Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Jaddah ta amsa tana mata sannu da zuwa har ƙasa ta duka ta gaida surukar tata, bayan sun gama Gaisawa ta tambayi me jiki Jaddah tace da sauƙi don har ta sha pepper soup ɗin kayan ciki da Amminta ta turo baba Alhj dashi da ruwan zafi.

“Bacci ma take”
Cewar mammi.

“Yanzu fa muke hira ina ga baccin ya fusge ta”

Shi kam da idanu yake binta, kaman ze cinye ta, fuskanta yayi fayau ya faɗa, tsab kuma ya fahimci ba bacci take ba shine bata son gani, ajiyar zuciya me sanyi ya sauke suka gaisa da Jaddah kan, Jaddah da mammi suka fita akan zasu je wurin fa’iza daga chan Jaddah zata wuce gida mammi ta dawo ɗakin.

Shi cewa yayi ba yanzu ba, zama yayi ya kishingida idanunshi a lumshe yana tuna the best moment of his life, be taɓa sanin haka mata suke ba lallai fauzar tashi ta daban ce, a kan labbanshi ya furta
“precious pearl” wato lu’u lu’u mai daraja.

Murmushi ya saki yana gyara kishingidarshi haka ma ya gode.

A hankali ta soma buɗe idanunta ta kure shi da kallo, dukda ba fuskantar ta yake ba saide tana iya hango farar fatar fuskar tashi da take cike da kwwantanccen saje da suka yi lublub, zara zaran gashin idanunshi da suka sauko sossai waenda suke taimakawa wurin maida idanunshi sexy kaman me jin bacci, gashin girarsa kaman zana mishi ita aka yi baƙi sidik, komai nashi me kyau ne da tsari.

Ganin yana motsa idanun alamar ze buɗe yasa tayi saurin janye nata tana lumshewa, murmushi me sauti ya saki a jikinshi yaji tana kare mishi kallo kuma tsab ya ganta ta ƙasan idanunshi ya barta ne ta morewa kallon nashi.

Miƙewa yayi Tsam ya nufi gaban gadon ya ja silver chair ya zauna dab ita cikin yanayin maganar shi yace
“ya dae ƴan mata? Na miki ne?”

Takaici ne ya zo mata wuya, kaman ta kurma ihu ji wani zance anan fisabilillahi.

Chan ƙasa ƙasa yace bayan ya kama hannunta ya saka cikin nashi.
“Precious pearl buɗe idanunki ki kalleni son ran ki, ni ɗin naki ne gabaɗaya, Mallakinki ne.. Ki kalleni har ki gaji babu mai miki hijabi”

Bata motsa ba kaman ma bata san yana yi ba, murmushi ya saki Sam baze yi fushi ba don ya san yayi laifi, lallaɓata ze tayi har ta sauko.

“Fauuuzaaa..!”
Ya ja sunan wadda ya saka ta jin kiran har cikin jininta, tsammmm haka tsikar jikinta suka amsa.

“Na san ban kyauta ba, na miki ba daidai ba amma wallahi ba da niyya bane so da kishin ki ne ya janyo, kiyi hakuri, kiyi min duk wani hukunci zan ɗauka amma banda shariyar nan please…ki taimaki bawan Allah Faizan kar zuciyarsa ta tsaya da aiki”

Nan ma bata buɗe idanunta ba, se baki da ta ɗan turo, red lips ɗin nata se sheki suke Dukda babu abunda ta shafa musu, caramel skin ɗin nata yabi da kallo kaman da madara take wanka tsabar shekin da fatar tata take Dukda ba fara ba ce.

Hannunshi ya kai ya zame ɗan kwalin kanta ya sanya ya fara shafa lallausar gashin kanta alamar rarrashi, ko motsi ta ƙi tayi, jin za’a shigo ne ya sanya ya miƙe ya rankwafo ya bata zazzafar peck a goshi sannan yayi pecking hannunta dake cikin nashi kan ya saki ya koma da baya ya zauna inda ya tashi.

A ranta take raya wannan gayen bashi da kunya, tsaki ta ja kaman ta buɗe idanu tayi ta dukanshi ko zata huce take ji.

Dr ce ta shigo, Gaisawa suka yi cikin mutunci tace
“Captain, Mrs Faizan kaka ta samu sauƙi ga takardar sallamar ta nan amma please a sahirta mata har ta warke don ta sha matukar wahala”

Wani irin smile yake saki yana shafa kanshi ba se ta faɗa ba ma ai yanzu shi da ya kara gangancin rabar ta ai se da amincewarta ɗari bisa ɗari.

“OK Dr. Thank you and in shaa Allah za’ayi yadda kika ce”
Karbar takardar yayi se ga jadda ta shigo ashe bata wuce ba, se kawai yace bari yaje ya biya bill ɗin kan sun Haɗa abunda zasu Haɗa se su wuce.

Fa’iza ma an sallameta don taji sauƙi sossai, saide har yanzu bata daena share hawaye time to time ba tana tuna irin evil mom da Allah ya bata.

Duk a tare suka fito, Fauzar na tafiya a hankali ko inda yake bata kallah ba, a maimakon ta shiga motar shi da ya buɗe mata se ta wuce ta buɗe na Farhan ta shiga gaba, Fatima na baya da zaliha.

Jaddah da mammi ne suka shiga nashi ya ja ya tafi kan Farhan ya bi bayanshi.

Dayake lafiyar motar ba ɗaya ba yasa Faizan ɗin ya tsere mishi kuma da yanayin tuƙinshi don kowa ya san yadda mutanen Abuja suke tuƙi ba kaman na sauran garuruwa ba.

A hankali Farhan ya shigar da motar cikin gidan, daga chan kofar sashen jadda suka hangi Faizan na tsaye yana amsa waya, kaman an ce ta kalli chan gefen kofar su se taga motar Aunty Fatima zaune a driving seat fuskanta a kumbure suntum ta kure Faizan da kallo.

Buɗe motar Fauza tayi ta fito, daidai fa’iza ma ta fito amma se suka yi sashen Mammi da zaliha don chan mammi tace ta je, yayinda Fauza kuwa ta nufi sashen Jaddah babu abunda take so irin tayi wanka ko zata sake jin daidai, Kure ta Fatima tayi da idanu tana jin tukukin bakin ciki yadda taga Faizan duk hankalinshi ya ɗauku kanta ita kuma tana tafiya kamar hawainiya.

Tada motar Fatima tayi a ranta tana ayyana da ta bar wa Fauza Faizan wallahi gwara ayi biyu babu, sake motar tayi tayi kan Fauzar gadan gadan, kanta na a ƙasa Sam bata lura ba, yayinda Faizan kuma idanunshi na kanta ta ɗauke mai hankali kaman an ce ya waiga se yaga Fatima tayi kanta da mota…

Wani irin hantsilar da wayan hannunshi yayi ya nufe ta da gudu yana kwala kiran sunanta a tsorace ta ɗaga kai kan ta waiwaya taji an yi sama da ita da mota, ta bugi gaban motar tare da faduwa ƙasa tana jin yadda Faizan ya sake kwala kiran sunanta idanunta suka lumshe.

Da gudu Fatima ta juya kan motar ta nufi gate, se daka tsalle gateman yayi don shima saura kiris ta take shi, Farhan da shima ihun Faizan ne ya rinjayeshi ya fito daga sashensu na en maza haka muryar tashi tayi sanadiyar fito da rabin ahalin gidan, babu wadda ze ce ya taɓa jin muryarshi haka don bashi iya ɗaga murya in yana magana kaman da kanshi yake se yau.

Ɗagota yayi ya sa akan kafar shi a rikice yana kiran sunanta ba kakkautawa yana cewa ta buɗe idanunta, saide inaa bata jinshi seda Farhan ne yace
“Ya Faizan dauko ta mu wuce asibiti”

Kan ya tuna da wani asibiti da gudu ya sabeta zuwa motarshi Farhan ya buɗe, mammi na riƙe da Fa’iza da ta sake sakin kuka itama tana jin kunar wannan abu a ranta kaman tayiwa Fauza kuka, me mutanen nan suke nema da ita?

Amminta ma komawa sashensu tayi tana me share hawaye, jaddah kam driver ta sa ya ɗauke ta ta bi bayansu tana ta tsinewa Fatima da Aunty Albarka.

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

32

**Assalamu Alaikum warahmatullah, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya, kun jini kwana biyu shiru nayi tafiya ne kuma ban zauna ba har saida na dawo jiya da dare, kwata-kwata ban samu time ɗin kaina ba se yau… Ku yi hakuri kaman yadda na yi alkawari kan azumi zan karkare wannan littafi wadda be dayawa saide na tabbatar saƙon ciki me girma ne in ka fahimta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected