Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Kanta ƙasa hawayenta da ta kasa rikewa na ɗiga akan shinfidadden jan carpet da ya cike parlorn tass tace
“in shaa Allahu Baba, ai Fauziyya ƙanwata ce kaman yadda ba zan iya cutar da Fa’iza ba haka ba zan taɓa iya cutar da Fauziyya ba, Zaku sameni me hakuri akan hakan Allah ya bamu zaman lafiya”
Kowa a parlorn seda ya sa mata albarka, Fauziyya wani irin baƙin ciki ya zo mata wuya, a duniya in akwai abunda ta tsana ya biyo bayan munafurci wallahi ita bata taɓa yiwa Fatima kallon ba munafuka ba, komai nata na munafurci ne, sunanta da Baba prof ya kira ne ya katse mata bitar wasiƙar jaki.
Ta ɗago fuskanta da yayi mugun chanzawa ta kalleshi.
Yace
“Fauziyya ba wai Bama son ki bane muka nace da lallai se an ɗaura wannan aure, ina so ki san gata ne wadda ba kowa ke samun irin wannan ba, Fauziyya ke ce shaye shaye kece club club da hotels hotels babu wani zuri’a da zasu zauna dake ba tare da sun wulakanta ki ba…”
Katse shi tayi saboda yadda zuciyarta ke matukar ƙuna idan aka jefeta da waennan kalamai masu daci wadda ta san ba laifin kowa bane illa nata.
Hawaye na gangaro mata ta miƙe tsaye tace
“Duk nan kuna zargi na ne da zina da kuma kuma shaye shaye, lallai idan har kuna zargina ku dangi na waenda na ɗauka bani da ya su a duniya to babu wadda ze yarda dani kuma!”
Katseta babanta yayi yace
“Me yasa baki da kunya ne ni kam a rayuwarki Fauziyya? Kin zauna kin rufewa mutane baki ko se na zo nan nayi fata fata dake?”
Baba prof ne ya dakatar dashi ya san she’s too young for all this duk tauna tsakuwar da suke don kawai aya taji tsoro ne.
Yace
“kina nufin ki ce duk wasu videos da hotuna naki da aka turo mana ƙarya ne? Ko kuma ganinki sau biyu da Faizan yayi a mabanbanta hotels da mutanen banza cikin shigan banza da buguwa suma ƙarya ne? Ko ganinki da idanuna da nayi shima karya na miki? Ko kuma biyo cikin layin nan da kika yi a buge shima karya ne?”
Girgiza kai tayi in confused tace
“bani da masaniya akan wasu pictures da videos, shi kuma da ya ganni duk a wuraren na yarda ni ya gani amma na rantse da wanda raina yake hannunsa ban taɓa aikata zina ba, tun da nayi wayo na san menene zina kuma na kyamaceshi wallahi ban san duk yadda abubuwan suka zama haka ba…”
“FAUZIYYA!”
Yayanta Farhan ya kirata yace cikin jin zafinta
“Ki dena rantsuwa akan ƙarya zaki cutar da kanki da kanki!”
Shesheka ta ja me karfi tana ciccilla idanunta cikin parlorn, chan cikin sif ɗin baba prof ta hangi Alqur’ani izu sittin da gudu taje ta ɗauka tare da ɗaurawa akai
a razane duk suka miƙe suna kallonta har Faizan da duk jijiyoyin jikinshi suka miƙe saboda wani irin tafasa da zuciyarshi ke yi, ji yake kaman in ya kamata da musu da rantsuwar nan ze iya kashe ta.
“Na rantse da wanda ya saukar da wannan littafi ban taɓa aikata zina ba kuma ban taɓa ɗaga abun maye da hannuna cikin hayyacina na sha ba, ban san meke faruwa dani ba amma wallahi ko a mafarki ban taɓa aikata zina….”
Kwace Alqur’anin da aka yi a hannunta ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, yana shirin sauke mata zazzafar mari mahaifiyarshi tayi Charab ta riƙe hannunshi a kausashe tace
“A kul Faizan! ban yarda ba ban amince ba, ko a bayan idanunmu ka daga hannu da sunan dukan Fauziyya ban yafe maka ba duniya da lahira!”
A razane yake kallon mahaifiyar tashi kan yayi wani magana mahaifinta ya bata mari daya, Farhan ya ƙara mata har Seda bakinta ya fashe.
Da sauri Amminta ta miƙe ta nufi kofa tana kuka, Baba prof ne ya dakatar da ita
“Ruƙayya!”
Tsayawa tayi tana jin yadda kukan ɗiyarta ke ratsa parlorn.
“Dawo ki zauna”
Mikewa ya yi da kanshi ya nufi Fauziyya ya riƙe hannunta suka dawo dab dashi a ƙasa ta zauna kanta ƙasa tana cigaba da kuka.
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya kan ya sauke ajiyar zuciya yace
“Farhan ban yarda ba ko da bakin wasa ka sake ɗaga hannunka akan Fauziyya, bana so ka sake mata kallo a matsayin ƙanwarka ita ɗin matar yayanka ce a halin yanzu”
Hannunshi na kan ta yana shafawa ya ɗaga ya kalli Faizan da da kallo guda zaka san ranshi be taɓa sosuwa irin na ranar ba, ko ɗagowa baya yi yadda mamminshi ke fifita wannan yarinyar fiye da farin cikinshi hakan na matukar ƙona ranshi, idan ya kalli matarshi da halin da ta shiga duk saboda ita se yaji ina ma ze iya kawar da ita a duniya ko ze huta.
Ɗauke kai baba prof yayi shima kwarai ya san an shiga hakkin shi sede ya za’ayi shine babba dole shine Juji.
“Fauziyya ki sani yanzu bakin alƙalami ya riga ya bushe, duk wannan bashi da anfani sannan Qur’ani ya wuce wasa babban hatsari ne amfani dashi wurin rantsuwa se idan har babu yadda za’a yi ne…. Ki yi haƙuri ki rungumi sabuwar rayuwar ki”
Kai ta gyaɗa tace
“shi ke nan Baba”
Shafa kanta yayi yace
“Allah ya miki albarka”
Babanta yace
“Ni kam ba zan ce kiyi hakuri ba, in kin ga dama kar kiyi abunda nake so ki sani shine daga ranar da kika kashe aurenki karki neme hanyar gidan nan, kije chan wurin abokanan watsewarki ku cigaba na yafe ki har Abada, in har kina son Adu’a da farin cikina gareki shi ne ki zauna da Faizan ba tare da wani matasala ba, ko a labari na ji ranar da kika saɓawa umarninshi Fauziyya ban yafe ba, tun rayuwarki baki taɓa saka ni farin ciki ba kullum da fargabar abunda ze fito daga gareki nake kwana nake tashi, sau ɗaya dae zaki yi kokarin proving Cewar ke ɗin ɗiyata ce har ki min biyayya!”
Ammi ta ɗago tana Kallonshi
“me yasa ne Sulaiman? Me yasa kullum ka buɗi baki alkhairi baya fita in har dae akan Fauziyya ne? Duk wannan hali da ta shiga da wadda take ciki baka taɓa tausayinta ba! Ni kam wlh ban yarda a zalunce ta ta ja baki tayi shiru ba!”
Kallonta kawai jadda ke yi, wani lokacin hankalin Ruƙayya na bata mamaki ganin idanunta tana ga yadda Aisha da Prof ke ture yaronsu ba wai don basa sonshi ba se don ganin sun samawa Fauziyyan ƙima da daraja a idanun Faizan ɗin sun kuma hana shi cutar da ita saboda rashin ƙaunarta da baya yi tun tale tale, amma ji inda ta dosa ita, babu wadda ya fi dacewa yayi magana a nan na rashin adalci irin Fatima da mahaifiyarta amma they sat patiently suna sauraron baba prof ɗin.
“Ruƙayya….”
Ɗaga mishi hannu baba prof yayi, kan ya dubi Faizan
“Faizan ga amanata na baka, ka san girman amana ka kuma san hukuncin duk wadda ya ci amana, in ka cutar da ita ina rokon Allah ya saka mata, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya, an riga an yi mata jerenta so mutum biyu ne kawai zasu raka ta su dawo”
Mammi tace
“Toh ka ji, nima Amana na baka Fauziyya in ka ci ma kanka! Ka riga kayi karatu babu abunda baka sani ba, ina fata zaka wanzar da adalci a tsakaninsu su biyun”
Jadda da hawaye suka zubo mata da kewar fauzin nata tace
“Fauziyya kiyi haƙuri! Kiyi hakuri!! Ki ƙara haƙuri!!! Ina tabbatar miki zaki ci ribar wannan haƙuri.. Faizan ga ƙanwarka nima na damka maka amanarta, Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a dayyaba, Fatima kiyi hakuri kin ji? Haka Allah ya tsara”
Kuka sossai duk su biyun suke kowa da abunda yake saƙawa cikin zuciyarsa, Fauziyya ta ƙudiri aniyar zama ɗiya ta gari for the first time ko don saboda Mammi da Baba prof, ko don babanta yayi alfahari da ita sau ɗaya dae a rayuwarta, bata taɓa saka shi farin ciki ba kap rayuwarta se bakin ciki har hawan jini yake dashi sanadiyarta, zata yi hakuri har taga yadda Allah ze yi da ita a wannan gida da yafi kabari ko wuta a gareta….