Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Chan da yunwa ya fara damunta don ko abincin rana bata ci ba ta sa a zuciyarta zata ci wainar fulawa yasa ta mike ta fito a hankali ta nufi kitchen, ja tayi ta tsaya jin kuka na tashi a hankali….
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Bakwa*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA❤️**
“Aunty wallahi son shi ze kasheni! Kin Reneni ne da soyayyar shi hakan ya bani karfin gwiwar kwallafa rai a kan samunshi sede gashi har yanzu shi bana gabanshi, yanzu har fa su fa’iza sun san nice me cusa kai a gareshi shi ba ta ni yake ba! Aunty kinga wulakancin da ya min a gaban su Fa’iza da kannenshi maza?”
Ta karasa tana me kara rushewa da kuka.
Aunty tayi saurin sa mata hannu a baki tace
“Haba Fatima! Me yasa ke kam kullum rashin haƙurinki kara gaba yake? Na faɗa miki na kara jadadda miki idan har Faizan be aureki ba to wallahi ba ze auri wata ba, wannan alqawarin da na daukar wa kaina ne tun kan in shigo gidan nan, tufka nake ana warwarewa amma ba matsala ki kwantar da hankali na miki alqawari Faizan ba ze bar garin nan ba tare da an tsayar da magana tsakanin ku ba!”
Wani wawan tsaki Fauxa ta ja kan ta juya ta fice daga gidan gabaɗaya, a chan gefe da sashensu inda aka yi wasu kujeru haka masu kyau na tayoyi ta zauna, tana me kallon qonannan hannunta, murmushi ta saki na jin daaɗin ba ita ba aikin gida har se ta warke, makaranta ma in ta je ba rubutu ai kuwa za’a sha neman tsokana.
Bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a wurin ba, chan ta hangosa yana tahowa cikin tafiyar nan tasa me cike da natsuwa kaman saraki, sanye da wasu kananun kayan still farin Jean da navy blue shirt a ko yaushe Adonshi da shigar shi masu kyau ne da salo irin na burgewa.
Maganan Fatima ne ya faɗo mata bata san sadda ta kwashe da wani irin dariya ba har da hawaye, wai amma Fatima tayi asara ta taɓe duniya da lahira fisabilillahi ta rasa abun so se wannan? Dariya take tayi tana sakewa wai fa har da kuka Fatima ke yi sbd shi? Ta kara kwashewa da dariya tace
“Taabbb Allah ka rabani da aikin wahala”
Har ya wuce tana babbaka dariyar ta kaman sabon kamu inda Allah ya taimake ta ba Kallonshi take ba don ta san in har ya san dashi take yadda ba kowan nan se na lahira ya fi ta jin daaɗi, ji fa yadda yake tafiya, ita wallahi tafiyar da yake yi ko ita mace bazata yi irin shi ba, dariyarta tasha daidai sashensu na samari ta ga ya ɗan tsaya ya waigo, daidai itama ta ɗago ta kalle shi se suka Haɗa idanu, kallon kanki ya taɓu ya watsa mata.
Ko seconds biyu be yi ba ya juya ya karasa shigewa sashen, mikewa tayi tana share hawayen dariyarta kaman wacce duniya ta yiwa daaɗi ta wuce sashen Jaddah, tana shiga ta narke tana tafiya kaman marar lafiya.
Jaddah tace
“zo ki karbi tsarabar ki na wurin Faizan”
Haɗe rai tayi, Fa’iza tace
“ke kinga rikicin da aka kwasa da ya Faizan kan Jaddah ta kwasar miki chocolates ɗin nan karfi da yaji? wlh ki gode mata ta san yadda kike son chocolates shiyasa, ga su da daaɗi kaman zasu tsige kunne”
Kallon chocolates ɗin tayi masu tsada ne sossai, daga gani ma maybe ba a nan Nijeria ya sayo su ba sede tunda daga hannunshi ya fito basu ba ta sha’awa ba, kau da kai tayi tace
“Jaddah da baki wahalar da kanki ba don ni kam ba sha zan yi ba”
Jaddah ta saki baki zata yi magana kenan Fauxa ta fara kukan hannunta na zugi, da sauri Jaddah ta karɓe hannun tana salati tace
“Faozia garin yaya? Me ya sameki haka?”
Ai jin tambayan Jaddah yasa ta kara narkewa tana fashewa da kuka, she’s so fragile in tana abu kaman little baby, Fai’za tace cikin damuwa.
“Jaddah ita da ya Faizan ne”
Nan ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, Jaddah tayi ta masifa ta kuwa ci alwashin se ta saɓa mishi wani irin mugunta da bakin hali ne wannan?
A kan cinyar Jaddah ta kwanta tana jin daaɗin yadda Jaddah ke ta zuba mitan abunda ya farun, ta kara da
“mutum ne se baƙin miskilanci yanzun nan yasa yarinyar da yake ikirarin buduruwarshi ce kuka amma ko a kwalan riganshi”
Kau da maganan Fauxa tayi don be shafe ta ba, anan ta kwana ma yau..
Washegari Monday ko aiki ɗaya bata yi ba da taje school ma babu abunda ta rubuta se surutu da neman magana, a ranar Ammi ta dawo itama Seda tayi faɗan hannun nata sede baba Alhj be ce komai ba.
Bayan 2days ta ɗan samu sauki ta cigaba da aikinta, zuciyarta kuwa na kiyasta mata yadda zata rama abunda ya mata sbd ta sha wahalan qunan sossai.
Yau tana kwance bisa kujerar Jaddah tana danna ƴar karamar wayar jaddahn sbd ita ba kaunar kallon tashoshin wa’azuzzuka da shi kaɗai suke dashi gabaɗaya gidan take ba, jaddah ta fito rike da tray tana kallonta tace
“Fauziyya don Allah miƙawa Faizan abincin nan kinga yaran duka suna wurin Ibrahim(baba prof)”
Haɗe rai tayi tace
“Jaddah eyyah ki jira su in sun dawo su kai mishi”
Jaddah ma rai ta ɓata tace
“zan saɓa miki wlh Fauziyya, ki wuce ki tashi ki kai in dodonki ne se ya cinye ki, in kuma baza ki je bane ki gayamin”
Hawaye ne ya cika idanunta, ita ba mikewa take son yi ba don ko da yaran suka je wurin baba prof da be ganta ba seda ya aiko fakiha tace mata tace tayi bacci idan kuwa bata ce haka ba se ta kirɓa ta in aka dawo sake kiranta, gashi yanzu Jaddah zata saka ta kaiwa wannan azzalumin abinci.
Mikewa tayi ta ɗauki tray ɗin da Jaddahn ta dangwalar ta fito, shiru tayi tana tunani, in ta taɓa ji da kyau Jaddah ta taɓa maganan rashin son yajinshi sbd muguwar ulcer ɗinshi ko yaya ya ci yaji se ya kwanta, murmushi ta saki taje kan kujerun tayunsu ta ajiye tray ɗin da gudu ta koma gidansu taje ta fara binciken drawer ɗinta akwai wani yaji me zafi da ta daka ranar girkin Amminta sbd an yi mata dole daka yajin shinkafa da waken, kowa da wahala yaci yajin sauran ne ta kulle ta boye a sif ɗinta.
Da gudu ta dawo ta buɗe miyan kubewa danyen ta juye duka, cokalin da ta biya ta ɗauko a kitchen ta saka ta juya kan ta ajiye shi a wurin, ta dauki abincin ta nufi sashensu, a gaban site ɗin ta kalli Haɗaddiyar beymach ɗinshi baƙi siɗik se ɗaukar ido yake da yayi parking a wurin, baki ta taɓe ta isa kan motar da sbd yanayin kyaunta mutum kan iya finshi tsawo ta ɗaura a kai ta juya tayi tafiyar ta.
Tana nan kwance a parlorn na Jaddah har wuraren karfe tara da rabi, wayan Jaddah ne ya fara ringing ta ɗauko ganin Faizan ta taɓe baki ta mayar ta ajiye tare da lumshe idanu kaman tayi bacci, Seda ya kira sau biyu a na ukun ne Jaddah ta fito tana tambayar Fauziyya kam bacci tayi ne ana ta kira bata ji.