Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ita dae Fauza tunda tana da husna bata da matsala don yarinyar na debe mata duk wani kewa, tare suke koman su cikin hira da dariya lokuta dayawa gani take kaman husnan sa’ar ta ce in gujel gujel ne ma duk haka suke zagewa su yi kayansu.
Kaman yau a parlorn ƙasa suka yi la’asar sbd cookies da suke yi kar ya ƙone, bayan sun idar suka zuba shi a tray me kyau, da Homemade pineapple juice tayi musu har zasu haura dashi se husna tace
“Aunty mu je garden pls you promised fa cewa weekend nan zamu je ni kam I want to play with swing”
Fauza ta kalleta tace
“ke kam kina da aiki mutum baya mantuwa? To mu je”
Juyawa suka yi suka fito, daga hannun hagunsu akwai wani ƙofa suka shige sun ɗan yi tafiya kaɗan se ga garden ɗin masha Allah kore sharrr, akwai lilo sbd hutawa, gefen shi akwai table da chairs, nan ta ajiye snacks ɗin, suka je suka hau Lilon suna lilawa Fauza na tsoron juwa bata so da karfi amma da gangan husna ke wullawa da karfi wadda ke saka Fauza ihun kiran sunanta ita kuma ta watse da dariya.
Zaune yake a balcony ɗinshi bayan ya dawo daga sallar la’asar sanye da farar jallabiya wacce bata kai kasa ba don kana iya hangen black trouser da ya sa daga ciki, fuskanshi yayi wasai yayi wani irin kyau, dariyar su da kuma ƙarar Fauza shi ya saka shi miƙewa tsaye, chan ya hange su suna ta lilo, lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan tray ɗin dake gefensu, ba karya his tongue have been craving for the tatse of her food again barin ma tea ɗin nan da sati biyu kenan da yake so yace ta mishi yana fuskewa.
Jaridar ya ɗauka ya koma ɗakinshi ya buɗe kofa ya sauƙa ƙasa, a natse yake tafiya cikin ƙasaitacciyar tafiyar shi da already ya zamar mishi jiki ya isa garden ɗin.
“Husna bari! Bar lilawa hakanan jiri ze yarda ni”
Ta faɗa tana runtse da idanu, husna kam ina ruwanta ta maida kafafunta baya ta cilla da karfi daidai ta buɗe idanunta ita kuma ta hantsila tana shirin faɗuwa yayi azamar tare ta duk idanu suka zubawa juna..
Da sauri kuma ta miƙe tsaye tana gyara ɗan kwalinta da ya zame ya bayyana baƙi sidik ɗin gashinta da ta tsefe kitson bukin ta ta tufke saboda ihun da husna tayi na
“Uncle zo ka hau lilo tunda Aunty na tsoro..”
Ta faɗa tana wangale mishi wawulonta, murmushi yayi yace
“zan zo babyn uncle amma yanzu cigaba da abun ki ke kam”
Ya karashe yana zama akan chairs ɗin wurin tare da crossing kafanshi, duburcewan da tayi yake kallo ƙasa ƙasa duk in yana wuri sakewarta ba sossai ba don tun sati biyu da in har yana gari ya kan shiga sau biyu ya duba su ya lura da hakan musamman idan husna ta rike shi da surutu ya ɗan jima se ta rasa natsuwa.
Juyawa kawai tayi tana cewa husna
“in kin gama se ki dawo ɗaki”
Har ta juya ta ji sassanyar muryarshi me cike da natsuwa ya ce
“Ji mana..!”
Baki ta tura tace a ranta se kace wata budurwa da ake shirin tarewa a titi.
Juyowa tayi bayan ta gyara bakin da ta turon tace
“Na’am”
Yace yana kallonta kai tsaye wadda har tsikar jikinta take jin kallon
“Ni dodo ne da in na zo wuri kike guduwa?”
Bakin ta sake turowa tana cewa a ranta
“ai ka fi dodon ma razanarwa, in ka so kayi kirki in ka so ka tabka tsiya ko a gyalenka”
A fili kuma tace
“A’a kawai ina da abunda zan yi ne a cikin”
Yace
“ok, before then zan samu shayi?”
Kai ta gyaɗa mishi kan ta juya ta fice, cookies ɗin ya ɗau ɗaya ya sa a baki yana mamakin yadda ta iya abubuwa haka masu daaɗi.
Cikin mintuna da basu fi ashirin ba ta dawo da tray me ɗauke da karamin glass tea flask da cups ɗinshi a jere a gefe, a gabanshi ta ajiye tana kallon yadda yayi nisa a cin cookies ɗin nata.
A ranta tace
“ko tayi ba’a yiwa mutum ba ya zage ya cinye mana abunmu”
Kaman kuwa ya san me take cewa yace
“daina min kallon ba’a gayyaceni ba na ci, ladan kati na da kika ƙarar ranan ne”
Wara idanu tayi a kanshi yana tsiyaya tea ɗin a cup bayan ya gama ya ɗago yace
“yes”
Ta langwabe kai tace
“to Ayya in sake maka cookies ɗin ka bani in sake waya dasu? Bana jin daaɗi yadda na kwana biyu ban ji su ba”
Yace
“no bana son wannan, wani abu daban nake so”
Ta Yi saurin cewa
“menene?”
“Zaki dinga dafa min wannan tea ɗin kullum”
Da saurinta tace
“eh na yarda”
Murmushi ya saki wadda ya sakata kusan shagala da Kallonshi yace
“wayan na sama in mun haura zan baki”
Tsallen murna tayi tana cewa ta gode, kallon da yake mata yasa ta natsu ta juya ta wuce cikin don bazata iya zama a inuwa ɗaya dashi ba Sam bata iya sakewa.
Kaman yadda yayi alkawari bayan sun hauro da Husna ya bata ta kai mata, taji daaɗi sossai amma ta ji haushi da ta duba taga ya goge hotunan da tayi a wayan kuma da gayya ne tunda ga na matarshi da nashi na ciki nata ne ya goge, a daren suka sha hira da jadda har da su fa’iza da faaazila sun gaisa sbd tayi kewarsu.
Mammi ma sun jima suna waya kan ta ba husna ma ta ishe ta da surutu, bayan sun gama ta bata wayan ta maida mishi.
Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka’ida se tayi mishi tea ɗin nan, yawanci tana samun shi ko a dining ko a parlor ta ajiye mai, sadda Fatima tayi noticing kusan hauka ta saka mishi ai ba bata iya bane be ce yana so bane, shi kuwa namijin duniya kai tsaye ya ce mata na hannun Fauza yake so ba nata ba shiyasa be tambayeta ba, tayi kukan maganan nan, kudirinta da haushinta kan Fauziyya kuma ya ƙaru, dukda Auntyn ta tayi fushi me girma da ita sbd abunda tayi kwanaki tace ya so lalata musu aiki don in ta bari Faizan ya fara tausayawa Fauza so ze iya shiga idan kuma so ya shiga tabbas ze saka alamar tambaya akan son da yake yi mata ita.
Ta dawo daga lectures tana haurowa suka kusa cin karo da fauza dake shirin sauƙa da kayan tea ɗinshi da yanzu kenan ya gama sha take shirin sauka dashi, tare ta Fatima tayi.
Matsawa tayi zata bi ta gefe ta sake tare gefen, tana kallonta tace
“Fauza me kike nufi da mijina?”
Har kaman bazata amsa ba se kuma tace
“me kuwa nake nufi? Last time da na bincika duniya sun sheda Cewar matan Faizan biyu ne, ko kunnuwanki sun toshe ne a sadda amsa kuwwa ke bayyana cewa an shafa Fatiha fauza ta zama ta Faizan?”
Wani irin takaici ne ya zowa Fatima wuya
“ke har kin kai macen da zaki yi ikirari namiji kamille irin Faizan ze so ki? Sauran wasu ce fa da sauran shaye sha….”
“Shhhhhhhhh”
Fauza ta faɗi tana sa mata hannu a lips ɗinta tace
“wannan kuma tsakaninmu ne kin gane ko? So kiyi ta kanki gwara ni ban bi hanyoyi masu yawa da haramci wurin mallakarshi ba, ban kuma zauna na ɓata hawayena wurin kukan in ban same shi ba zan mut…..”
Ɗaga hannu Fatima tayi zata mareta tayi saurin tarewa wadda ya saka tray ɗin hannunta faɗuwa ya fashe tartsatsa, hannun Fatima ta cillar wadda ya sakata loosing balance ta tafi suuuu tana kwala ƙara.
Razanar da tayi yasa Dukda bata faɗi kan cikinta ba cikin ya ƙulle har jini ya balle mata, Da sauri ya karaso yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun, Fauza ta buɗe baki zata mishi magana ya ɗauke ta da wani irin mari wadda ya sakata yin baya kafanta na dama ya sauƙa a kan glass da ya fashe a wurin, runtse idanuta tayi da karfi tana jin zafafan maganganun da yake jefanta dasu.
Bata buɗe ba har ya sauka ya kama Fatima dake kuka haikan sbd baƙin ciki don ta san wannan ciki kam se wani ikon Allah suka fice daga gidan da hanzari.