Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Fauza tace
“Toh husna”

Husna tace
“Aunty in kallo MBC kan ki dawo?”

Kai kawai Fauza ta ɗaga, kan ta ɗauki hijab ɗin sallarta ta zura tare da fitowa, baya parlorn don haka ɗakinshi ta wuce tayi knocking aka bata izinin shiga.

Ta tura a hankali ta shiga, this is the first Time da ta shigo ɗakin, tsaruwa da haduwar ɗakin ya tafi da ita kasancewar shi me son fari hakan yasa komai na ɗakin fari ne, sossai tsarin rashin hayaniyar ɗakin yayi mata kyau, a kan kujera yake zaune ya tankwashe kafa, hannunshi wani daily trust ne yana dubawa.

Ta ɗan rusuna tace
“ga ni yaya”

Da hannu ya mata nuni da ledojin da suke kan table wadda Fatima ce ta ajiye ta je kuma ɗauko plates da sauran abubuwan da zasu yi anfani dashi ne, yace
“Ki dauka muku ɗaya”

Tace
“An gode Allah ya saka da alkhairi”

Se a lokacin ya ɗago yana kallon face ɗinta da ya fito fess a onion hijab ɗin nata, daidai lokacin kuma Fatima ta shigo ɗakina gabanta ne yayi wani irin faɗuwa wadda seda cikinta ya nemi kullewa, a makogoronta taji wani abu ya tiƙe ta me take yi a ɗakin nan? Ta tambayi kanta kan ta karasa daidai lokacin ita kuma Fauza ta ɗauka ta juyo.

Da wani irin banzan kallo Fatima ke bin ta, ta san duk sbd wannan Husnan nan ne har Fauzan ta samu shigowa ɗakin mijinta, daga yarinyar har Fauza ji take kaman taje ta sa musu wuta a ɗakin su mutu, sbd yanzu bayan shigan asuban shi duk in ya dawo se ya shiga, gashi Faizan mutum ne da babu fuskan kawo mai wargi ko tace zata hana shi abunda yayi niyya, gaskiya bazata iya hakuri ba kaman yadda take aika mata da harara haka itama ta rama tare da jan tsiririn tsaki wadda ya sake hasala Fatima har bata san ta furta

“kan uba!”
Ɗagowa Faizan yayi yace

“lafiya?”

“Baby yarinyar nan wai ta buge ni kuma ko sannu babu tayi wucewarta?”

Yace
“Fauza?”

Haushin kiran sunan tan ma ya sake mamaye ta tace
“ita fa”

Shi har ya manta da ainihin halinta don yanzu yana ganin babu shiru shiru irin ta, sannan ga saurin bada hakuri wadda wannan na daga cikin abunda yasa tunda ta zo gidan faɗa me tsayi be taɓa hada su ba don duk ɓacin ranshi da zaran ka ce mishi yi hakuri shikenan, fauza bata san shi ba bare ta san lagon shi.

“Tunda har ta fita bata sani bane na san da ta baki haƙuri, yunwa nake ji zo yi serving ɗina”

Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi serving ɗinshi ta mike yana tambayarta bazaki ci bane? Ko bata juya ba tayi ficewarta, girgiza kai yayi yana mamakin halayyar da take nuna mishi tun daga shigowanta gidan, tabbas ba don shi jajirceccen namiji bane da se abunda Fatima tace a gidan za’a yi, ita in har ba’a yi ra’ayinta ba tayi ta fushi kenan tana kumbure kumbure?

Abincin shi ya ci ya koshi ya wuce toilet yayi brush da wanka ya zo ya sauya zuwa kayan bacci, kwanukan ya fitar da sauran abubuwan makulashen da ya sayon ya kai fridge ɗin kitchen, daga nan ya wuce ɗakinta ya samu wai har ta kwanta be tanka mata ba ya fito ya nufi ɗakin Fauza.

Suma ya sa mu sun kwanta kuma har ma sun yi bacci, fitowa yayi kawai ya koma dakinshi ya kwanta shima don yana da flight 8 zashi Lagos amma around 9 na dare ze dawo..

Washegari yana idar da sallah yayi sauri ya watsa ruwa ya shirya kan ya fice bayan ya leƙa Fatima da bata tashi Bama, don ita wai don ze yi tafiyar sassafe ta samar mai abinci bata san wannan ba sede in yaje airport ya karya a chan kan ya wuce, be damu ba sbd dama chan haka yake yi.

Tana jin fitan motan shi ta mike zaune, tare da sauka daga gadon dama tayi wanka kawai ta saka kaya ta yafa gyalen ta ta fito, tun wata biyun farkon aurensu ya koya mata mota kuma ya saya mata wata karamar Hyundai, direct kitchen na sama taje ta rufe da key, ta sauƙa kasa ma ta rufe ta haɗe keyn ta watsa jaka kan tayi ficewarta daga gidan.

Bayan su Fauza sun tashi tayiwa husna wanka itama tayi suka gyara gidan tare duk bata lura kitchen a rufe ba se bayan ta gama taje ta murɗa kofan ta ji shi a rufe, kitchen na sama ta dawo taji a rufe, da mamaki take kallon kofan kan ta wuce kofan Fatima ta murɗa shima a rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta kama hannun Husna suka koma ɗakinta da Tunanin Fatima ba nisa tayi ba Dukda dae ita bata taɓa gani an rufe kitchen ɗin ba duk zamanta a gidan.

Sauran kazan jiya ta turawa husna da Admiral ‘A Dukda yayi sanyi sossai haka dae ta lallaɓa husnan ta ci, bata san lokacin da zasu dawo ba hakan yasa bata ci ba ita gudun kar kuma basu shigo da wuri ba husna ta sake jin yunwa.

Wasa wasa har azahar babu wadda ya dawo a cikinsu gashi lokacin yunwa ya fara kama Fauza da babu abunda ta saka a cikinta, sauran kazan ta sake baiwa husna ta cinye.

Tun suna kallo har taji bazata iya cigaba da kallon ba sbd yunwa da yake shirin yi mata illa, bayan sun yi la’asar ta duba jakanta ta fiddo kuɗin da Jaddah ta sanya mata ciki tun randa za’a kawo ta tare da sanya hijab ta kama hannun husna suka fito, saide me gadin wadda yoruba ne yace mata oganshi ya mishi umurni kar ya barta ta fita daga gidan ba tare da izininshi ba.

Rokon shi ta fara saide tsoron rasa aikinshi yasa be kula ta ba, don Sam be san ita ɗin matar Faizan bace ba ma, haka suka hakura ganin tsayuwar baze yi musu ba suka koma ciki amma fa ganin magrib yayi ga dukkansu biyu yanzu sun jikkata don husna har ta fara kuka yasa ta sake fitowa ta roke shi ko ze kira mata ogan nashi da Wayanshi don ta san dae duk muguntar Fauzan in har ita ze iya mata to baze iya yiwa ɗiyar kaninshi ba, unfortunately layinshi baya wucewa.

Haka suka sake dawowa parlorn kasan tana jin yadda ƙasan cikinta ya riƙe kam kam kaman zata mutu, daurewa take tana rarrashin husna da yanzu ta fara kiran iyayenta se tausayin yarinyar ya kama ta, fita tayi ta fara duba gidan, ba irin gidansu bane bare ta iya zamewa ta fita, ba kuma zata iya faɗawa me gadi abinci babu zata je su saya ba sbd ta san hakan kaman wani tonon asiri ne ga Faizan wadda be kamata gida kaman nashi ace babu abinci ba me gadin ma ba yarda ze yi ba.

Hawaye ne ya gangaro mata ta sa hannu ta share, bata da waya bare tayi order a kawo mata har gida.

Komawa sama tayi zuwa dakinshi banda sassanyar kamshi shi babu abunda yake tashi, duk irin dubawar da zata yi bata samu wayan da ya ara mata jiyan ba. Kuma Sam bata kula da lockers ɗin gefen fridge ba waenda snacks ne a ciki da su dangin cereals tunda ta san ita nata babu komai ciki.

A ƙasa ta saka gwiwowinta ta ɗaura kanta a kan gadon hannunta dafe da mararta dake wani irin kugi, husna ce ta biyo ta tana kuka sossai ita tana jin yunwa, miƙewa tayi ta kama ta tace
“mu je mu yi isha se mu koma ko mai gadin ze yarda mu fita”

Komawa ɗakinta suka yi ta bar ɗankwalinta anan a ɗakinta suka yi sallah shima ba natsuwa, ko da suka sake fitowa neman yiwa mai gadin bayani take saide be kula ta ba, masifa zata fara mishi saide bata da karfin hakan kasancewar bata bar ko ruwa ne ya shiga cikinta ba.

Rarrashin husna kawai take suna tsaye kaman marayu se suka ji horn, da sauri me gadin ya karasa ya duba ganin oganshi ne yasa yayi hanzarin wangale gate ɗin.

Wutar motar shi ne ya haske mishi su yadda suke tsayen yasa gabanshi faɗuwa.
“Peter, me ya kawosu bakin gate?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected