Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Yace
“lafiya ƙalau ƙanwata”
Shiru duk suka yi ya ɗan tsaya kan yace
“Na fita”
Tace
“Allah ya tsare ya kiyaye”
Dama abunda yake son ji kenan se yayi murmushi ya nufi gangarawa.
Dama sun sha cereals yau a ɗaki don bata yi wani girki ba, zaman jiran Fatima tayi seda ta ga dama kan ta fito suka sauka zuwa motanta, gaba ta tura husna ta buɗe baya ta zauna.
Tak be Haɗa su ba har suka isa makarantar, Fauza tayi dept ɗinta suka haɗu da Afnan suka yi lecture hall, Afnan ƙanwar matar Faisal ce Dukda basu haɗu da matar ta Faisal ba amma Afnan na yabon halinta hakan ya kwadaitar mata da son zama dasu ko zata rage kaɗaici barin ma in husna ta koma.
Ko da aka tashi saida ta jira Fatima har ranta ya soma ɓaci kan ta zo suka yi gida, abinci marar nauyi ta Haɗa musu suka zauna suka ci da husna kan suka haura sama abin su.
Ko da ya dawo ma abincin Fatima ya samu haka dae ya ci yana Tunanin kwaɓar da yayi da yadda ze gyarota.
Washegari ma hakan ce ta kasance..
Suna zaune a ƙasan bishiya ita da Afnan da husna wurin akwai students haka dake kai kawo duba wani handout take yayinda Afnan ke kara mata bayani don an yi farkon lectures ɗin bata nan.
Wani shirgegen ƙadangare taga yana saukowa daga bishiyar ita ba wai tana tsoron su chan chan bane amma bata so su zo kusa da ita ganin ya tsaya yana ta gyaɗa kai gashi marar kyaun gani yasa ta ɗan ɗaga hannu tayi shhh, ai kaman ta ce mishi ya zo yayi wani irin tahowa da gudu ta kafafunta kan ta miƙe tsaye ya shige mata hijab ƙara ta saki tana ambaton Hasbunallahu wani’imal wakeel….!
***
Tsaye yake gefen Faisal yace
“kwaɓa nayi faisal kuma duk tunanina na rasa yadda zan warware shi wlh”
Faisal yace
“Toh kai ɗin ma kenan bare mu? Wani irin kwaɓa ne haka da ya dameka?”
Shafa kanshi yayi yana jan iska tare da fesarwa yace
“ka gane ko? Yarinyar nan ne a sadda ta zo na ɗauka tayi kankanta da ɗawainiyar gida kuma bazata iya wani aikin a zo a gani ba bare har ta iya girkin da zan iya ci, to my biggest surprise abubuwan da ta iya ko chef da yayi ten years in profession be iya ba, ta kula da cikina tsawon lokacin da Fatima bata nan yanzu kuma Fatima ta dawo se ta sakar mata”
Faisal ya kwashe da dariya yana cewa
“kana raina yaran yanzu my guy… Dama baka raba musu kwana bane?”
Girgiza kai yayi yace
“she’s too young”
Shi karan kanshi da ya faɗa ɗin he’s not so sure of his self bare Faisal me sauraro.
“Maganan gaskiya shine ka fito ka raba musu kwana ko da bazaku kwana tare ba ya zamana ran kwanan ta bakwa tare da Fatima ta hakan ne zaka iya kwasar girkin tunda kana so”
Shi ba fa hakan ne baze iya ba yanzu yadda ze fuskanci Fauza ne yace ta cigaba da girki bayan a fuskanta ya jefe ta da mugun kalamai yana cewa ba ze iya cin jagwagwalonta b…..
Gigitaccen Ƙara da yaji da Hasbunallahu wani’imal wakeel shi ya saka shi saurin miƙewa daga jinginen da yake..
Muryarshi na rawa yace “Fauziyya..!”
Da gudu shi da Faisal suka yi inda suka ji ƙaran tana kokarin cire hijab ɗinta yayinda wani dake daga gefe yake kokarin kai hannu da taimaka mata, cikin zafin nama Faizan ya damki hannun nashi ya cillar kan ya fusgota kaman yadda take a rude haka shima ta ruɗa shi.
Fahimtar ƙadangare ne ya sa ya sure ta gabaɗaya yayi wurin motan shi yana sanyata ya zare hijab ɗin gabaɗaya ta haukace da kuka da kiran sunan Allah daidai ƙadangaren ya zo kan bayan wuyanta se ya tsaya Chak a wurin ko motsi baya yi.
“Yaaaya.. Don Allah ka cire min wayyo kafafunshi na shiga min fata, da zafi sossai ka cire min don Allah”
Yadda take kuka take abu kaman shafan aljanu yasa ya matse ta bisa kirjinshi yasa hannu da nufin fusge ƙadangaren sede duk iya gwada karfinshi ƙadangaren nan ya ƙi ko motsi, hankali tashe yake kallon ƙadangaren wani irin tashi tsikar jikinshi yayi da sauri ya fiddo waya ya fara kiran Baba prof.
Cikin hanzari ya mishi bayanin abunda ke faruwa gashi Fauza ta dena motsi, Baba prof yayi salati ya sallamar kan yace
“ku yi sauri ku je wurin prof ghali na tabbatar ze yi duk abunda ya dace yanzu yanzu Faizan karka ɓata lokaci bari na kirashi”
Kofan motar ya tura ya kira Faisal tare da cila mai key don yanzu ba ze iya tuki ba gabaɗayanshi ya sauya idanunshi har sun sanja kala, Afnan da husna da har sun fara hawaye ne suka shiga gaba. A take ya ja mutane suna ta mamakin wannan abu da Allah ya kiyaye haka students suka watse.
A hannu ya ɗauke ta zuwa wurin malam ɗin, already Baba Prof ya kirashi ya mishi bayani, a jikinshi ya sanya ta Tare da kwashe gashinta da ya baje Malam ghali na kallon kadangaren yace
“la haula wala quwwata illa billah…”
Da sauri ya janyo ruwan zamzam da wasu Adu’o’i ke ciki ya tashi ya shiga dakinshi mintuna biyu ya fito da wani Allon karfe ruwan ya zuba a Allon kan ya saka ya buge ƙadangaren yana ambaton sunan Allah.
A take ƙadangaren ya fice fit daga jikinta ya faɗi ƙasa ya fara kokarin guduwa wannan ruwa malam ya diba ya fara zuba mai nan ya fara wani kalar birgima da mutsu mustu ba’a ɗauki lokaci ba ya zama baƙi kirin ya tamushe kaman wadda wuta ya babbake.
Faizan na ta patting kumatunta yana cewa
“Ke Fauza buɗe idanunki kiga an cire… Fauza! Fauziyya..!!”
Malam yace
“bazata tashi ba Faizan kwantar da ita”
“malam me yasa bazata tashi ba? Don Allah kayi wani abu”
Yadda yake maganan kaɗai zaka san ba karamin ruɗe wa yayi ba, me hakan ke nufi? Yau da baya school ɗinsu fa? Haka zata shiga wannan hali ita kaɗai?
Malam ghali yace
“wato wannan ƙadangaren ɗan aike ne, a yadda ka ganshin kila ta ambaci Allah a sadda ya nufi hawa jikinta da bata ambata ba ƙara kawai ta tsaya yi da yanzu ganinshi ma wahala ze mana don jikinta ze shiga, ko ya lahanta mata abubuwan ciki ta mutu ko kuma yayi mata illar da warakarshi se rabba”
“waye ze mata hakan? Waye yake neman illatar da lafiyar ta haka? Me ta musu?”
Kaman ze yi kuka yayi maganan.
Malam yace
“wannan mu barwa Allah, yanzu mu tsaya kan lafiyanta”
Ruwan Adu’a malam ɗin ya bashi yace ya shafe ta dashi, bayan yayi ya saka shi saka mata a baki, nan ya bashi za’afaran da habba da suke dauke da Adu’a yace ya shafa mata, fuska, hannaye, gashin kanta da kafafunta nan take yayi.
Ya zauna yayi shiru yana kallonta cikin jiran malam ya gama Adu’ar da yake yi, yana gamawa kuwa ya watsa mata se ta ja numfashi a kuma ruɗe tayi hanzarin mikewa tana mutsu mustu..
“Yayaaa ka ciremin… Wayyo zafi, Hasbunallahu wani’imal wakeel… Wayyo Jaddah…”
Duk bata san tana wannan sambatu ba kamata yayi ya rungume a hankali ya sauke hannunshi bisa bayanta ya zagaye kan ya da matse ta a jikin shi cikin rarrashi yace
“shhhh ƙanwata, yi shiru an cire baya jikinki… Shhh”
Lub tayi.
Malam yace
“ku je a duba jikin nata in ya so ko maganin asibiti se a sake bata watakila yana da dafi, amma ga wannan ta dinga anfani dasu zamu yi magana da Mahaifin naka”
Prof ghali babban malami ne don tsohon professor ne na musulunci abokin Baba prof ne, kuma dama chan Faizan kan leƙa ya gaida shi idan ya samu time.
Zamewa tayi daga jikinshi kanta a ƙasa, haka suka miƙe suka fito, hijab ɗinta ya sanya mata yana kallon bayan wuyan nata da shape ɗin ƙadangaren har yanzu yake kwance yayi baƙi sidik…