Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Dukda ya tabbatar min da cewa ko an nakasta kafafun nata zata iya cigaba da nemawa yaranta kariya wurin rabba se na ce ya saka mata ciwo me tsanani wadda baze bar ta natsuwar lafiyar nema musu sauƙin ba, kwatsam se muka samu ciki ni da Ruqayya, da na koma ya duba min se ya tabbatar min yarinyar cikin Ruqayya masifa ce ga rayuwata don itace zata yi silar tabarbarewar duka aiki na in ban yi wasa ba, kai tsaye na nemi a ɓarar da ita ta bi rariya yace in bada kwanaki, duk wani hanya da ze bi don zub da cikin babu nasara ko da ya faɗamin nima ban zauna ba, hatta da maganin zubar da ciki na saka overdose na bata a kunu sede cikin nan ya ƙi barewa abun ba daaɗi wai mahaukaci ya ci kashi, duk inda muka buga cikin nan yaki ya lalace se ya kawo shawarar a dasawa mahaifanta tsanar ta musamman uba, suyi ta mata mugun fata ita kuma tun daga cikin za’a sa mata taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa..
Hakanan destiny ɗinta a sarƙe yake da Faizan shima za’a saka mishi tsanar ta kaman yadda itama baza’a bari ta so shi ba ko na minti guda, duk a aikin mun manta da Jaddah, Baba prof da mammi a tsanar na Fauza saide mutanen duniya da iyayenta yadda za’a yi ta mata baki ta bi duniya… Hakan kuwa ta kasance don haka ta ta cimma ruwa sbd tunda Fauziyya ta fara wayau kowa ke kuka da ita.
Mun kawar da hankalin baba prof kan Faizan ta yadda duk haɗe Haden auren da yake yi be bi ta kan Faizan ba, Ganin kissa ta bazata saka Faizan ya kula Fatima ba yasa na koma ma bokana da kukan damuwata, nan da nan ya ce ze yi aikin karkato hankalinshi dama already kaman yadda akwai tsana me girma tsakanin shi da fauza haka tsakanin mahaifiyar Fauza dashi, ita kuma ta fara jin haushin shi ne sbd abubuwan da yake yiwa fauziyya amma dayake bata da damar nunawa sbd akwai aiki a kanta se ya zamana ta fara tsanar shi a ranta wadda mu kuma muka kara rura wutar.
Fatima ta tashi ne da tsananin son Faizan sbd shine nake kwadaitar mata a kullum as miji, ita tayi ta matsawa nayi ta shiga da fita har aka ɗaura aurensu suka tattara suka tafi, burina na lalacewar rayuwar Fauza ya cika na kuma san ko a kafa aka ɗaurawa Faizan ita se ya kunce ya yasar, sbd ta zama itace yawace yawace, shaye shaye da Zin…..”
Faizan da Jaddah suka Haɗa baki cikin kunan rai suka ce
“Fauza bata yi zina ba..”
Hawaye ne ke zubarwa Jaddah kaman yadda Fauza ke kuka marar sauti tana jin ita kuma yadda aka yi da rayuwarta tun tana cikin cikin mahaifiyarta.
Cigaba Da bayani tayi..
“Kwatsam Professor ya shammaceni aka ɗaura auren Faizan da fauza duk wata hanya da zan bi wurin ganin na wargaza auren hakan be yiwu ba, na ba Fatima baki akan duk yadda zamu yi mu lalata auren se mun yi, bani da masaniyar cewa igiyar aure da girman darajarshi ya warware wasu abubuwa nawa masu dumbin yawa akan Fauza ciki har da rashin ji da saurin faɗa, rashin kunya da kuma shaye shaye, se da na koma wurin bokana yake faɗamin, Fatima taki kwantar da hankali tayi tayiwa Fauza abubuwa wadda a hankali ya kawo kusanci tsakanin Fauxa da Faizan se kuma ta dawo ta haukacemin, gashi Allah da ya fi ni dabara se ya hana cikin Fatiman zama bare in saka ran mallakar burina.
Komawa nayi nace ko ta karfi ko ta tsiya a fitar da fauza daga gidan Faizan, ko kasheta ne ayi, shine aka tura mata ƙadangare da nufin kasheta amma Allah ya bata kariya, aka sake nufin haukatata sbd ranar ne muka samu dama ta kwanta da zazzaɓi bata iya tayi Adu’ar bacci ba shi kuma Faizan ya mance be yi mata ba, a son mu ne fitan tan nan ta bi duniya amma se Allah ya sake kare ta ta kawo kanta gida. Wannan shine abubuwan da na aikata ni shamsiyya….”
Salati kowa yake yi, wasu na ta kuka barin ma fa’iza da ta fi wayo cikin yaranta kaman zata hadiye ranta, Farhan ne dake kusa da ita ya iya miƙa hannu yana lallashin yarinyar, Allah sarki uwar su bata duba kananun yara har uku da take dasu ba kwata kwata babu wacce ta kai secondary, ta aikata irin waennan abubuwa har gwara su kuma da Fatima da ta ɗaura a Keken ɓera wadda ya dire su a tashar dana sani.
“Fauziyya me yasa kika amsa Faizan cewa kina shafawa Aisha magani?”
Baba prof yayi mata tambayar, tana cikin ciwo bazata iya magana ba, abubuwa sun mata yawa kuma sun haɗe mata, Aunty da Fatima sun cutar da ita mafi munin cuta kuma bazata taɓa yafe musu ba har duniya ta tashi.
Kirjinta ciwo yake mata, gabadaya ji take kaman zata mutu.
Ammi ce tace
“Kwarai tana shafa mata magani da wani Adu’a wadda ni na bata, maganin kuma wurin kawu na Wadda yake bada magungunan gargajiya na musulunci nake karbar mata sbd tausayin halin da take ciki wadda ba zan iya nunawa ba, Fauziyya…”
Ammin ta kira sunanta, ɗagowa tayi har bata iya kallonta da kyau sbd kuka ta amsa..
“Ki yafe mana iyayen ki Fauziyya don Allah ki yafe mana mun kasa baki kariya kaman na kowa su iyaye, tun kan ki zo duniya muka yi saken da aka cutar dake barin ma ni mahaifiyarki, ki yafemin don Allah”
Kai take gyaɗawa tana kuka, Baba Alhj ma dake kuka sossai yace
“Fauziyya nima ki yafe min irin kalamai da tsana da na ɗaura miki, ki yafe mana don Allah kwarai bamu kasance iyaye na kwarai a gareki ba..”
Girgiza kai tayi cikin muryarta da baya fita tace
“Na yafe muku wallahi Ammi, ban taɓa rikeku ba, ko na riƙe ɗin Jaddah da ta zame min uwa kuma uba ta kan nusar dani har in yafe muku, tabbas ban samu gatan iyaye ba saide na samu gatar kakata wadda har Abada bazata taɓa fita cikin mutanen da suka fi kowanne daraja a rayuwata ba… Mammi kiyi hakuri da irin amsar da na bayar”
Mammi tace
“Fauza nima na ji ne kawai Amma ban amince ba, ko kin manta a duk sadda kika taimakamin na kan yi bacci cikin kwanciyar hankali? Wannan kaɗai ya isa shaidar cewa ba don cutar dani kike yi ba”
Su ya Farhan ma yafiyar ta suka nema duk ta amsa da ta yafe musu, se a lokacin Faizan ya iya ɗaga kai ya kalleta zuciyarshi kaman ze fashe da tausayi da kuma ƙaunar ta, lallai ta ga rayuwa kuma daga yanzu yayi alkawari wa kanshi cewa har Abada baze taɓa judging mutum by cover ba, Fauza yarinya ce amma kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu babu ita.
Hannu ta mika ta rike na fa’iza dake wani irin kuka ta kasa kallon ko mamanta da Fatima da suma suke kukan tace
“Ni kam ba zan iya neman yafiyar ki ba twin sister, na san bazaki taɓa yafe mini ba, ina ma ina ma… Ina ma zan iya chanza Aunty daga mahaifiyata in dauki mammi ko Ammi, ina ma bawa na da damar ɗauke ranshi da kanshi… Aunty kin cuceni, kin cuci kannena, kin cuci mahaifina, kin yi min illar da Har Abada baze taɓa mantuwa a raina ba… Wallahi na tsaneki, na tsani ganin mummunar fuskarki, meyasa kika haife ni meyasa aaa”
Ta karashe tare da kurma ihu faɗuwa tayi, numfashinta na barazanar ɗaukewa, Faraj ne yayi hanzarin ɗaukar ta, Farhan ya rufa mishi baya suka yi asibiti don zata iya mutuwa a yadda taken nan. Allah sarki shiyasa wani lokaci in zaka yi abu kake duba bayanka, me zaka barwa ƴaƴan ka?
Fatima ce ta rarrafo tana kuka har da majina ta riƙe kafafun Faizan..
“Wallahi wallahi abubuwa dayawa ban sani ba se yanzu, na rantse da Allah ban taɓa bin ta ko rakata wurin wani mushiriki ba, wallahi soyayyar da nake maka daga cikin zuciyata take don Allah karka barni, wallahi kana Rabuwa dani babu abunda ze hana ni mutuwa ka taimakeni karka bari na mutu Ya faizannn Don Allah..”
Yadda take kuka seda kowa yaji a ranshi kwarai ita kam ta so Faizan..