Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Idanunshi na kanta yana kiyasta abubuwa masu yawa a ranshi yace
“thank you”

Ta miƙe tana ɗan murmushi bata zauna a parlorn ba se ta nufi ɗaki.

“Fauza!”
Ya kirata yadda kowa ke kiranta, da sauri ta juyo yace
“kin sha magani?”

Kai ta gyaɗa mai yace
“to dawo ki zauna”
Dawowa tayi ba musu ta zauna a parlorn.

Bayan ya gama cin abincin da kanshi ya tattare kwananukan amma kitchen ɗin sama ya ajiye, a tare suka yi spending time me yawa Dukda babu me magana cikinsu banda husna da ta ishe Fauza da surutu sede ta amsa da eh ko a’a, azahar da aka kira ya saka su duk mikewa.

Ya fita be dawo gidan ba se yamma lis.
Yanzu ma abincin ta kawo mai tuwon semo ne da miyan busashiyar kubewa sbd shi tayi tuwon don ta san yana so, ita kam indomie ta dafa ta ci, husna ma tuwon ta ci, se bayan magrib ya zauna cin tuwon gefen shi papers ne, bayan ya gama ya wanke hannu ya dube ta kan yace

“Dukda ban so ki fara karatu nan kusa ba saide Baba prof ya ƙi aminta da kudiri na hakan ya sa dole na shiga nemar miki admission kuma Alhamdulillah yau gashi kin samu, ina so ki san rayuwarki na da da na yanzu ba ɗaya ba, idan da kin yi abubuwa masu yawa ganin u r free yanzu kina da aure, matsayin aure kuma ya wuce duk wani matsayi da kike tunani, duk laifin da zaki aikata yanzu ki sani ba iya ke da zuri’arki ba har mijinki da ƴaƴanki wannan image ɗin baze mantu a idanunsu ba, sannan zunubinki se ya fi na da sbd kin wulakanta sunnah, in Allah ya kaimu gobe zaki je ki ƙarasa sauran abubuwan da ban karasa ba ki fara shiga aji”

Karɓan admission da ya miko mata tayi tace
“na gode Allah ya saka da alkhairi in shaa Allahu zan kiyaye”

Wayanshi ne ya ɗauki ringing ganin baba prof yasa ya ɗaga tare da sallama bayan sun gaisa baban yace
“Faizan me ya faru? Meyasa zaka bar matarka tayi yaji kuma ta kamo hanya daga Abuja zuwa yola a mota bayan ka san ba lafiya ne da ita ba?”

Yace
“Yola ta tafi kenan? Hmm baba maganan nan ba na waya bane ta zauna a gidan in Allah ya sa Fauziyya ta warke zan zo”

Baba yace
“Assha Fauziyyan ma ba lafiya?”

Yace
“Eh amma da sauƙi”

Baban yace ya bata, miƙa mata yayi a ladabce ta gaishe shi ya tambayi jiki take ce mishi ai ta warke ma bayan sun gama ya ba jadda da suke tare itama ta mata sannu tana tambayar me ke damunta, tace kwalba ta taka amma da sauƙi.

Miƙa mishi wayan tayi tana Kallonshi, kallon lafiya kike kallo na yayi mata se tayi saurin kau da kai ta miƙe.
“Gulma”
Ya faɗa yana maida kanshi ga TV

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

23

“Aunty fa wai kinga kuwa yadda ya ɗauke tan ne? Be fa hukunta ta na abunda ta aikata ba, wallahi zuciyata zata bu….”
Zazzafar mari Auntyn ta sauke mata tace

“zuciyar ta buga Fatima, nace ta buga ɗin..”
Dawowa tayi ta zauna ganganta tace
“Fatima kin san irin asarar da kike shirin ja min? Kin fa san shekaru sama da goma sha wani abu nayi ina wannan tanadi meyasa se lokaci ɗaya zaki nemi watsar min da buri? Ni da nake zaune lafiya da kowa a gidan nan alhali zuciyata dankare take da haushi da tsanarsu duka ni me ya sameni? Toh wallahi ba zan ɗauka ba, bazaki zama wawuya shashasha, lusara a gidan Faizan har ki barwa Fauza shi ba…”

Cikin kuka Fatima tace
“Aunty fa kin san makircin Fauza, da gangan yarinyar nan ta sauya gabaɗaya ni bata min rashin kunya bare shi ballantana in ce zasu samu sabani har ya sauya mata kamanni don baya daukar rashin kunya..”

Dakuwa Aunty tayi mata tace
“baya ɗauka kin sani kuma kika mishi? Fatima wallahi wallahi zan iya sauya ki idan baki yi hankali ba bazan taɓa zama ki wargaje min mafarki na ba, sarai kin san tun kan na shigo gidan nan nake da buri a cikinshi, target na ba Sulaiman bane amma saboda in yi anfani dake yasa na auri Sulaiman yanzu bayan kin girma kuma ki kasa yi min komai ba, kin san wahalan da muka sha kan Faizan ya aureki”

Fatima tana kuka tace
“Amma Aunty ai laifin ki ne, kin sanya min soyayyar faizan tun ban san target ɗinki ba, kuma mun yi yarjejeniya a aikinki ba za ki taɓa cutar da shi ba, wlh rasa shi daidai yake da na rasa rayuwata, bala’in son da ban san adadinshi ba nake mishi shiyasa kusancinsu da fauza ke kasheni… Aunty ke kika ce aure kawai za’a ɗaura ba ze shiga lamarin ta ba sbd tsanar da yake mata amma gashi nan reshe na shirin Juyawa da mujiya… Ko ki san yadda zaki yi dani ko kuma wallahi kowa ya rasa nashi Burin…”

Wara idanu Auntyn tayi tana kallon Fatima tace
“Fatima? Are u threatening me?”

Mikewa tayi tana share fuskan ta tace
“ba threatening ɗinki nake yi ba, ina gayamiki ne ki ɗaukar min mataki akan Fauza in ba haka ba daga ni har ke dab muke da rasa burikanmu”
Tana kai nan ta fice daga ɗakin.

***

Kaman yadda ya faɗa washegari bayan ta gama Haɗa musu abin kari ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga marar nauyi ta saka tare da sanya hijab coffee color wadda yaje mata har ƙasa, ta shirya husna ma cikin doguwar riga da baby hijab, daidai sun fito shima ya fito murmushi ya sakarwa husna wadda ya saka Fauza daskarewa a wurin tana ganin cikakken haiba da kyaun bawan Allahn nan, daga baba prof har mammi ba wadda ya bari duk seda ya bi ya zaftare musu kyau da kwarjininsu.

“Madam chogal”
Ta faɗa yana kallonta da neman tsokana, ai kuwa baki ta turo tana cewa
“Allah yaya ni ba chogal bace gashi ina tafiya da kyau”
Ta fara tafiya tana nuna mai dariya yayi yace
“ni dae idanuna chogal suka gani”

Dining suka nufa tana ta tura baki, idanunshi kafe kan lips ɗin da take ta turowan ta saka pink lipstick da yayi mata kyau sossai.

Bayan ta gama sa abincin ta tura mishi ta zubawa husna ta kuma zuba nata Dukda yadda take a takure a kuma sarge sbd yadda yake aika mata kallon ƙasa ƙasa haka ba yadda ta iya ta zauna a wurin ta fara ci, Seda suka gama suka yi hamdala kan ya saka hannu ya zari tissue ya miƙe.

Taku biyu ya iso dab da ita har suna shaƙar numfashin juna, ƙashim jikinsu na gaurayuwa, duƙowa yayi yana rarraba idanunshi tsakanin kirjinta dake bugu da sauri har yana iya kallo da kuma idanunta da suke kashe shi, da kyar ya samu ya tsayar akan lips ɗinta da yanzu suka zama abu na biyu da baya iya gajiya da kallo a jikinta, saukar hannunshi taji da tissue ɗin ya ɗan kwashe lipstick ɗin cikin wani salo da ya saka su jin yarrrrrr gabaɗayansu.

“Haka is ok”
Ya faɗa chan ƙasan maƙoshi kan ya miƙe tsaye ya juya tare da cusa hannayenshi cikin aljihu ya fara takawa don fita daga wurin.

Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta, ‘oh ni fauza me ke faruwa ne kam?’
Ta tambayi kanta sede ba amsa.

Mikewa suka yi duk suka bi bayanshi, husna ta tura gaban motan ita ta shiga baya, har suka isa da shi da husna suke hiran su ita bata saka musu baki ba.

Microbiology ne course da aka bata yayinda Fatima take yin biochem kusan dept ɗinsu wuri daya ne, sauka suka yi suka nufi ciki inda office ɗin Faisal yake nan biology dept, kan su isa ta Haɗa idanu da en mata sama da biyar waenda idanunsu kan Faizan kaman zasu cinye shi danye, ɗan Kallonshi tayi taga abunda suke kallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected