Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Hmmm wani irin moment ne suka yi spending wadda baze Mantu ba, gabaɗaya seda ta gigitashi da albarkatun jikinta wadda duk ba cikin hayyacinta take hakan ba, ba jikinsu kaɗai ba a lokacin ze iya rantsuwa cewa numfashi ma guda ɗaya suke yi ba biyu ba, Seda suka shafe mintuna sama da talatin suna rabawa juna temperature ɗinsu kan ya mirginata, hancinshi yake gogawa da nata yana jin yadda su biyun duka numfashi ta hanci yayi musu kaɗan suna Haɗawa da baki, a hankali ya fara brushing lip ɗinshi kan nata, yana kokarin haɗe lip ɗinsu tayi wani miƙa da ya tabbatar da zazzaɓin ya sauka, yaraf ta dawo kan pillow a take wani wahalallen bacci ya sure ta, zamewa yayi ya kwanta daga gefenta yana jin yadda zazzaɓin tan ke shirin dawowa jikinshi.

Bacci me nauyi ne ya kwasheta yayinda shi kuwa yace be san zance ba, janyo ta ya sake yi jikinshi ya rufa musu bargo sbd jikinshi wani irin rawa yake yi… Ya fi awa kwance cikin wannan yanayi Ganin in yana cigaba da barin ta haka a jikinshi komai ze iya faruwa ya sa ya miƙe dafe da marar shi ya fice a ɗakin.

Kitchen ya shiga ya matsa lemon tsami a lipton ya kwankwade tunda yau ba kwanan Fatima bane bare ya rage wani abun, tunda yake be taɓa jin irin wannan sha’awa ba se yau, ɗakinshi ya shige ya zube rub da ciki bisa gadon shi yana juye juye.

Ita kuwa bacci tayi sossai, chan wuraren karfe uku na dare taji kaman ana kiran sunanta, cikin gigin bacci ta buɗe idanunta se taga ɗakin gabaɗaya ya sauya mata ya koma wani irin Ƙango me cike da abubuwan razanarwa, a firgice ta miƙe sede bata iya ambaton komai ba kaman ɗaure mata baki aka yi ko numfashi da kyar take iya ja amma bakinta ya ƙi furta komai.

Wasu irin abubuwa taga suna motsi daga jikin ginin ɗakin, sanyi taji me yawa a jikinta waigawar da zata yi taga wani irin hallita da bata taɓa sanin akwai irin shi ba baƙi sidik, me munin gani da razanarwa, ƙara ta saki wadda taji muryar yayi amsa kuwwa iya ɗakin, da sauri ta sauƙa jikinta na rawa ta nemi riga ta saka ta suri hijab ɗin sallarta ta saka, jakan da ta dawo dashi jiya ta zara ta fice da sauri daga ɗakin.

Parlorn kasa taje chan lungun dining ta makale ta takure Kaman wacce ta rasa gata, jikinta wani irin karkarwa yake gabaɗaya bazata ce ta san me take yi ba, banda tsanar gidan da tsananin tsoronshi babu abunda take ji.

Tana nan har aka kira sallar asuba fuskanta har ya kumbura da kuka, kaman wuta ake rura mata a gidan haka take ji, tana ji ya sauko da nufin tafiya masallaci, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi yana fita itama ta fice daga gidan ko waiwaye babu….

**Ayi comment in takarkare in baku na dare**

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

28

Saboda rashin baccin da be samu ba jiya ya sa ko azkar da kyar ya iya yi ya mike ya dawo gidan, ɗakinshi yayi direct ya kwanta ba shi ya tashi ba se wuraren karfe goma sha ɗaya, wasai haka ya ji shi Adu’a yayi kan ya sauƙa ya wuce toilet ya watsa ruwa har a lokacin ze iya cewa yana jin tsadaddiyar jikinta cikin nashi, yana jin duk wani moment da suka yi spending a jiyan cikin ƙashi da ɓargonshi.

Haka ya gama wankan ya fito ya shirya cikin kananun kaya, fitowa yayi yana baza kamshinshi me natsuwa da kwantar da hankali, ɗakin Fatima ya fara dubawa bata nan da alama ta tafi school, ɗakin Fauza ya nufa haka kawai ya tsinci kanshi da sakin murmushi.

A hankali ya tura kofan saide turus ya tsaya ganin kaman an yi wasan kura a ɗakin, komai kaca kaca a wargaje abinda ba ɗabi’arta ba.

Sunanta ya fara kira yana shiga ciki ciki sede bata kan gadon, bayin tura ya shiga nan ma bata nan.
Saukowa yayi kasa ya je wurin Peter yake tambayar shi ya ga fitan Fauza ko tare suka fita da Fatima?

Yace a’a Fatima ita kaɗai ta fita kuma shi yana kofan tun asuba be ga fitan ta ba, hankalinshi ya fara tashi da sauri ya koma saman ya fara kwala kiran sunanta saide babu ita ba alamar ta.

Fitowa yayi ya shiga mota ya ja da matsiyacin gudu se makarantar su, Afnan yake ta nema ko ze gansu tare sede be ganta ba, wurin Faisal yaje yace ya kira mishi Afnan ko suna tare da fauza? Kiranta yayi tace tun jiya da suka rabu basu haɗu ba, yau basu da lecture ma da safen.

Tun Faizan na ɗauka wasa sede hankalinshi yayi matukar tashi ganin da gaske bata nan ɗin, Faisal ne ya tuka shi suka je police station suka yi reporting, polisawan sun tabbatar saide in da kafafunta ta fice da sakacin me gadi in ba haka ba da shiga aka yi aka ɗauke ta se an gane bare da yace har tsakiyar dare ma suna tare.

“Iyayen ku na nan garin ne?”
Dpo ɗin ya tambaya.

Faisal ne ya amsa da
“A’a suna Adamawa”

“to ko gida dae ta tafi?”
Dpo ya faɗa.

Faizan da ranshi ya soma ɓaci yace a tsawace
“Me aka mata ɗin da zata tafi gida ba tare da sanina ba? Ni fa mijinta ne!!!”

Ya faɗa cikin hargowa, Kafadanshi Faisal ya dafa yace
“Calm down please Faizan ka natsu, ban san ka da hayaniya haka ba..”

Yace
“Kar in yi hayaniya Faisal? Matata fa na nema na rasa na kawo musu report kuma me makon su yi aikinsu sun tsaya suna faɗan wasu abubuwan da baze yiwu ba, ana tafiya gida haka kawai ne a aure?”

Dpo ɗin yace
“I’m so sorry, ka natsu please ka san komai na iya faruwa ne shiyasa muke maka waennan tambayoyi kila ka mata wani abin ɓacin rai da ze sa ta bar gidan ta tafi gida ba tare da saninka ba, amma tunda kace ba hakan bane yanzu zamu fita mu fara bincike ka kwantar da hankalinka komai ze tafi daidai”

Fitowa suka yi sbd azahar da ake ta kira suka tsaya suka yi sallah, Faisal ya dube shi yadda gabaɗaya kamananninshi ya sauya jijiyoyinshi suka tashi suka yi raɗa raɗa yace
“Faizan ko zamu kira su baba?”

Kai ya girgiza yace
“Ko gidan ta tafi in dae a mota ne zuwa yanzu be ci a ce ta isa ba… Amma me na mata da zata tafi gida?”
Ya faɗa cikin sanyin murya.

Dafa kafadanshi Faisal yayi ya bubbuga alamun rarrashi kan suka miƙe suka fito se ga Jafar shima suka haɗu suka fara yawon nemanta da polisawa, a Airport babu jirgin yola da ya tashi a ranar ma gabaɗaya ya gayamusu amma basu yarda ba seda suka je suka gama binciken su kan suka nufi tasha…

***

Ita kuwa Fauza bazata ce ga takamammen Tunanin da take yi ba, Sam kaman makuwa tayi ne ko yaya haka dae ta miƙi hanya ta tafi sossai Dukda wani irin sanyi da ake zabgawa na asuba, bakin wani masallaci ta zauna ana sallar asuba limamin na karatu cikin Suratul baqara ayoyin ƙarshe, a hankali take jin natsuwa na zuwa mata, itama ta karɓa taci gaba da binshi har ya kai karshe yayi ruku’u.

Da sauri ta miƙe ta shiga ciki ta samu ruwa tayi alwala kan ta gabatar da sallar itama nan fa ta ji bakinta ya iya fara ambaton Allah amma zuciyarta har lokacin baƙi kirin babu abunda ta tsana irin Abuja da gidan Faizan.

Fita tayi daga masallacin ta tafi ta tari taxi yana tsayuwa tace
“Park zaka kaini”
Yace ta shiga, tashar Jabi ya kaita.

Ta biya shi sbd akwai kuɗi a jakan, taje ta shiga mota nan da nan motar yola ya cika suka ɗauki hanya, Seda ta tabbatar sun bar yankin Abuja kan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected