Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Tara*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA❤️**
Ƙurawa kanta idanu tayi a Door size mirror na ɗakin tana jin sukar kalaman iyayenta a kanta, lallai kam basu faɗi abunda ze gyara mata rayuwa ba se ma wadda ze ɓata saboda hango abubuwan da zata ke yi musamman wadda a da gudun ɓacin ran nasu yasa ta danne burinta take rayuwa yadda ta taso ta gani Dukda baya cikin tsarinta, kallon kanta take da kyau tare da lumshe idanu tana tuna maganar sakina.
“Ke yadda kike da kyaun nan da sura wallahi kika fara ɗaukar wanka kika zama ƴar gayu ba karamin rububi maza zasu yi a kanki ba, kin san kuwa irin baiwar da kike dashi na fusgan hankalin mata ma ba maza kaɗai ba? Babe ki waye pls ki dena kunshe kanki cikin hijab”
Ajiyar zuciya ta sauke tana tuna amsar rahama.
“Ke wallahi abunda Sakinah ta faɗi gaskiya ne baki ganin yadda duk muke rayuwa cikin wayewa da aji da izza? Don Allah hakan baya burgeki? Amma ku kullum gidanku hijab hijab Ina ka fito karatu ina zaka karatu, babu babban waya, babu samari babu hangout da su party, wallahi kuna cikin duhu”
Ba kalaman nasu bane ke tunzura ta sede illa irin tsarin rayuwar da take so ɗin kenan se ya haɗu da maganganun su yake tasiri a hankali a ranta sede yanzu kalaman iyayenta ya hauhawa su kaman tashin farashin man fetur, a yanzu take jin zata fara nunawa su baba prof ba irin rayuwar su take so ba, ko da zasu yanka ta su fige tane.
Rahama da sakina ƴan ajinsu ne waenda suka shigo third term na SS1 ɗinsu asali a Abti suke sede rashin jinsu, da yawace yawace yasa iyayen Rahama suka cire ta suka dawo da ita Elkenemy ganin makarantar musulunci ne kila ta shiryu sede ba tare da sun sani ba sakina ma ta uzzuruwa iyayenta suka sake dawowa suka jone a ajin su Fauxa, tunda suka ganta suke admiring kyaunta da kalar idanunta suka fara nuna mata yadda zata ja hankali tare da tada hankalin maza a tiktok sede bata mai da hankali ba, iya kaci taji wakoki da wayoyinsu tayi ta kallon mata masu class a Instagram waenda har ga Allah suke burge ta.
Tana matukar son gayu da class sede su gidansu ko ba hijab baka isa fita ba, a daren ta fara tsara yadda zata sauya rayuwarta zuwa ra’ayin kanta ba ra’ayin wasu ba, sallamar Faazila ya sa ta ɗago idanunta da suka sauya ta zuba mata, birkicewa yarinyar tayi don ta san sarai yanzu se Adda Fauxa ta mammake ta yadda take a harzuke ɗin nan.
“Me??? Kin zo kin wani yi min kerere kina kallona?”
Baya ta ja tace
“Mammi ce tace in kira ki”
Dauke idanunta tayi ba tare da ta amsa ba ta juya ta dauki hijab ɗinta ta saka tare da fitowa zuwa sashen Mammi, tana shirin shiga ɗakin Fatima na shirin fitowa da gayya ta bangaje ta har Seda tayi baya tana kallonta sede ko kallo bata ishi Fauxa ba ta wuce zuwa wurin Mammi tana daidaita fuskanta Gaisawa suka yi Mammi tace
“Fauxa zo don Allah kiyi min tofi a kafan nan”
A ladabce tace
“to Mammi”
A gabanta ta duƙa ta fara se Fatima ta shigo da bowl na fruits a hannunta ta ajiyewa Mammi ɗin tana cewa
“Mammi Adu’a ce ake yi?”
Mammi tace
“eh wlh jiya da ta min baki ji yadda na ji daaɗin kafafun ba”
A fakaice Fatima ta aika mata da wani kalar kallo tare da taɓe baki, ina Fauxa ta ma san tana yi, wai harara a duhu, bayan ta gama mata ta fice don bata jin magana in kuma ta zauna inuwa daya da Fatima karshe se Mammi ta raba faɗa.
Washegari a class bayan an tashi break ta kalli rahama tace
“am interested in ur way of life taya nima zan fara?”
Rahama da sakina suka yi wani ihu tare da tafawa suka ce
“welcome to the club babe”
Sakinah tace
“dama akwai wasu Zafafan dinkunan da zamu yi har ma mun yi placing order ɗin materials ɗin amma tunda zaki yi bari na sa dake”
Fauxa tace
“amma fa bani da kuɗi kun san gidanmu ba wani bada kudi ake banza banza ba”
Rahama tace
“don’t mind dear! anything for you precious ”
Sakina tace
“bare ma kwana biyu zaki fara rike wasu makudan kuɗin da se kin ji tsoro just chill babe”
Aiko gwada ta suka yi suka turawa tailor ɗin su, nan suka fara nuna mata mahaukatan dinkunan tana kallo cike da yabawa..
Iyaye ya kamata mu san cewa duk fushin ka da yaro ba kowacce kalma ya kamata ka furtawa ɗa cikin fushi ba domin baka san irin influence da zaka yiwa yaro ba idan har Allah ya amsa.
MAFARI
Dukda rashin son karatun Fauxa ta kasance mace mai son karance karance, hakan yasa bata rabo da littafi ko na turanci ne, babu kalar abunda bata karantawa hakan yasa abubuwa dayawa tana da masaniyar already aikata shi a fili ne kawai bata yi ba.
Wani irin kalar Juyawa rayuwar Fauxa yayi cikin lokaci kankani, idan tayi dressing se ka dauka ba Fauxan gidan baba prof bace, Fallin balaga ya buɗe rashin M ɗin ta se abunda ya karu ga rashin daukar raini, se neman tsokananta da yayi sauƙi sede fa ba shi ya hana kana ce mata Kule ta ce maka chass ba.
Abunda take yi shine tunda yanzu Sam Sam ba cika zuwa part ɗinsu tayi ba se idan zata gaida Ammi don baba Alhj ma ta manta rabon da su haɗu tunda ya ce baya kaunar ganin fuskanta ta gwammaci ta dinga wasan buya dashi.
Idan an tafi school daga an tashi break zata yi bribing gate man sbd su Rahama ma ba cika zuwa suke ba se once or twice in a week, zasu ɗauke ta a gate su tafi gidansu rahama inda wasu abubuwanta suke a nan zasu yi dressing ɗinsu na class su fice yawo, samari kuwa kaman kuda a kan Fauxa hakan yasa ta juya wannan ta waina wanchan ga yadda take sha musu kamshi kaman ƴar shugaban kasa, ɓarin kudi suke mata ba na wasa ba har ta mallaki iPhone 13pro na kanta kuma har gida take zuwa da abunta.
Ta chanza mayukanta gabaɗaya zuwa wasu organic masu tsananin tsada, na kafa daban na gashi daban na fuska kala kala, in ta wuce ka se ka jima kana jin kamshin designers perfumes na jikinta.
Aka ce akuyar ɗaure in ta samu sake Habaaa, har Sakina da half rayuwarta outside tayi wani lokacin ta kan mutu da kalar gayun Fauxa sede a gida har yanzu babu wadda yayi noticing ana getting to five months.
Sau ɗaya fa’iza ta taɓa mata maganan rashin zamanta aji se da ta ja mata katoton layi tayi mata fata fata wadda har ta Haɗa da mahaifiyarta hakan yasa fa’iza dauke kai daga rayuwar ƴar uwar tata.
Se dab za’a tashi school take dawowa su koma tare da ƴan gida, wayanta kuwa kullum a ɓoye yake kasancewar ɗakin da take a sashen Jaddah ita kaɗai ce, yanzu damuwanta yadda zata fara fitan dare sbd ana kawo mata cikas sossai da ganin ƙarancin wayewarta sbd rashin zuwa night parties ɗin nan.
Zama tayi ta tsara yadda zata ke fita abunta bayan isha zuwa asuba, randa ta fara gwada luck ɗin ta Dukda yadda take a tsorace kuma cikin bugawar zuciya haka ta saka dogon hijab ɗinta bayan ta yi wanka ta gama duk shafe shafenta, fuskanta da ba ko Digon powder se wani ɗaukar hankali yake sbd kyaun da ta kara na musamman, wurin Jaddah ta je tace