Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Anan suka kwaɓa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaɗa sbd shi fa’iza ke so, suna cikin yi se Fa’iza tace
“ni bani manjan ma in yi mixing kaɗan yadda ze bada wani dandano me armashi”
Fauxa tace
“Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so”
Musu suka fara, fa’iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta ɓalle da gudu daidai kofar kitchen ɗin taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaɗaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.
A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya..
Ko kaɗan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma’abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baƙi sidiƙ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma’abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murɗaɗɗen hali da zama dashi se ka shirya.
Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen ɗin, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya ɗago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha’awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa’iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka.
Kokari yake yayi controlling ɓacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haƙuri ta kasa ce mai yasa ya ɗaga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi ɗin sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taɓa Haɗa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin ɓacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain ɗinshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta.
Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun.
Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa’iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.
“Sannu Fauxa! Sannu”
Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa
“Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?”
Cikin kuka Fauza tace
“mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!”
A hankali Mammi tace
“FAIZAN!” Don shi kaɗai Fauxa ke cewa Azzalumi.
Da sauri Mammi ta cewa Fauxa
“ɗauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi”
A hankali ta karasa gareta ta ɗaga ta tare da riƙe hannun har ya tashi gabaɗaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaɗi amma se ta saɓawa Faizan, ashe kaddarar ƙone wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka?
Akamun fa’iza ta kawo ta kwaɓa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaɗan ma su kammala ta ƙi tace ta koshi, cikin rashin jin daaɗi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa’iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari.
Haka kuwa aka yi da fa’iza ta kawo mata ma ƙin ci tayi, Allah ya isa kuwa ta ja mishi yayi cikin kwando, gashi Ammin ta bata nan ta tafi kauyensu jiya uncle ɗinta ya rasu, da magrib ma da kyar ta samu tayi alwala ta tako zata fito zuwa masallaci kenan ta tsaya Chak jin muryar dake tashi a speaker na masallacin, tsaki ta ja ta koma ɗaki nan tayi sallah har isha bata fita ba, a Cewar ta bazata bi sallar azzalumi ba don Allah ba karba ze yi ba. bayan tayi isha ne ta kunna speaker ɗinta iya daidai jin kunnen ta ta saka waƙa abunta anan mood ɗinta ya fara dawowa daidai.
Tana ji su fai’za na cin abinci bata fita ba, idanunta a lumshe take jin Fatima na fesawa fa’iza ita duk yadda take jin karatu bata taɓa jin me natsuwa da kwantar da hankali irin na Ya Faizan ba, fa’iza na dariya tace mata
“zaki ce haka ne ma tunda kina son shi”
Fatima ta ce
“ban gane ina son shi ba? Ko de muna son juna?”
Fa’iza tace
“ai ko makaho ya shafa ya san ke ce kike mahaukacin son ya Faizan shi ba take yake ba, ba ta yadda za’a yi yana son ki ne ke karan kanki kan ya miki magana ɗaya se kinyi hamsin, sannan ya tafi yayi wata da watanni ko a wayan Jaddah baze ce a baki ku gaisa ba idan ma yana jin kunyar Mammi kenan, ni wlh bana son miki kasancewa da ya Faizan ina so ki samu me son ki inda zaki ji….”
Tsawa ta daka mata
“dakata fa’iza! Don ina maganan soyayyata dake ba shi yake nufin ki gayamin duk wani banzan maganan da ze fito daga bakin ki ba idan ma ba kitsa miki aka yi ba don baki da wannan wayaun, to henceforth as from today kika kara min irin wannan maganan wlh se nayi mummunan saɓa miki ni ba sa’ar ki bace”
Fa’iza tace
“Ya Fati daga faɗar gaskiya?”
“Bana son gaskiyar ki riƙeta”
Daidai lokacin Fakiha ta shigo da gudu tana shelan ya Faizan ya ce a je a karɓi tsaraba yana sashen Jaddah.
Da sauri duk suka tashi suka fice daga tsakar gidan.
Taɓe baki Fauxa tayi, Fatima na neman magananta ta tabbatar harda shagube a zancen nata, amma ba ta ita take ba yanzu ta samu ta warke shine damuwanta kuma wlh akan Fatima zata rama abunda ya mata tunda shi azzalumin ya fi karfinta.