Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Abun nata kaman jinnu, tana son fa’iza sbd haƙurin ta ta kan yi hakuri da duk wani halinta tana yawan kare ta, in kaga sun yi faɗa to akan Fatima ne, Fatima na son nuna mata uwarsu ɗaya da fa’iza ita kuma ta tsani hakan, idan kuma fa’iza tace mata kar ta biyewa Fatima su yi ai jinin dake yawo a jikinta shine yake yawo a nata jikin tunda uba suka Haɗa se ta ce ai fa’iza ta goyi bayan Fatima alhali Agola take a gidan Anan zasu yi faɗa su Rabu Toh Fauxa da zuciya se ayi kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa’izan yake yawan ja baya.
Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace
“Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa”
Jaddah tace
“se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba”
Fa’iza tace
“kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare”
Mikewa Fauxa tayi tace
“mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba”
Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.
Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni’imtacciyar inuwa.
“Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za’a yi ruwa da kankara”
Fauxa na murmushi ta zube kasa tace
“sannu Mammi ina yini? Ya kafa?”
Mammi tace
“Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har ɗazu ma na taka zuwa toilet”
Fauxa tace
“Allah ubangiji ya ƙara sauki”
Da Ameen ta amsa, fai’za ma ta gaisheta.
Fauxa tace
“Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma”
Ta karashe tana karya wuya
Mammi tace
“Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba”
Tana dariya tace
“Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa”
Mammi tace
“ba za’a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaɗi”
Cikin jin daaɗi Fauxa ta mike, fa’iza ta bi bayanta suka yi kitchen.
Anan suka kwaɓa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaɗa sbd shi fa’iza ke so, suna cikin yi se Fa’iza tace
“ni bani manjan ma in yi mixing kaɗan yadda ze bada wani dandano me armashi”
Fauxa tace
“Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so”
Musu suka fara, fa’iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta ɓalle da gudu daidai kofar kitchen ɗin taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaɗaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.
A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya..
Ko kaɗan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma’abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baƙi sidiƙ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma’abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murɗaɗɗen hali da zama dashi se ka shirya.
Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen ɗin, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya ɗago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha’awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa’iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka.
Kokari yake yayi controlling ɓacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haƙuri ta kasa ce mai yasa ya ɗaga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi ɗin sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taɓa Haɗa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin ɓacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain ɗinshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta.
Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun.
Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa’iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.
“Sannu Fauxa! Sannu”
Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa
“Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?”
Cikin kuka Fauza tace
“mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!”
A hankali Mammi tace
“FAIZAN!” Don shi kaɗai Fauxa ke cewa Azzalumi.
Da sauri Mammi ta cewa Fauxa
“ɗauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi”
A hankali ta karasa gareta ta ɗaga ta tare da riƙe hannun har ya tashi gabaɗaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaɗi amma se ta saɓawa Faizan, ashe kaddarar ƙone wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka?