Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Juyawa tayi ta koma tana mamakin kanta, for the first time kenan da aka yiwa Fauxa Abu ta ɗauke kai ta wuce, lallai abunda ya dameta ya dameta.
A kan gadon Jaddah ta sake yin masauki tare da tsunduma komar Tunaninta da ta san babu ranar gamawa, ɗagowa tayi jin alamun shigowar mutum.
“Ya Fadeelah!”
Ta kira sunan kawai kan ta maida idanunta ƙasa, babbar yayarta ce itace babba mace a ɗakin su, bata da wani shaƙuwa ko kusanci da kowa a gidan bayan Jaddah da Fa’iza wacce ta san a yanzu ko giyar wake fa’iza ta sha bazata zo kusa da ita ba.
karasowa Fadeelah tayi ta zauna gefenta tare da rike hannunta tace
“Fauxa! Kin ga yadda kika koma kuwa? Wannan anya fauxa ce kuwa? Wannan Fauzan da na sani bata taɓa zama na minti biyu shiru ba tare da ta nemi maganar wani ko faɗar wani ba? Fauxa nata ne..!”
Ɗago kai tayi tana dan ɓata fuska tace
“A’a yaya Fadeelah banda ɗan banza”
Dariya Fadeelah ta saki ita kuma fauza ta ɗan yi murmushi duk sun tuna sadda suke tare kirarinta kenan ‘Fauxa kowa naki banda ɗan banza’ ta kan faɗi hakan da proud musamman idan Fatima na kusa se gashi kaddarar Allah ya Haɗa su zama inuwa ɗaya a matsayin kishiyoyi.
“Bazaki tambayeni yaushe na zo ba? Ko ina yara?”
Ɗago idanu ta sake yi ta kalleta cikin gajiyawa tace
“Yaya stop been nice please ba haka muke ba”
Rike hannunta tayi tace
“I know, yanzu ina so mu fi haka.. Fauziyya ke yarinya ce har yanzu gashi Allah ya jarabceki da auren wadda kika ɗauka a matsayin Maƙiyi gabaɗaya rayuwarki ya kuma Haɗa ki da wacce tun shigowarta gidan nan matsayin agola baku taɓa kaunar juna ba a matsayin kishiya, ba Yola Zaku zauna ba bare ace akwai idanun Jaddah ko Ammi da mammi Abuja Zaku inda daga ku se ku you really need a guardian, please Fauxa ki girma and let me be a good sister I’ve supposed to be tun farko”
Hawaye masu zafi ne suka saukar mata tana kallon Fadeelah tace
“Ya Fadeelah kema kin yarda in hakura in zauna da Maƙiyina bayan kin san cewa duk mun tsani juna? Hakanan matarshi ko na minti biyu shiri be taɓa shiga tsakaninmu ba? Yaya Fadeelah wallahi wallahi ban taɓa aikata zina ba, meyasa kowa ze min wannan shedar alhali duk sharrin Faizan ne?”
Fadeelah ta sake rike hannunta tace
“Fauziyya kiyi Adu’a kinji? Ki sasaautawa ranki ki ɗauka cewa wannan aure shine alkhairinki kuma aljannarki karki manta abunda babba ya hango yaro fa baze hangonshi ba ko da kuwa ya hau dutse, yanzu iyayenmu duka fushi suke daku especially ma ke da kike da taurin zuciya, Fatima ta zama abar tausayi tunda tana chan kwance ta rasa cikin da ta kwallafawa rai”
Tace
“ya fadeela duk cikin munafurcinta ne, ni a duniya Ban taɓa ganin munafuki irin Fatima ba!”
Dafe kai Fadeela tayi, Fauza ta kau da kanta, Fadyaa ce ta shigo itama suka haɗu Suka yi ta nusar da ita, ɗan banzar taurin kai ne da ita kaman arnan fari, ga kafiyar tsiya da kyar suka samu tayi wanka ta ci wani abu, Fadyaa ta fice ta barsu da fadeela tana ta kokarin cigaba da bata shawarwari.
Walimar da za’a yi ranan har an yi niyyar fasawa Baba prof yace ayi tunda an yi gayyata, duk a Tunanin Faizan za’a fasa auren nan a gobe ganin abunda ya faru kuma har a yammacin da aka yi waliman Da seda mammi ta sa baki kan Amaryar ta fito Fatima na kwance a asibiti, Bayan ta farka tayi ta mishi kuka likitoci suka tabbatar mishi da jininta yayi mugun hawa duk abunda ya ɗaga mata hankali haka yayi kokarin kau dashi.
Da takardar ya dawo gida a Tunanin hakan ze zame mishi wata madafa wurin gujewa wannan kadararren aure sede hasashen shi be zama gaskiya ba, a washegarin da safe jama’a masu tarin yawa daga mabanbanta garuruwa ciki harda sarakuna da ƴan siyasa tare da manyan malaman ƙasa suka shaida auren
“FAIZAN IBRAHIM KAKA DA AMARYARSA FAUZIYYA SULAIMAN KAKA” kan sadaki dubu ɗari uku lakadan ba ajalan ba.
Sanarwan yayi daidai da tsayuwar bugun zuƙata masu yawa sede waenda suka bayyana a fili mutum uku ne, Chak numfashin Fauza ya ɗauke ta yanke jiki ta faɗi dama tun safiyar ranar kuka take, Faizan dake zaune kaman mutum mutumi yaji wani duhu ya rufeshi tsana da kyamar auren na ƙara lulluɓe shi.
Fatima da take daga cikin mota dawowar su kenan daga asibiti da mahaifiyarta ta fashe da wani matsanancin kuka me taɓa zuciya, lallai An zalunce ta kuma an ci amanar ta an nuna mata ita ɗin ba jinin GIDAN F ba ce, har Abada bazata manta wannan ba kuma tabbas an taɓa wutsiyar damisar da take bacci cikin matsanancin yunwa…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Biyu*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**Wannan shafi gabaɗayanta sadaukarwa ce gareki sister zainab Salis, hausawa suka ce yaba kyauta tukuici na ji daaɗi sossai da wannan kyauta Allah ya saka da alkhairi❤️**
Ba’a samu kan Fauza ba har Seda aka nemi doctor da kyar ta farfado, in ka ganta bazaka ce Fauzan Jaddah ba ce gabaɗaya ta firgice wadda hakan ya taɓa zuciyar Jaddah da Baba prof sossai.
Ya sani auren dole a musulunce haramun ne, sede yana da tabbacin gata ya musu wadda har abada ba zasu mance ba, watarana kuma in sun tuna zasu yi alfahari dashi su mishi Adu’a idan har be riski lokacin da rai ba, sannan sunan gidanshi ya riga ya fara ɓaci ta silar Fauziyya har hawaye ya zubar saboda wani da ya tare shi ya faɗa mishi magana marar daaɗin ji akan ɗiyar ƙanin nashi, sannan ya san halin Fauziyya ba me chanzuwa da sauki bane muddin bata gamu da abunda ya girgiza mata kwakwalwa ba, ko ta shiryu samun mijin da zata samu farin ciki da kaunar en uwanshi ze yi matukar wahala hankalinsu baze taɓa kwanciya da tayi ta musu yawon makaranta alhali sun san da cewa ga hanyar da ta ɗauka ba.
Duk zaune suke a babban parlorn nashi, in ka cire yara daga kan Fa’iza dake sa’ar Fauziyya zuwa kan auta Faazila babu wadda babu a wurin kuma tsab ya ɗauke su duka har ya bar fili me yawa saboda girman parlorn na Baba prof.
Gyaran murya yayi kan ya fara nasiha me ratsa jiki akan bin umarnin iyaye da kuma kyautata musu, daga nan ya ɗaura da haƙuri da irin girmansa har a wurin Mahalicci, bayan ya gama ya kira sunan Fatima.
Ɗago rinannun idanunta da suka haɗu da fuskanta suka kumbure tayi ta kalleshi kan ta maida kanta ƙasa tana bitar karatun da ba’a jima da fara ɗaura mata ba tace
“Na’am Baba”
Yace
“ke zan fara ba haƙuri Fatima, na san mun miki ba daidai ba kina zaman zamanki mun saka mijinki aure, amma ki sani mu ɗin ma bamu isa hakan ta kasance ba idan ba da yardar Allah da sahalewarsa ba, Ke da Fauziyya ƴan uwa ne waenda kuka tashi gida ɗaya ɗaki guda kusan gabaɗaya rayuwarku tare kuka yi shi, babu halin juna da baku sani ba hakan yasa nake jan kunnen ki da ki cigaba da rike Fauziyya a matsayin ƙanwarki, kiyi haƙuri da duk wasu halayen ta kaman yadda na san ki na kuma shede ki me dumbin haƙuri da kauda kai, to ki ƙara akan hakan, Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri’a dayyaba”