Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Hawaye ta share tace
“zaka ce haka ai tunda ta baka ka kwasa”
Ya rasa me ke damun Tunanin Fatima, mikewa yayi ya fice tunda ta ƙi fahimta tana kan rashin daidai.

Tsaye ya samu Fauza tsakiyar parlor tana ganinshi ta nufo shi yayi saurin saka hannu ya riƙe nata ganin kai tsaye jikinshi take shirin shigewa wadda illar da take mishi a yadda ya san kanshi idan be yi da gaske ba baze yi bacci ba yace
“menene?”

Tace
“Motsi nake ji a ɗakina”
Yace
“Ina kin yi azkar kuma kin karanta Alqur’ani?”
Kai ta gyaɗa yace
“to ki yi yaƙini da hakan ki saka a ranki babu wani abu da ze iya cutar dake kinji?”

Kai ta gyaɗa ya Janyeta suka yi ɗakin nata inda yace ta kwanta, zama yayi ta kwanta a kan pillow yana shafa kanta idanunta a lumshe yayinda shi kuma nashi ke kan fuskan nata yana kare mata kallo har bacci ya ɗauke ta.

Fita yayi ya tabbatar da komai daidai a gidan kan ya dawo ya rage musu wuta ya cire jallabiyar tare da kwanciya da dogon wando kawai be damu da saka kayan bacci ba, har ya lumshe idanu ya tuna magungunan ta bata shafa ba.

Sauka yayi ya ɗauko ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu na mintuna kan a hankali ya fara sakawa a hannunshi ya shafa mata a kafafu, ya sake sakawa ya shafe hannayenta dashi, daga nan se gashin kanta ya shafa mata. Sauran na hannun nashi ne yake shafa mata a fuska a hankali wadda ya saka ta ɗan buɗe idanunta dake cike da bacci tana Kallonshi.

‘Tsarki ya tabbata ga Allah da ya halicci wannan idanu’ baze taɓa cewa ya taɓa ganin abunda har ranshi yake mishi kyau irin idanunta ba, a hankali yake shafa kumatunta idanunsu sarke da na juna se chan ta turo baki tace

“bacci” cikin muryar da bacci ya ci karfi.

“Yi baccinki an gama”
Ya faɗa a natse kan ya miƙe ya adana magungunan ya dawo ya kwanta daga gefenta yana lumshe idanu, baya son kawo Tunanin komai a ranshi in yace ze yi tunanin wadda ya aika mata da wannan ƙadangare tabbas ze fara zato kuma ya san zunubi ne, in yace ze yi Tunaninta kuma tabbas ze iya Jawa kanshi damuwa wadda baya fata ya kasance yanzu don baze iya ɗaukar abu guda biyu ba idan abunda yake gudu ya kasance.

Haka dae yayi bacci da blank thought, asubar fari ita ta fara buɗe idanu se ta ganta kwance dab dashi kansu a kan pillow ɗaya yayinda hannunta ke kwance bisa faffaɗar kirjinshi, a hankali ta kai idanunta fuskanshi da dim haske ya bayyana haske da kwarjininshi, dukda bacci yake yi but ba karamin kyau yayi ba sajenshi dake kwance lublub gwanin sha’awa.

A hankali ta ɗago hannunta ta ɗan shafa sajen nashi tana mamakin yadda aka yi tun da chan bata taɓa ganin kyaun nashi ba se yanzu, karab taji ya riƙe hannun da take shafa mai fuskan, a hankali ya waigo yana kallon ta, kunya ne ya rufeta se tace
“Ina kwana?”

Daga haka ta zame ta sauƙa tayi toilet, murmushi ya saki kan shima ya sauƙa, zuwa yayi ya kunna Alqur’ani don da asuba sunna TV karatun Alƙur’ani mai girma suke sakawa, daga haka ya ɗauki jallabiyarshi ya fice dakinshi a chan yayi alwala ya zo ya fice masallaci.

Ko da ta idar da sallah azkar tayi tare da karatun Alƙur’ani, bayan ta gama ta miƙe ta shafa magungunanta da kanta daga kai har kafa kan ta saka riga dogo marar nauyi, tana zama a cikin kujerun ɗakin yana shigowa.

Ganinta haka ya sa ya sakar mata murmushi itama ta mayar mai tana sake cewa
“Ina kwana?”

Yace
“kin tashi lafiya? Ya jikin?”

Tace
“Alhamdulillah”

Matsowa yayi kusa da ita tare da rankwafowa yana duba bayan wuyanta inda ƙadangaren ya bar tambari sede wayam babu, ajiyar zuciya ya sauke wadda numfashin a wuyanta se da ya sakata saurin kame jikinta tana ɗauke numfashi.

Mikewa yayi yace bari ya ɗan kwanta, dakinshi ya wuce ita kuma ta mike ta fara gyaran ɗakinta daga nan ta sauka ta musu abin kari ita da husna, tana haurowa ta gamu da Fatima, abunda ya faru jiya ne ya dawo mata se tayi saurin kauda Tunanin Dukda gabaɗaya gidan babu wadda ya san ainihin su Fatima se ita amma bazata ce sune suka mata hakan ba tunda bata da shaida..

Har zata wuce se ta tsaya tare da waigo wa ta dube ta tace
“Faɗan bayan fage na lusari ne, harara a duhu kuma baze sa in chanza rawa ba kirrr nake kallonku, wai baki yi mamakin yadda nake yawan faɗin cusa kanki kika yi wurin samun ya Faizan ba? Ko kwakwalwarki a toshe yake baya tunani? Toh duk wani sirrin ku yana tafin hannuna the next time kuka sake yi min abu makamancin haka ina me tabbatar miki za’a yi walƙiya… Karku yi gangancin tarar aradu da ka don tabbas kuka tara se kun samu, ni ɗin kafin Allah ce!”

Tana kai nan ta nufi ɗakin Fatiman ta tado husna suka yi ɗakinta har lokacin Fatiman na tsaye tana juya maganan, kenan Fauza ta san suna da mission akan ahalin prof? Ta yaya? Kuma a ina ta sani? Da sauri ta nufi ɗakinta don kiran Aunty hankalinta a tashe.

Fauza kam bayan tayiwa husna wanka ta zuba musu abincin da already ta hauro dashi suka fara ci, har sun yi nisa don har husna tana cewa ta koshi ya tura kofan ya shigo.

A tsakiyar center rug ya samesu suna ta cin abinci, har a ranshi yaji sanyi ganin har ta iya yin girki kenan ta ji sauƙi, zama yayi husna na gaidashi.. Daidai lokacin ta gama itama ta fara tattare wurin ganin bata mishi tayi ba kuma ranshi ya riga ya biya yace

“Ni baza’a bani breakfast ɗin bane?”
Ɗago kai tayi ta kalleshi kan ta kauda don bazata iya faɗar abunda take son faɗa ba matukar tana kallon cikin idanunshi tace

“Ni? Wani jagwalgwalon zan baka?”
Kallon mamaki yake aika mata magana take shirin gaya mai ko me?

Yace
“Eh jagwalgwalon dae zan ci”

Tace
“ai wannan ba zaka iya ci ba, na tabbatar matarka da ta kware a girki ta tanadar maka hadadde ma kuwa”

Kallon husna yayi yace
“je parlor ki kalli cartoon”
Da gudu ta tashi ta fice.

Yace
“Me kike nufi ne kam?”
Ganin ta mike tana shirin tattare kwanukanta tace
“Yaaya pls me yasa kake so se na fito na faɗa kai tsaye? Toh ina nufin ba zan iya baka ba gaskiya don jagwalgwale ne kaje wurin matarka ta baka me daaɗi.. Ko ba haka kace ba?”

Tayi maganan tana kallon gefe…
Mikewa yayi ganin da gaske take yayi saurin riƙe hannunta yana cewa
“Toh yanzu zan cigaba da cin jagwalgwalon don raba muku girki zan yi kwana bibbiyu yadda addini ya tsara”

Kai tsaye tace
“ni kam ba zan yi ba”
Ta karashe da murguda baƙi idanunshi gabaɗaya ya waro yace
“ni kike yiwa rashin kunya da murgude murgude?”
Me makon yaji haushi ma dariya take bashi ala dole fushi take yi.

Tana kunkuni tace
“ni dae ba zan yi ba bana so ai tun farko ba’a nuna ana so ba se yanzu! Ni de babu wani girkin da zan karɓa”
Hannu ya kai ya dalli bakinta

“ni kike yiwa kunkuni?”
Haba ai se ta sakar mai kukan shagwaɓa har da bubbuga kafafu wai zafi…

“Yaa ilahil alameeen”
Ya furta akan lip ɗinshi kawai yana kallonta, yarinyar nan bazata kashe shi ba.

Ganin kaman yayi fushi yasa ta dangwalar da abincin tana tura baki ta zuba mai, ba tare da ya kalleta ba yace
“ɗauke kayan ki ba zan ci ba”

Da sauri ta fara kokarin ɗaukewa yayi hanzarin rike hannunta suka zubawa juna idanu….

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected