Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

A hankali suke waya tun bata saki jiki ba har ta sake saboda ya iya hira da sanya dariya ga kalamai, ta shagala sossai se jin bugun kofa tayi da sauri ta ce mai tana zuwa ta kashe wayar tare da boyeta cikin Rigan pillow ta dirka taje ta buɗe kofan.

“Jadda tace ki fito ki ci abinci kar kiyi bacci baki ci ba”
Cewar zaliha.

Bayan zaliha ta bi suka fito tare, kan kujera ta zauna bayan ta ɗauki abincin daga cikin tray da zaliha ta shirya ta fara ci, Jaddah na bata labarin irin kewar ta da suka yi gidan yayi shiru sossai a kwana biyu da bata nan.

“Ashe ana kewata amma in ina nan kowa ya buɗe baki Fauxa kaza Fauxa kaza!”

Jadda zata yi magana wayanta ya fara ruri ta duba tace
“oh kai kuma se yau ka tuna dani”
Ko bata faɗa ba Fauxa ta san waye don haka ta maida kanta kan TV Dukda wa’azi ne gwara ta ji da ta ji zancen da zasu yi.

Bata san ma jaddar ta kashe ba saida taji tana cewa
“Fauziyya yi sauri gama ki je ki sharewa Yayanku ɗaki ki wanke mai toilet yadda kwana biyu be zon nan ba na tabbatar yayi kura kuma kin san shi da rashin son datti, yace min ya shigo garin gida ne dae ze ɗauki mintuna masu yawa kan ya karaso akwai abunda ze yi”

Haɗe gabas da yamma tayi kaman zata yi kuka tace
“Jaddah ina Fatima da ni zan mishi aikin ɗaki yau? Allah ya kyauta wlh kin dae san kap rayuwata ban taɓa taka kafa ɗakin shi ba haka kawai ba zan fara yau ba…”

“Fitsararriya ajiye abincin nan ki wuce kan in Haɗaki da abincin in take”
Cewar baba Alhj da yake shirin shigowa sallamar da ze yi ma be yi ba sbd abunda yaji Fauzar na faɗawa Jaddah.

Da sauri ta miƙe tsaye
“ban hanaki saka waennan kayan ba?”

Da sauri ta wuce ɗaki tana tura baki seda ta shiga ta fara kunkuni, kaman zatayi kuka haka ta sanya hijab kato har ƙasa ta fito, ta samu baba Alhj na cewa Jaddah

“Mama ni fa ba tsanar ta nayi ba, halayen ta ne bana so, a yadda Fauziyya ta ɗauko rayuwarta wlh bata so gamawa da duniya lafiya ba, tun da ta sanya kafa ta bar sashena bata sake zuwa ko da gaisheni bane wai dani uban ta zatayi gaba? Har Fauziyya ta bar garin nan bata iya zuwa ta min sallama ba se a bakin mamanta nake ji?”

Kanta ƙasa tace
“key!”

Jadda tace
“Kin san inda nake ajiyewa ai”

Ɗakin Jaddar ta wuce ta ɗauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faɗa Adu’a da lallashi Fauza ke bukata ba faɗa da duka ba.

Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah).

Direct ɗakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key ɗin, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a ɗakin Sam babu tarkace kaman ba ɗakin namiji ba.

Gado ne a ɗakin saɓanin sauran ɗakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai ɗan corridor inda drawer ɗinshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe ɗinshi tare da ɗaukan tsintsiya ta fara aikin ɗakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan.

Tsab ta share ɗakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror ɗinshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take ɗakin ya ɗau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab ɗinta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita.

Tana sanyo kai ɗakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faɗawa, wani irin disgusting look na me kike min a ɗaki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta.

Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta ɗau hijab ɗinta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape ɗinta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa.

Kai tsaye yace
“Ke!”

Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi.

“Ke! Sa gwiwowinki a ƙasa”

Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace
“Amma me na y….”

Ɓas haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace
“kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?”

Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama ɓaci wani tsanar shi na sake mamayarta.

Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts ɗinshi kawai yake son yi..
“Me ya kaiki Abuja?”..

Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, hannayenta suka soma rawa, bata ɗago ba don tana ɗagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta.

“Don’t let me repeat myself… Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?”

Gabaɗaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire
“A…abu…ja kuma?”

Be yi magana ba, tace da sauri
“ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba”

Duk yadda ya so ya firgita ta ta faɗi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba.

Tsaki me karfi ya ja yace
“get out of my sight”

Da sauri ta miƙe tayi kofa ya sake cewa.
“Ke!”

Chak ta tsaya, yace
“this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a ɗakina bana son harka da kazamai kin gane ko?”

Kai ta gyaɗa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata.

Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali.
Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja? Allah ka rufa min asiri.
Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace

“Fauziyya”
Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious.
“Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saɓawa iyaye kaman saɓawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saɓa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saɓa musu alhali ban koyar dake ba?”

Raurau tayi da idanu tace
“me nayi kuma Jaddah?”

“Meyasa zaki yi tafiya baki sanar da mahaifin ki ba? Ba wannan ba meyasa tunda kika dawo nan baki je kin gaida shi ko sau ɗaya ba? Kina son ganin haske a rayuwarki? Ya kamata ace kiyi nadama ki shiga alhini akan korar da yayi miki a sashenshi amma Fauziyya duk babu? Ko don kinga kina dani? Har fa rashin lafiya mahaifin ki yayi cikin wata biyar din nan ashe baki je kin gaishe shi ba?”

Bakinta kaman ze taɓa gini tace
“amma Jaddah kina ji yace ko ganina baya son yi, taya zan kai mishi fuskar da baya son gani da sunan gaisuwa?”

“Fauziyya!”
Jaddah ta kirata ranta na ɓaci.

Hawaye saura kiris ya zuba mata, dama bata dawo ba da wannan damuwar da ta dawo ta riska kuma.
“Naji jadda zan gyara yanzu kullum da safe kan in tafi makaranta zan je in gaishe shi ba shikenan ba? Kin turani ɗakin wanchan ya wulakanta ni kin huta!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected