Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Da Faizan ya gaji ya kira baba Alhj ya faɗa mishi, aiko kaman ze bar yola ya zo Abuja ya daka ta don faɗa seda baba prof ne ya dakatar dasu ya kirata ya mata nasiha sossai da kuma nuna mata kyauta ce daga Allah wasu na nema ido rufe basu samu ba, kan ta sassauto be bar Faizan ɗin ba ma ya mishi faɗa shima ya nuna mishi Fauza har yanzu yarinya ce, kwata kwata yanzu ne take shirin yin 19 ga albarkan yara Allah ya bata idan be bita da lallami ba kenan ba anfanin tarin shekarun da ya bata.
Wayanshi da ta gama jin nasihar mammi ta mike ta nufi ɗakinshi Shiga d’akin tayi don bashi wayanshi ta samu har bacci ya d’aukeshi, a gefen hannunshi ta zauna tare da kura mishi ido na seconds yadda lashes d’inshi suka kawata fuskanshi zuwa sajenshi da yafi komai d’auke mata hankali lumshe ido tayi ta bud’e kan pink lips d’inshi da ya d’an bud’e kad’an, murmushi me kyau ta saki he looks so damn cute kaman d’an baby, d’an buge goshinta tayi tare da mikewa da sauri bata d’aga kafanta ba taji ya rike hannunta tare da fisgo ta ta fad’a kan gadon kanta ya sauka akan hannunshi da ya Mikar cikin wani irin yanayi ya bud’e idanunshi da suke cike da bacci da tsananin kewanta ya zubasu cikin nata yana lumshewa a hankali.
Wani abu taji daga tsakiyar kanta har zuwa babban yatsanta ya tafi zirrrrr, runtse ido tayi tare da d’an juya kanta kad’an zuwa kan hannunshi hakan ya bawa gashinta daman zubowa saman fuskanta, hannunshi d’aya ya sa ya maidashi a hankali zuwa bayan kunnenta, tare da maida hannun cikin hannuta dake tsakiyarsu ya fara shafawa a hankali.
“I badly missed you hayatee…if am left alone without you how am I supposed to live?”
In a whisper tace
“I missed you more Hubby am so sorry, na yi kuskure, forgive ur wife”
Peck yayi mata a goshi kan a ƙasan maƙoshi yace
“u are pardoned, I love you”
Ta rungumeshi tana mishi raɗa a kunne
“I didn’t fall in love with you because I was lonely or lost, I fell in love with you because after getting to know you, I wanted to make you a parmanent part of my lif…”
Bakinsu ya haɗe sbd kasa hakura da yayi a take suka fara nunawa juna zallar so da kauna me tarin yawa wadda baki yayi kaɗan ya misalta ko ya furta.
FIVE YEARS LATER
Da gudu suka hauro saman suna rige rige, dukkansu uku sanye da uniform na makarantar boko
“mommyyyy! Daddyyyyy we are back yeyyyyy”
Fauziyya dake daga tsaye tana serving Faizan Abinci ta haɗe fuska tamau tana gyara tsayuwar ta da ya bayyana cikin jikinta da ya soma girma tace
“Arwa, Marwa, Alaya me na faɗa muku akan sallama?”
Chak suka tsaya se suka juya sum sum suka koma da baya suka doka sallama daga karshen stairs seda ta amsa ta musu izini kan suka hauro har lokacin bata sake fuska ba.
“Sorry mommy mun manta ne”
Arwa ta faɗa tana kama kunne.
Marwa ma tace
“sorry mommy”
Alaya da taci Sunan Ammi tace
“we’re sorry mammy”
Faizan yace
“my princesses are sorry daga yanzu bazaku sake shiga wuri ba sallama ba ko?”
Da sauri suka gyaɗa kai Alaya tace
“Allah mommy in mun sake punish us”
Dariya Fauza tayi wai wani punish them ko me za’a yi punishing ɗin oho,
“oya kuje Mamu ta muku wanka ku zo ku ci abinci kar kuyi lattin islamiyya”
Da gudu suka wuce ɗakin su..
Faizan ya dube ta yace
“mommy please a taimakeni da soldiers nima in samu friends”
Murmushi kawai tayi, da dare suna kallon news ake sanar da mutuwar ɗan dan majalisa wadda ya shigar da kwaya wata kasar da ba’a shiga da kwaya kwata kwata suka kama shi ya jima a prison ɗinsu kan ya mutu, Zubair ta gani rayuwa fa kenan in kana takamar kuɗi da hanya akwai inda zaka je ka zama bawa ko almajiri don a komai wani ya fi wani ne..Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta.
****
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!
ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NA DIDDIGAR ƘAYA ME WUYAR TSINCEWA, ABUNDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WADDA KUMA MUKAYI KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA. WAENDA SUKA SAYA INA MATUKAR GODIYA DA KAUNA KUMA INA ALFAHARI DA KU A DUK INDA KUKE, KU KUMA DA KUKA FITAR MIN DA LITTAFI KU KUKA SANI DA ALLAH, AKWAI FULL DOCUMENT ƊINSHI IDAN DA WANNAN PAGE KIKA FARA CIN KARO MAZA BIYA KI MALLAKI NAKI KI SHA KARATU KI KWASHI ILIMI.. ALLAH YA SADA MU A WANI LITTAFIN NA GABA❤️
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shimfiɗa*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**Assalamu Alaikum warahmatullah, tadaaaa ga Gureenjo da sabon littafi,salo,labari me kama zuciya.. Ba zan ce wadda baku taɓa gani ba sede in ce ya sha bam-bam da wadda kuka saba gani, Mallaki naki tun kan free pages su ƙare ki sha karatu cikin kwanciyar hankali**
Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata, wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.
“Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali… Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba, idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!”
Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
“Na yarda baba Alhj….a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina…! Ko yaya yake… Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni..”
Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa.
Wani mugun kallo ya watsa mata yace
“ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!”
Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.
Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama’ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe