tuwon alkama ne da miyar kuka ya ji ma shanu naman kazan nan yayi raga raga a ciki, ya ci sossai kuwa kan ya kira su duka parlor, nan yayi musu faɗa sossai akan rikici tsakaninsu ya kuma gargadesu da kar ya kara ji bare gani, daga karshe ya ɗaura da
“Fatima tunda kina da mota Zaku dinga tafiya school da fauza har muga yadda za’a yi”

Tace
“Toh Yaya in shaa Allah”

Fauza da bata so ba kuma har a fuskanta ya nuna ya kalla se tace
“in shaa Allah, mun gode”

Daga haka ta mike tayi ɗakinta da kallo ya bita har ta shige, sadda Fatima bata nan kusan a parlorn suke kashe lokacinsu amma yanzu tana so ta komawa halin farko da ta fara zama a gidan.

Mikewa yayi ya bi bayanta, husna na kallo ya nufi wurinta don tana tsaye ne gaban wardrobe kuma in ba husna ta taso ta zo wurin ba ba ganinsu zata yi ba.

Dab da ita ya tsaya har tana jin kamshin shi na cika mata ciki, yace
“Bakya so ne?”

Ta ɗago tace
“me fa?”

Bakinta yake kallo kan yace
“seems like baki ji daaɗin zancen tafiya school da Zaku ke yi da Fatima ba, for now it’s my only option don in aiki ya min yawa ba zan dinga iya kaiki ina ɗauko ki ba and I hate it so much in ga matata tana hawa motar haya ko bolt ne kuwa”

Juyawa tayi tana kokarin buɗe wardrobe ɗin tace
“ba komai, na fahimta”

Har yanzu ranshi be bashi ta gamsu da hakan ba, ya rasa me yasa ya matsu kuma yake so ta fahimce shi ba don cin fuska bane yayi hakan, amma dae haka ya hakura ya fita kar ya janyowa kanshi raini a faɗar shi fa kenan.

Washegari da safe ya fito tsab a shirye saide ganin Fatima tsaye a dining yasa ya san yau kam ze yi missing girkin Fauza, zama yayi tayi serving ɗinshi kaɗan ya ci ya miƙe yana duba agogo yace
“zan ɗan fita wani meeting ba zan dawo yanzu ba ku kula pls”

Daidai ya nufi cikin parlorn Fauza ta fito rike da hannun husna shirye cikin hijab dogo tayi kyau sossai, tace
“Ina kwana yaya?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected