Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Chan cikin baccin ta taji ana taɓa gefen hannun kujeran da tayi matashi dashi, yadda ta saba yiwa jadda in bacci be ishe ta ba ta tura baki ta mike cikin kunkuni tana kaikaya idanu haka tayi, a hankali ta buɗe idanun nata se suka faɗa cikin nashi, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihu ɗaya na riƙe da Wayanshi, har kaman ze mata faɗan kwanciya bisa kujera se ya fasa.

“Riƙe Jaddah ke son Magana dake”
Ya faɗa yana miƙa mata wayan.

Da sauri ta karɓa
“Jaddah na!”
Tayi maganan tana karya wuya se hawaye..

“Haba Fauza, ke da nake miki kallon jaruma ashe ke ɗin raguwa ce kukan ma menene to? Yayyun naki suna miki wani abu ne?”

Yadda ya kakkafeta da idanu yana jiran jin me zata cewa jaddan yasa tace
“babu komai Jaddah kawai nayi kewanku ne”

Tace
“nima anan hankalina da tunanina duk yana wurinki Fauziyya fatan babu komai ko? In akwai wani abu ki gayamin”

Tace
“ba komai, ina mammi ya kafafunta? Allah sarki yanzu wa ze dinga mata Adu’a oho”
Ta faɗa cikin alhini.

Murmushi Jaddah tayi tace
“tana yiwa kanta amma na san tayi kewanki itama, fadyaa zasu taho ranar Laraba me kike so a kawo miki?”

Zata yi magana ya zare Wayanshi ya sa a kunne tare da Juyawa ya nufi fita yana cewa
“Zaku ƙarar min da credit, me zata buƙata kuwa yarinyar da ta zo jiya in ba ke ba ma Jaddah”

Zata fara mishi nasihun da suka kashe mai jiki da niyyar da yayi a kan yarinyar yayi saurin kashe wayan, daga Jaddah, Babanshi da mammi duk in sun kira ko ya kira su maganan ɗaya ne kar ya sa yarinyar nan kuka kanwarshi ce wacce ko ba aure shi me share mata hawaye ne, hakanan bata da kowa a Abuja in ya cuceta don ba idanunsu Allah na gani kuma ze saka mata.

Yana zama kan kujera se ga call na baba prof suka gaisa kan ya ce
“na manta ne ban maka maganan karatun yarinyar nan ba, ka san ko bare na aurarwa ɗiyata akwai sharadin yin karatu to akan Fauziyya ma ba zai sauya zani ba, idan Neco ɗinta ya fito zaka nema mata university of Abuja su cigaba da zuwa da yayarta”

Idanunshi na kan TV ya ɗan fesar da iska yana shafa kai yace
“Baba ba za’a bar maganan makarantar yarinyar nan mu ga kamun ludayin ba tukun? Ba wai ina nufin ba zata yi bane sede ina tsoron komawarta halin da ta shiga a baya ne wadda yanzu se ya fi zunubi da da, tunda yanzu tana da aure”

“in shaa Allahu yanzu bani da shakka akan Fauziyya zata maida hankali tayi abunda ake so, mu cigaba da Adu’a dae kar mu gajiya sannan ka riƙe ta amana kaman yadda ba zaka cutar da farida ba karka cutar da ita Faizan”

Ajiyar zuciya me nauyi ya saki yana sake shafa kanshi Fatima ta fito ta zauna kusa dashi tana cewa
“ya aka yi ne?”

Ya ce
“Fauziyya…! Kowa ya tashi amana amana duk sun ɗaure ni da jijiyoyin jikina wallahi”

Bakinta ta taɓe kan tace
“amma yaya ka san yarinyar nan da gangan ta so cutar dani ɗazu? Ai ko bata san ina da BP ba ta iya girki me yasa bata yi me kyau ba?”

Yace
“Meyasa ne kike son dawo da abunda ya riga ya wuce Fatima? Yarinyar nan ta baki haƙuri ba shikenan ba? Kina ji dae ina faɗa miki yadda ake bani amanarta kina so ne in yi ta jan matsala tsakaninmu har iyayemu su yi fushi damu?”

Girgiza kai tayi ranta na zafi, wai ina duk tsanar da yake cewa yana yiwa Fauziyyan? Duk a kwana ɗaya baya bata wani wuta wuta kaman ma lallaɓata yake akan wani dalili? Idan ta bar zaman nan ya cigaba a haka akwai matsala dole zata nemi wani hanyar wargaza tsakaninsu.
Da sauri ta miƙe ta ɗauki wayanta dake kan table ta nufi ɗakinta don neman shawarar abin yi…

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

18

Bata san me ya hau kan Fatiman ba ta dena shiga mata sabga girki ma idan ita zatayi bazata ci ba, se ta koma dafa nata ita kaɗai ita Fatiman nayi musu su biyu.

Tsakanin ta da shi kowani asuba ze tasheta sallah, anan take gaishe shi ba zasu sake haɗuwa ba se wani asuban sbd bata fita a sadda taji motsin su a parlor, babu ruwanshi da komai nata tunda bata rasa ci da sha ba don be katangeta ta harkar abinci ba kullum kawo abubuwa ake a loda a fridge se abunda taga daman dafawa.

Iyakaci ta ci ta sha ta kwanta, a sati biyu da suka yi tayi wani irin kara girma fatanta ya sake yin fresh sbd zama wuri ɗaya, kaɗaici duk ya dameta gashi bata da waya bare ta ji mutanen gida.

Yau bata nemi abinci ba sbd wani series da ake yi a Star life da ya ɗauke mata hankali bata kula da lokaci ba kawai taga magrib yayi ko da tayi sallah bata tashi ba har tayi isha kan ta mike ta ninke hijab ɗin ta ajiye, sanye take da wani half gown wadda iyakanshi kaurinta purple ya zauna mata das a jiki, gyale ne yake dashi se ta mishi ɗaurin da ya fitar da jelar gashinta yana reto, ɗan kunne fashion purple ne a kunnenta haka ta buɗe kofan ta ta fito.

Dasu ta ci karo yana zaune hannunshi da remote Fatima kuma na kwance a kan cinyar shi cikinta gwanda ne a bowl da ta yanka kanana tana ci a hankali, jin motsin ta yasa duk suka ɗaga idanu suka zuba mata kowa da abunda yake saƙawa a ranshi..

Kaman bazata yi magana ba se tace
“Sannunku”

Be amsa ba ya maida kai TV haka Fatima ma bata amsa ba, a wuya yarinyar ta tsaya mata barin ma yadda take kara murjewa tana kyau kaman ka sure ta, ba don umarnin da aka bata na ta ɗauke kai a kanta zuwa ɗan wani lokaci ba da bata barta tana morewa zamanta gidan ba.

Kwafa ta ja a ranta tana cewa
‘Fauza kema maganin ki’
Daga haka ta nufi ƙasa abunta, kitchen ta je ta fara Haɗa macoroni salad ɗan daidai na cikinta, bayan ta gama tayi smoothie na ayaba da madara ta zuba a cup, kyuiyar haurawa taji dashi don se ta sake fito da kwanukan bata iya bari a ɗakinta don haka dining kawai ta karasa ta zauna ta fara cin abincinta.

Da ma ze yiwu da ta ce a dawo mata da kayan ɗakinta ɗakin ƙasan tana rayuwanta hankali kwance, da kyar ta gama ɗan abincin taje ta dauraye plate da cup ɗin ta mayar ta kara kimtsa kitchen ɗin don tsabtar gidan banda dakunan masu gidan har yau bata dena ba.

Haurawa ta nufi yi yanayin da ta iske su ne yasa tayi saurin ɗauke kanta ta nufi ɗakinta Dukda sun riga sun Haɗa idanu dashi, janyewa yayi wadda hakan ya sa Fatima Juyawa se ta ganta tana kokarin shiga ɗakinta, tana ji Fatima na tsaki sede bata juyo ba Dukda kuwa so take tayi waya da su jadda kaman me.

Haka dae ta kwanta tana ta juye juyen kewa kan bacci ya sure ta, washegari da asuba da ya shigo ɗakin ya jima tsaye yana kallon yadda ta kwanta ɗin a matukar takure irin kaman mutum na kaɗaici haka, se ta ɗan bashi tausayi bubbuga gefen pillown yayi tayi miƙa wadda ya saka shi saurin ɗauke idanu daga kanta kan ta miƙe zaune bakinta na motsin Adu’a kaman yadda ta saba tana gamawa tace

“Ina kwana”

Ya amsa
“lafiya”

Ɗan tsayawa yayi be fita kaman yadda ya saba ba yana tunawa da Fa’iza ta zo gidan basa barin ta tayi mintuna arba’in ɗaki dole zasu zauna da ita su yi hira a ci abinci ayi kallo duka, amma in ba jiya ba ya manta rabon da ya ganta tana tafiya zata kitchen ko wani abu Sam basa haduwa se a ɗakinta in ya zo da asuba ba dole ta takure wuri guda ba!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected