Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Fauxa ko ɗar bata ji ba ta wuce sashensu abunta, yau itace da wanke wanke da kuma gyaran ɗakin su, Seda ta fara shara da gyara ɗakin tana cewa
“Wallahi in an ga dama a wargaza kan a tafi ba ruwan Fauxa”
Falaq tace
“amma kin san dole a shirin su Fakiha su wargaza ɗakin nan kam ko?”
Cikin kunkuni tace
“suna da hannu ai, se su gyara! Ni de na san nayi”
Tana kai nan ta hau sharewa ta fitar da Sharan a memakon ta kwashe se ta watsa tsakar gida alhali Fatima ta riga ta wuce nan a shararta na tsakar gida, tana watsawa ta bi ta kan tsintsiyar Fatima da ta sake baki tana kallonta tayi wurin wanke wanke ta fara yi, dama kowa ya san wanke wankenta kwanuka kam se sun bugu iya buguwa in akwai na fashewa kuwa to se ya fashe.
Ammi da suke aikin kari da Fa’iza bata ce mata komai ba, don in tace zata yi magana kuka ze iya fin karfinta Fauziyya ta riga ta fi karfin duka yanzu kuma se Adu’a.
Da yamma bayan sun dawo makaranta Fatima na wankin uniform na su Fakiha yayinda fa’iza ke wanke wanke, ita kuwa uwar gayyar kitchen take tana taya Aunty Amarya sa magana tunda ba aikin take ba duk abunda Aunty Amarya ta saka ta se tayi mata shirme da gangan.
“Ni sumayya! Yanzu Fauziyya daka attarugu ma se kin zuzzubar a ƙasa haka? Ai ko Faazila dake karama a gidan nan karankap zata daka min kayan miya in kwashe lafiya lau ke kam babu abunda kika iya goɗe goɗe dake se sa mutane magana? Wani irin jaraba ne wannan?khaih Allah ya shirya mana in na shiryuwa ne”
Kunkuni wadda Aunty Amarya bata ji ta hau yi. “Yen yen yen yen… Se ki zo ki shirya ai tunda charbi nake ko jigida” kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faɗan da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai.
Aunty Amarya tace
“tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don baki dauke ni da daraja ba tunda ba ni na haife ki ba jeki karki sake sakamin hannu a aiki”
Mikewa kuwa tayi ta fito ko a jikinta, ta zo wucewa ta gaban Fatima suka Haɗa ido a saman labbanta tace “munafuka” tana ball da bucket ɗin wankin har ruwan ya kwararare.
“Fauziyya!”
Baba Alhj ya kirata cikin wani irin kaushin murya.
Se Fatima ta fara kuka mikewa tayi ta wuce ta gaban Fauziyya ta duƙa a gaban Baba Alhj tace cikin sanyin murya
“Baba Don Allah ina so kayi min izini ina so in koma wurin mahaifina haka…”
Cikin tausayinta yace
“Babu inda zaki koma Fatima, nima mahaifinki ne in akwai wacce tafi cancanta da ta bar min gida Fauziyya ce!”
A razane Fauziyya ta ɗago ta kalleshi, Ammi ma da ta fito se idanu ta zuba mishi yana kallon Fauziyya yace
“Eh kin ji abunda na faɗa! Na gaji bazaki kasheni tun kwana na be kare ba, ke kaɗai ranki guda kin zama sheɗaniy….”
“A’uzubillahi Sule!”
Jadda da ta shigo bikon ƴar gidanta sbd ta ƙi shiga wurinta tun jiyan nan ta faɗa tana karasowa ta kama Fauxiya da ta zama speechless tana kallon mahaifinta.
“Ƴarka na cikin ka kake kira sheɗaniya Sule? Wani irin baki ne wannan? Me tayi maka da zafi haka?”
Kanshi a ƙasa yace
“Mama na gaji da halayyar Fauziyya, dubi goshin uwarta Sumayya yadda tayi mata jiya, babu wadda ze faɗa magana Fauziyya bata bashi amsa ba, ta sakawa yarinyar nan karan zuƙa tana mata gadara da gidan uba! Ita ɗin ai ba daga Bishiya ta faɗo ba, gwara Fatima sau dubu don bata sa uban ta da uwarta zub da hawaye ba… Wallahi wallahi Mama Fauziyya ta gama sane min cikin yarana har raina na gaji da komai nata”
Ammi kuka ta fashe dashi tace
“ba kinji ba Fauziyya? Wallahi ki guji duniya, uban da ya haife ki ma yace ya gaji dake to wa ze iya zama dake? Da wannan halayyar naki Fauziyya gwara ki sa wuƙa ki mana yankan rago mu huta da zafin zuciya kullum a kanki”
“Ruqayya! Sulaiman!! Ya isheni haka, tunda mutuncina da ganin idanuna be sa kun kasa amayo da kalaman bakinku ba, ni kuwa ba zan tsaya in cigaba da saurara ba, karku manta yaranmu kaman kiwo suke a garemu Allah ya kan jarabceka ta hanyoyi daban daban maybe ita ɗin itace jarabawar taku, idan kuka yi hakuri a matsayinku na iyaye kuka kai zuciyarku nesa kuka cigaba da mata adu’a har zuwa sadda Zaku Rabu lafiya kila ku samu rabauta ta sanadiyar ta, yanzu da duk kuke aika mata da kalamai marasa daaɗi ta karasa lalacewa kuma haka Zaku ɓata lahirarku saboda se Allah ya tambayeku, abunda ya saura ku ce shine kawai ta fita ta bar muku gida tunda har ka fara attempting to zan tafi da ita sashena ku zuba ruwa a ƙasa ku sha”
Tana kai nan ta janyo hannun Fauza da take tsaye kaman icce suka fice.
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Tara*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA❤️**
Ƙurawa kanta idanu tayi a Door size mirror na ɗakin tana jin sukar kalaman iyayenta a kanta, lallai kam basu faɗi abunda ze gyara mata rayuwa ba se ma wadda ze ɓata saboda hango abubuwan da zata ke yi musamman wadda a da gudun ɓacin ran nasu yasa ta danne burinta take rayuwa yadda ta taso ta gani Dukda baya cikin tsarinta, kallon kanta take da kyau tare da lumshe idanu tana tuna maganar sakina.
“Ke yadda kike da kyaun nan da sura wallahi kika fara ɗaukar wanka kika zama ƴar gayu ba karamin rububi maza zasu yi a kanki ba, kin san kuwa irin baiwar da kike dashi na fusgan hankalin mata ma ba maza kaɗai ba? Babe ki waye pls ki dena kunshe kanki cikin hijab”
Ajiyar zuciya ta sauke tana tuna amsar rahama.
“Ke wallahi abunda Sakinah ta faɗi gaskiya ne baki ganin yadda duk muke rayuwa cikin wayewa da aji da izza? Don Allah hakan baya burgeki? Amma ku kullum gidanku hijab hijab Ina ka fito karatu ina zaka karatu, babu babban waya, babu samari babu hangout da su party, wallahi kuna cikin duhu”
Ba kalaman nasu bane ke tunzura ta sede illa irin tsarin rayuwar da take so ɗin kenan se ya haɗu da maganganun su yake tasiri a hankali a ranta sede yanzu kalaman iyayenta ya hauhawa su kaman tashin farashin man fetur, a yanzu take jin zata fara nunawa su baba prof ba irin rayuwar su take so ba, ko da zasu yanka ta su fige tane.
Rahama da sakina ƴan ajinsu ne waenda suka shigo third term na SS1 ɗinsu asali a Abti suke sede rashin jinsu, da yawace yawace yasa iyayen Rahama suka cire ta suka dawo da ita Elkenemy ganin makarantar musulunci ne kila ta shiryu sede ba tare da sun sani ba sakina ma ta uzzuruwa iyayenta suka sake dawowa suka jone a ajin su Fauxa, tunda suka ganta suke admiring kyaunta da kalar idanunta suka fara nuna mata yadda zata ja hankali tare da tada hankalin maza a tiktok sede bata mai da hankali ba, iya kaci taji wakoki da wayoyinsu tayi ta kallon mata masu class a Instagram waenda har ga Allah suke burge ta.