Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Idanu kawai fa’iza ta zuba mata kan ta girgiza kai tace
“Allah ya shirya”

A masifance Fauza tace
“Ameen in da gaske kike, kema na lura yayarki kan ta tafi ta tsammiki wannan munafurci nata in ba haka ba yaushe kika yi wani buɗewar idon gayamin magana yen yen yen da fuska kaman nawa anan”
Har Fa’iza ta bar parlorn tana jin masifar Fauxa.

Ita kuwa fa’iza na kulewa ta fiddo wayan dake ringing, Zubair ne nan ta gayamashi duk abunda aka yi mata a gida
“yanzu wani mataki kike shirin ɗauka?”

Tace
“ka bari tukuna in ga matakin su don na tabbatar ba shikenan ba, shurun baba prof wani abun ze kulla wadda babu wadda ze yi zato ko tunani, amma in na fara fita necon zan san yadda zan yi muke haduwa for now mu dinga wayan kawai”

Haka ta kasancewa Fauxa, kullum in ta tashi asuba bazata dawo sashen jadda ba se ta gama komai na sashensu ta kan yi mamakin Amminta wacce bata rabo da maganan Fauxa kin wulakantani kin zubar da ƙima ta a idanun kishiyoyi, hakan yasa har ta gama ayyukan idan ba gaisuwa ba daga babanta, mamanta har Aunty Amarya babu wadda take sake tankawa.

In ta gama na sashen ta koma sashen jadda tayi na nan da aka ware mata, kan ta karya, jadda zata sakata wucewa ta gaida duk matan gidan, bata fitowa daga sashen mammi kuwa se da nasiha me tsayawa a rai, hakan be hana ta waya da Zubair ba, sossai yake kara riritata yana hure mata kunne akan rayuwar gidansu ba rayuwa bace takura ce.

Ana haka take samun labarin ɓarin da Fatima tayi, dukda babu wadda yake magana akan zaman su don haka bata san yadda suke yin ta ba amma ta tabbatar kowa se da ya shiga damuwa kan wannan bari har Fa’iza aka tura dake an gama jarabawar makaranta Hutu ne kawai za’a bada abunda ba ɗabi’ar Baba prof ba, don baya yarda wata cikin en matanshi taje gidan wata zama da ko wanni nufi kuwa.

Ko a jikin Fauza kaman ma bata san me ake yi ba, bayan sati biyu da tafiyar fa’iza ta fara Neco, driver musamman aka ajiye mata shi ze kaita ya jira har ta fito ya dawo da ita, to ranan baba prof ya fita za shi unguwa da ya Faraj kenan ya hangi wata yarinya me irin uniform ɗin Fauzan a farkon layi saka Faraj parking yayi ya kira mishi ita.

Ko da ta zo ya tambayi sunanta se ya gane mahaifinta mutum ne da baya ƙaunar shi don ko sallah baya zuwa masallacin shi ta bayan layi yake zuwa, murmushi kawai yayi ai ya riga ya san ba kowa ne ze so ka a duniya ba amma tunda akwai hakkin makotaka ze sauke.

“Zan sanya driver da ke kai Fauziyya ya dinga biyowa yana daukar ki se kuke tafiya tare kuna dawowa tare se ya fi miki sauƙin neman abin hawa a nan wadda suke wahala”

Har ƙasa ta duƙa ta mishi godiya Dukda kwarjini ne kawai da ya cika ta dashi in ba haka ba babu abunda babansu be faɗa musu akan Prof kaka ba.

Haka ko aka fara, abunda ya fara ba Fauxa haushi yadda yarinyar take shigowa har su je su yi paper su dawo bata gaisheta, dukda ita ba kalar wacce ta damu da damuwar wasu bane sede haushi ya kan cika ta da al’amarin yarinyar kina cin arzikin mutanen gida kina musu gadara.

Wata rana suna da papern rana tun da suka fito ma Fauxa ke wayanta da Zubair don yau din zasu haɗu a makarantar, musamman ya kawo wadda ze zauna yayi mata papern ranar a madadin ta ita kuma su fita tare.

Ko da ta isa bata nufi hall ɗin ba ta zagaye bayan classes anan Zubair ya ɗauke ta suka fita, ya nuna mata yayi kewanta ta amince mishi sau ɗaya dae kan ta gama paper ta koma kulle, lallaɓa shi tayi akan tunda suna son juna ya turo magabatanshi in ya so tana gamawa baban ya ɗaura mata aure su huta, yace ze yi tunani akai haka dae suka gama yawon su ya haɗo ta da chocolates masu yawa.

Ko da ta dawo kowa ya waste a school wanchan yarinyar se tsaki take ja, driver dae sanin halin Fauza yau ne kuma na biyu na farko sun hadu har dasu sakina yasa be ce komai ba.

Koda ta zo bata ce musu su yi haƙurin ajiye su da tayi ba kawai ta shiga ta zauna abunta tana bare diary milk, har sun kusa unguwarsu yarinyar da ko sunanta bata sani ba tace
“Fauziyya sunanki ko? Nace ya kamata kike sanin darajar mutane, don ana cin arzikin gidanku ba shi ze sa ki samu damar wulakanta mutane ba, sannan wallahi kika yi tsiya se in yi tattaki har gaban tsohon ki in sheda mishi abunda kike yi in kin fita, ko de!”

Ta taɓe baki tace
“na ji labarin da saninsu ma tunda arzikin na safarar yara ne ko me nasu tayi sakamako n…..”

Wani kalar buge mata baki da hanci da fauxa tayi da gwuiwar hannu se da yasa hancin ta da bakinta fara zubar da jini.

“Da alama baki san Fauxa bane! Ina me tabbatar miki wannan gargadi ne ɗon wannan ne karo na farko ko da bakin wasa wannan kazamtacciyar bakin naki ya sake ambatar iyayena ko da Kalmar alheri ne se na gurje shi bare ta tsiya”
Tana gama faɗa ta saka hijab yarinyar da already ya ɓaci da jini se yarfa hannu take tana kuka ta share bayan hannunta, don kowa ya san Fauxa er gayu da kwalliya ce, kayan ta bata yarda wani stain ya bata su.

Driver ne yace
“ashhha! Hajiya Fauxa ayi haƙuri ai duniya ɗan hakuri ne”

Bata ce mishi komai ba sbd be saba shigar mata idanu ba wannan ne na farko kuma ta ɗaga mai kafa, yana tsayuwa yarinyar ta sauka da gudu tana kuka ta shige gidansu.

Tsaki me karfi fauza ta ja tana rasa me ke damun baba prof da manna waenda basa kaunarka jiki.

Ta samu fa’iza ta dawo da sha tara na arziki don sayayya me dumbin yawa Faizan yayi mata matsayin kanwarshi, kowa seda ya samu tsarabar shi kasancewar shi mutum me kyauta sossai.

Washegari ko da suka tsayawa yarinyar bata fito ba Fauza tace su wuce, a makaranta ta samu yarinyar da wasu mates ɗinta don ita bata san makarantar ba tunda jarrabawa ne kawai ya kawo ta sbd gudun haduwa da su sakina yasa baba yayi mata registeration a wani makarantar.

Yadda suke ta hura hanci ga yarinyar fuska a kumbura yasa Fauxa kwashewa da dariya, irin kallon da suke mata na zaki daku yau tayi musu kan tayi wucewarta, bayan sun gama paper an waste tana tahowa don zuwa wurin mota en matan huɗu suka yi mata ƙawanya.

“Ke! Me kike takama dashi da zaki illatar da sukaina kuma kiyi Tunanin kin ci bulus?”

Sha ka hura dake bakinta ta ciro ta ɗan lasa tana Kallonsu dariya suke bata.

Ɗayan tace
“don an zagi prof kaka menene? Waye be san yadda kudinshin nan dake ta hauhawa ba na Allah da annabi bane? Ko karya aka yi don an ce yana safarar mata?”

Dayar tace
“ai ba mata da yara kaɗai ba har abubuwan shaye shaye don duk abunda kaji ana jita jita a kai da ƙamshin gaskiya”

Na farkon tace
“karki kai da nisa gashi har yaran yake baiwa suke sha, waye be san wannan ƴar fitsitsiyar babu abunda bata sha ba?”

Jakarta Fauxa ta sauke ta buɗe ta ciro paper ta fara naɗe sha ka hurarta na big bom, tana nadewa ta fara magana.

“Kaman yadda na miki alkawari bakinki ya sake aibata iyayena se na gurje shi to yau se na gurje shi da ƙasa idan gasa miki shi ne ba’a yi da kyau ba yayin wankan haihuwa yau za’a miki gashi me kyau…”

Tana kallon sauran tace
“ku kuma en korenta kowaccenku sakamakonta na rubuce a goshinta, ke yatsar da kika nuna ni dashi yau se an yi miki gyara, ke kuma haƙorin ki ɗaya se kin rasa shi, ke kuma zaki komawa uwaki da karyayyen hanci kin san Karyewan cartilage? To yau zaki sani”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected