Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

“Husna bari! Bar lilawa hakanan jiri ze yarda ni”
Ta faɗa tana runtse da idanu, husna kam ina ruwanta ta maida kafafunta baya ta cilla da karfi daidai ta buɗe idanunta ita kuma ta hantsila tana shirin faɗuwa yayi azamar tare ta duk idanu suka zubawa juna..

Da sauri kuma ta miƙe tsaye tana gyara ɗan kwalinta da ya zame ya bayyana baƙi sidik ɗin gashinta da ta tsefe kitson bukin ta ta tufke saboda ihun da husna tayi na
“Uncle zo ka hau lilo tunda Aunty na tsoro..”

Ta faɗa tana wangale mishi wawulonta, murmushi yayi yace
“zan zo babyn uncle amma yanzu cigaba da abun ki ke kam”

Ya karashe yana zama akan chairs ɗin wurin tare da crossing kafanshi, duburcewan da tayi yake kallo ƙasa ƙasa duk in yana wuri sakewarta ba sossai ba don tun sati biyu da in har yana gari ya kan shiga sau biyu ya duba su ya lura da hakan musamman idan husna ta rike shi da surutu ya ɗan jima se ta rasa natsuwa.

Juyawa kawai tayi tana cewa husna
“in kin gama se ki dawo ɗaki”

Har ta juya ta ji sassanyar muryarshi me cike da natsuwa ya ce
“Ji mana..!”

Baki ta tura tace a ranta se kace wata budurwa da ake shirin tarewa a titi.

Juyowa tayi bayan ta gyara bakin da ta turon tace
“Na’am”

Yace yana kallonta kai tsaye wadda har tsikar jikinta take jin kallon
“Ni dodo ne da in na zo wuri kike guduwa?”

Bakin ta sake turowa tana cewa a ranta
“ai ka fi dodon ma razanarwa, in ka so kayi kirki in ka so ka tabka tsiya ko a gyalenka”

A fili kuma tace
“A’a kawai ina da abunda zan yi ne a cikin”

Yace
“ok, before then zan samu shayi?”

Kai ta gyaɗa mishi kan ta juya ta fice, cookies ɗin ya ɗau ɗaya ya sa a baki yana mamakin yadda ta iya abubuwa haka masu daaɗi.

Cikin mintuna da basu fi ashirin ba ta dawo da tray me ɗauke da karamin glass tea flask da cups ɗinshi a jere a gefe, a gabanshi ta ajiye tana kallon yadda yayi nisa a cin cookies ɗin nata.

A ranta tace
“ko tayi ba’a yiwa mutum ba ya zage ya cinye mana abunmu”

Kaman kuwa ya san me take cewa yace
“daina min kallon ba’a gayyaceni ba na ci, ladan kati na da kika ƙarar ranan ne”

Wara idanu tayi a kanshi yana tsiyaya tea ɗin a cup bayan ya gama ya ɗago yace
“yes”

Ta langwabe kai tace
“to Ayya in sake maka cookies ɗin ka bani in sake waya dasu? Bana jin daaɗi yadda na kwana biyu ban ji su ba”

Yace
“no bana son wannan, wani abu daban nake so”

Ta Yi saurin cewa
“menene?”

“Zaki dinga dafa min wannan tea ɗin kullum”

Da saurinta tace
“eh na yarda”

Murmushi ya saki wadda ya sakata kusan shagala da Kallonshi yace
“wayan na sama in mun haura zan baki”

Tsallen murna tayi tana cewa ta gode, kallon da yake mata yasa ta natsu ta juya ta wuce cikin don bazata iya zama a inuwa ɗaya dashi ba Sam bata iya sakewa.

Kaman yadda yayi alkawari bayan sun hauro da Husna ya bata ta kai mata, taji daaɗi sossai amma ta ji haushi da ta duba taga ya goge hotunan da tayi a wayan kuma da gayya ne tunda ga na matarshi da nashi na ciki nata ne ya goge, a daren suka sha hira da jadda har da su fa’iza da faaazila sun gaisa sbd tayi kewarsu.

Mammi ma sun jima suna waya kan ta ba husna ma ta ishe ta da surutu, bayan sun gama ta bata wayan ta maida mishi.

Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka’ida se tayi mishi tea ɗin nan, yawanci tana samun shi ko a dining ko a parlor ta ajiye mai, sadda Fatima tayi noticing kusan hauka ta saka mishi ai ba bata iya bane be ce yana so bane, shi kuwa namijin duniya kai tsaye ya ce mata na hannun Fauza yake so ba nata ba shiyasa be tambayeta ba, tayi kukan maganan nan, kudirinta da haushinta kan Fauziyya kuma ya ƙaru, dukda Auntyn ta tayi fushi me girma da ita sbd abunda tayi kwanaki tace ya so lalata musu aiki don in ta bari Faizan ya fara tausayawa Fauza so ze iya shiga idan kuma so ya shiga tabbas ze saka alamar tambaya akan son da yake yi mata ita.

Ta dawo daga lectures tana haurowa suka kusa cin karo da fauza dake shirin sauƙa da kayan tea ɗinshi da yanzu kenan ya gama sha take shirin sauka dashi, tare ta Fatima tayi.

Matsawa tayi zata bi ta gefe ta sake tare gefen, tana kallonta tace
“Fauza me kike nufi da mijina?”

Har kaman bazata amsa ba se kuma tace
“me kuwa nake nufi? Last time da na bincika duniya sun sheda Cewar matan Faizan biyu ne, ko kunnuwanki sun toshe ne a sadda amsa kuwwa ke bayyana cewa an shafa Fatiha fauza ta zama ta Faizan?”

Wani irin takaici ne ya zowa Fatima wuya
“ke har kin kai macen da zaki yi ikirari namiji kamille irin Faizan ze so ki? Sauran wasu ce fa da sauran shaye sha….”

“Shhhhhhhhh”
Fauza ta faɗi tana sa mata hannu a lips ɗinta tace
“wannan kuma tsakaninmu ne kin gane ko? So kiyi ta kanki gwara ni ban bi hanyoyi masu yawa da haramci wurin mallakarshi ba, ban kuma zauna na ɓata hawayena wurin kukan in ban same shi ba zan mut…..”

Ɗaga hannu Fatima tayi zata mareta tayi saurin tarewa wadda ya saka tray ɗin hannunta faɗuwa ya fashe tartsatsa, hannun Fatima ta cillar wadda ya sakata loosing balance ta tafi suuuu tana kwala ƙara.

Razanar da tayi yasa Dukda bata faɗi kan cikinta ba cikin ya ƙulle har jini ya balle mata, Da sauri ya karaso yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun, Fauza ta buɗe baki zata mishi magana ya ɗauke ta da wani irin mari wadda ya sakata yin baya kafanta na dama ya sauƙa a kan glass da ya fashe a wurin, runtse idanuta tayi da karfi tana jin zafafan maganganun da yake jefanta dasu.

Bata buɗe ba har ya sauka ya kama Fatima dake kuka haikan sbd baƙin ciki don ta san wannan ciki kam se wani ikon Allah suka fice daga gidan da hanzari.

Ilai kuwa Fatima ta rasa cikin tayi kuka har kaman ba gobe, likitan ya tabbatar musu da cewa mahaifanta is weak already shiyasa abu kaɗan ya iya ɓarar da cikin, haka ta saka shi a gaba tayi ta kuka wadda ya saka tausayinta kama zuciyarshi, Baba prof ya kira ya sanar mai da ɓarin.

Ko da ya tambaya ta yaya hakan ya faru cewa yayi haka Allah ya tsara wadda kai tsaye Fatima ta dakatar da kukan tana kallon shi tace
“Haka Allah ya tsara fa kace yaya? Ko kuma Fauza ce ta zubar min da shi?”

Be so baba prof ya ji ba sede a yadda tayi maganan dole ya ji, tambayar shi yayi ya hakan ya faru? Taya Fauza zata zubar mata da ciki? A gaban jadda da Baba Alhj yake amsa wayan wadda duk hankalinsu ya koma kanshi jin wani sabon zance.

Yace
“Baba ban san me ya hada su ba na fito daidai lokacin da Fauziyyar ta hankaɗa hannunta wadda ya saka kafafunta gaucewa kasancewar tsaye take a kan stairs hakan ya saka ta faɗi amma bata faɗi kan cikin ba tsoratar da tayi ne ya saka cikin ɓarewa”

Kuka me karfi ta saka tana cewa yana shirin baiwa Fauza kariya bayan ya gani kiri kiri ita ta turo ta ta faɗi, yadda take ta maganganu har take nema ta wuce layi yasa baba prof yace ya bata wayan amma shima bata wani saurare shi ba sbd kuka da take tayi.

Allura kawai Faizan ya sa aka mata a take bacci ya ɗauke ta, Baba prof ya tambayi ina Fauza?

Se a lokacin Marin da yayi mata ya dawo mai, lumshe idanunshi yayi yana ɗan sauke numfashi yace
“tana gida baba”

Baba yace
“To ka tabbatar baka yanke hukunci cikin fushi ba, ka zauna kaji both side da yadda komai ya faru, abunda ya faru ya riga ya faru fushi ko hatsaniya ba ze dawo dashi ba, in har ka gama sulhunta gidan ka se ka Haɗani da Fauziyya ɗin”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected