Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ganin baccin take yasa ta ɗauki wayan tare da amsawa ta kara a kunne, cikin kamillalliyar Muryarsa da se ka saurara zaka ji sbd rashin son hayaniyarsa yace
“Jaddah abincin fa? I’ve been waiting.”
Jaddah ta kalli Fauza tace
“ba’a kawo bane? Tun fa ɗazu na bayar a kai maka, ikon Allah..”
Yace
“wa kika bai wa?”
Ta fara jijjiga Fauziyya sbd nauyin baccin da ta riga ta sani tace
“Fauziyya! Ina abincin da na baki ki kaiwa yayanku ne?”
Juya keya tayi kan tace
“yana kan motanshi mana”
Ba tare da yace komai ba sbd yana jin duk abunda suke yi ya katse wayan, Jaddah na ta mamakin ikon Allah akan Fauxa se kawai sallamanshi taji, juyowa tayi zata yi magana taga ya nufo su hannunshi riƙe da ruwa me sanyi wadda ya fara kankanra na kamfanin Faro babba yana tafiya ne cikin ƙasaitarshi yana me buɗe murfin.
Kan Jaddah ta ankara ya fara tuttulawa fauxiyyan ruwan sanyin, a firgice ta mike zaune tana jan numfashi sbd sanyin ruwan gashi a duniya ta tsani ruwa ya taɓa ta yanzu se tayi mura gashi ya zuba sossai a kanta da fuskanta, hawaye ta fara don sossai ta firgita sanyin ruwan kuma ya ratsa ta, ko a jikinshi cikin muryarshi me taushi yace
“wuce ki ɗauko!”
Mikewa tayi tana share hawayenta ta fito, ko da ta ɗauko abincin don tuna muguntan da ta mishi a ciki bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a gabanshi ta dire ta juya ta fice ya ja tsaki kan ya buɗe ya zuba kaɗan.
Spoon ya ɗauka sbd shi fa irin mutanen nan ne da ko tuwo zasu ci seda spoon, da bismillah ya kai loman abincin bakinshi Sam be kula da bala’in dake ciki ba seda ya haɗiye ya ɗaura na biyu a bakinshi.
A firgice ya dawo da abincin yana sakin tari kaman ze shiɗe, da sauri Jaddah ta dauki ruwa ta mika mishi ya amsa ya sha sede ba sassauci, tari yake kaman ze mutu gabaɗaya ya Haɗa zufa, idanunshi sun rine sun zama jajazir, da kyar ya samu tarin ya lafa se kuma gefen cikinshi ya riƙe.
Salati Jaddah take tayi tace
“na shiga uku! Yaji ne a abincin ko me?”
“Zaliha! Zaliha!!”
Zaliha ta fito da gudu ta zube a ƙasa Jaddah tace
“ke Zaliha kin saka attarugu a markaden kayan miyan nan ne?”
Girgiza kai tayi tace
“ban saka ba Jaddah ai kin ce yallaɓai Faizan baya so, wlh ko kaɗan ban saka ba”
Fauxa dake daga window tana ta dariyar cin nasara, kwanciya yayi a kan kujeran duk dauriyarshi ulcer na azabtar dashi shiyasa yake mugun kiyayewa.
Kaman wasa Seda Faizan yayi ciwo sossai kan ya samu sauƙi, kaman yadda itama saida tayi mura da zazzaɓi, kowa kuma Seda yayiwa Zaliha faɗan saka attarugu a abincinshi baiwar Allah gata da gaskiya sede babu yadda ta iya haka take shiru take bada hakuri.
Zaune yake gaban baba prof kanshi a ƙasa, baban ya tambayeshi jiki, cikin girmamawa ya amsa da da sauki Alhamdulillah, bayan shirun seconds kan yace.
“In Allah ya kaimu Laraba zan koma Abuja sbd akwai tafiyar da zamu yi da shugaban ƙasa”
Murmushi baba ya saki, a ko menene ya kan yi alfahari da wannan yaron nashi, Faizan ba irin normal pilots bane, yana daga cikin manyan pilots da idan ba da su ba shugaban kasa baya tafiya ko ina, bayan nan yana da hannayen jari da kampanunnuka ba daya ba ba biyu ba, Sam be dogara da aiki ɗaya ba, yaro ne shi me tsantsan biyayya ga iyayenshi, babban ɗabi’ar shi kuma kunya yanzu ya san akwai abunda yake son faɗa mishi ne sede yana jin nauyin maganan shine yake ta kwana kwana.
Baba yace
“masha Allah, Toh Allah ya kaimu ya nuna mana”
Yace
“Ameen baba!”
Baba ya kalleshi yace
“akwai wani abu ne kuma? Naga kaman kana son yin magana”
Kanshi ya dukar yana shafa kwantaccen Suman keyanshi yace
“dama akan maganan Fatima ne”
Murmushi baba ya fadada yace
“masha Allah, ka shirya auren kenan.. Toh tunda har ka furta wani satin in shaa Allah zamu je wurin mahaifinta mu tambayar maka ita, ai Fatima yarinyar kirki ce ta samu tarbiya me kyau daga Mahaifiyarta Allah ya tabbatar mana da alkhairi”
Da Ameen Faizan ya amsa, dukda maganan magana ne da ya kamata yayi farin ciki sede ko kaɗan be wani ji daaɗin hakan har chan ba, hira suka taɓa kadan da baban har baba Alhj ya shigo suka kara tattaunawa kan ya musu sallama ya fice.
Bayan ya koma aiki da kwanaki biyar aka tambayar mishi Fatima kuma an bashi sede an ja auren se ta gama secondary school in ya so se ta fara jami’a a gidanshi.
****
Kwance take kan gadonta jikinta yayi tsami da bugun da ya Farhan ya mata da magrib ɗin saboda bin wata ƙawarta da tayi gida bata dawo ba se da ana kiran sallahn magrib tun karfe 1:30, da farko basu so dukanta ba sede Sam ta ƙi faɗan inda taje hakan yasa ya Farhan da Ya Faraj suka zane ta har Seda Baba prof da za shi masallaci ya karɓe ta, Allah ya isa take ta ja tana cin alwashi kala kala a kansu, fa’iza dake ɗakin tun da suka dawo daga sallar isha’in bata ce mata komai ba…
Suna daga ɗakin Fatima ta shigo a wurin Aunty Amarya da Ammi dake bisa taburma a tsakar gidan suna cin Tuwon dare ta zauna, tace
“waii wallahi Aunty mammi na jin jiki, ciwon kafan nan baya mata ta daaɗi ɗan zaman da na yi na awanni a wurintan nan baki ga ba, komai se an yi mata”
Ammi tace
“Allah sarki, Allah dae ya bata lafiya ai kafa shine komai a jikin mutum, Allah dae ya sa kaffara ne”
Aunty Amarya tace
“Ameen Ammi, Fatima se ki dinga zuwa kina taya Asiya (ɗiyar Yayar mammi ɗin) kula da ita”
Fatima tace
“In shaa Allahu Aunty ai Mammi kaman uwa take a wurina, bari na shiga na dubo su Fa’iza mu ci abinci”
Mikewa tayi ta nufo ɗakin nasu, tana shiga suka Haɗa idanu da Faozia dake kallon kofan, ɗauke kai Fatima tayi yayinda Faozia tayi tsaki me karfi tace
“Fa’iza kin san Allah ko?”
Fa’iza tace
“me aka yi kike tambayana na san shi mana”
Faozia tace
“Daaɗina dake baki iya cin riban zance ba, ko da shike manta ma… Dama Tambayarki zan yi da munafukin ɓoye da na bayyane don Allah wanne ya fi?”
Fa’iza da bata fahimci zancen ta ba tace
“ai munafunci ko ya yake sunan shi munafunci kawai dae gwara wadda ze nuna maka a bayyane ka san dashi da wadda ze nuna maka Musa a fuska fir’auna a zuciya”
“sannan in zaka yi abu kayi don Allah da nufi ɗaya ni fa shiyasa bana son hulda da duk munafuki a duniya..” Fauza ta karasa
Fatima da ta tsaya kikam tana Kallonsu se hawaye ya fara kwaranya a fuskanta, Aunty ce ta fara shigowa ta buge Bakin Fa’iza tana cewa
“yanzu ƴar uwarki zaki Haɗa kai ana cusguna mata a gidan nan Fa’iza? Tana gayamin ina karyatata ashe da gaske ne? Fa’iza..!”
Ammi da ita ma ta shigo tayi kan Fauxa zata make tana cewa
“Ai ba ita zaki daka ba Auntynsu ita uwar iyayin nan zaki mara har se taga wuta..”
Dira Faozia tayi ta Ɗayan gefen kan Ammi ta zagayo ta fice da gudu harda bangaje Aunty goshinta ya ƙume da kofa salati duk suka saki ita kam ko waiwaye babu tayi sashen Mammi da gudu.
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.