Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ya amsa a ladabce.
Baba Alhj yace
“tayi wani abu kuma ko?”
Baba prof yace
“tayi, amma wannan tsakaninsu ne, ba zamu saka baki ba sbd idan muka zama masu saka idanu da yawan magana akan rayuwar gidanshi to lallai zuciyarshi zata mace, mu zuba idanu kawai ya gyara gidanshi da kanshi idan ba ya nemi mu shigan bane babu anfanin shigan”
Duk sun gamsu da hakan prof mutum ne me hange sossai, sun fahimci dalilin shi na yin hakan don duk sauran yaran nashi ba idanu yake saka musu a Gidajensu ba Idan har ba sun zo gabanshi bane da matsala so na me ze saka akan su Faizan?
A ta ɓangaren shi kuma ya jima zaune zuciyarshi babu daaɗi, dukda be kwallafa rai a kan cikin ba amma akwai zafi ace ka rasa gudan jininka da kake fatan gani a duniya, abunda kuma ya fi bashi haushi yadda sautin Marin da yayi mata ya kasa barin kwalwanshi a kuma ranshi yake jin zafin hakan.
Mikewa yayi ya nemi izinin tafiya zuwa anjima ze dawo su kula da ita sossai pls, Dr yace ba damuwa ba ma lallai ta tashi yanzu ba don allurar ze jima yana aiki sbd bata samun cikakken hutawar ruhi dama chan.
A hankali yake murza sitiyarin motar yana amsa wayan Jafar a kasalance, yana faɗa mishi matarshi na asibitinsu tayi miscarriage, tausayinshi yasa Jafar yayi ta bashi baki murmushi kawai yake ɗan yi yana furta ba komai haka Allah ya tsara.
Bayan ya kashe be fi mintuna biyar ba se ga kiran Faisal wadda shi kuma lecturer ne a makarantar su Fatima, shima cikin tausayawa don a cikin abokanansu Faizan ne kaɗai be da yaro ko yarinya wacce zata kai shekaru bakwai sbd be yi aure da wuri ba, bayan yayi auren ma ga wani matsala nan na ɓarewar ciki.
Shima dai nuna mishi yayi haka Allah ya tsara.
A harabar gidan yayi parking ya sauka yana karewa gidan kallo kaman sabo ne a idanunshi, kofan motan kawai ya tura ya nufi ciki, a stairs na karshe ya tsaya yana kallon broken glasses dake zube a wurin, gabanshi ne ya faɗi ganin jini me yawa da har ya soma bushewa a wurin.
Da idanu yabi ɗigon ɗigon da jinin ya bi se ya kare kan kofar ta, yana haurawa husna dake zaune jugum ta tashi ta zo wurinshi da gudu kaman zata yi kuka tace
“uncle na tashi bacci na samu Aunty tana ta kuka daga karshe ma ta koreni tace in zo in kalli MBC waye ya daketa?”
Shafa kan yarinyar yayi yace
“Babu, na san ma ta daina husna je ki kalli cartoon ɗin bari na duba ta”
A hankali ya buɗe kofan ɗakin nata ya sanya kai ciki, jinin ya diga har gaban gadonta, tana kwance rub da ciki kafan na daga ƙasa ɗauke da kwalba me girma jini se diga yake har lokacin amma ita kam kuka kawai take yi, ita kanta ta rasa wannan kuka da take yi don tana da taurin zuciya ta rasa yadda aka yi abunda Faizan ya mata yayi mata zafi sossai da sossai.
“Subhanallah! Fauziyya?”
Ya ambaci sunanta yana riƙe kafan, zare kafan tayi daga hannunshi ta maida gefe tana me cigaba da kukanta, sake riƙe kafan yayi ta sake zamewa, guwiwanshi ɗaya ya saka kan gadon ya mirginota tare da ɗaga ta zaune se ta kara sautin kukanta cewa yake
“baki da hankali ne zaki zauna jininki na ta diga haka a ƙasa in ya kare fa?”
Ba tare da ta kalleshi ba tace
“se in mutu kowa ya huta tunda dama an tsane ni…..”
Cakkk magananta ya tsaya jin ya sungumeta gabaɗayanta tayi hanzarin saka hannayenta ta zagaye wuyanshi gudun kar ta faɗi….
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
22
Yana kallon tsakiyar idanunta da suka kumbura don kuka yace
“kika sake cewa tak zan sake ki ki faɗi se ki san ba’a sonki an tsaneki da kyau..”
Haushi maganan ya bata kawai ta sake sakar mishi kuka, idanunshi ya runtse kawai ya juya da ita a hannunshi suka nufi kofa.
“Baby taso ki zo”
Ya kira husna, da gudu ta bisu ita ce ta buɗe mishi kofa ya sanya Fauziyyan, ta shiga baya ita kuma, ya zagaye ya shiga ya ja tare da ficewa daga gidan, minti minti yake kallonta har suka isa asibiti bata bar kukan da take yi ɗin ba.
Nan ɗin ma saɓarta yayi zuwa office na Jafar husna na binshi a baya, a kan gadon office ɗin ya dire ta yana cewa
“washhh Allah, mutum kaman buhu”
Ɗago rinannun idanunta tayi ta zabga mishi harara ya ware mata nashi gabaɗaya alamar ni kike harara? Se tayi saurin maida kanta ƙasa, idanunshi na kan kumatunta da hannunshi ya kwanta har Jafar ya shigo daga ward.
“Subhanallah kai kam yau gidanka da alama ba sa’a kuka tashi, garin yaya ta taka kwalba haka kuma kuka barshi har kafan ya kumbura ba’a zo asibiti ba Faizan?”
Yana ɗauke idanu daga kanta yace
“bayan mun zo da Fatima ne ta taka so saida kuma na koma na sameta hakan”
Yace
“sannu Amaryarmu”
Kai kawai ta ɗaga mishi.
Cikin sanyin muryarta tace
“Ina yini”
Ya amsa yana isowa da kayan aikinshi wurin gadon, se da ya gama kallon kafan kan yace za’a mata allura kan ya fara taɓa kafar, nan fa idanunta suka raina fata, duk bala’inta in aka zo fagen allura tsoron shi take.
Daga yadda reaction ɗin ta ya nuna ya gane tana tsoron Allurar, har aka gama Haɗawa ya matso yana cewa ta gyara idanunta na kan allurar yayinda gogan kuma nashi ke kanta, idanunta na da kyau a kowani yanayi…
Girgiza kai tayi muryarta har yana rawa tace a cire haka ba se an yi allura ba, a hankali taji shigar tattausan hannunshi cikin nata, Ɗayan kuma ya saka ya rungumo ta jikinshi, fuskanta ta binne bisa kirjinshi har yana jin hucin numfashin ta wadda a take gabaɗaya tsikar jikinshi suka tashi, har aka yi Allurar dukansu basu farga ba saida Jafar yace
“Romeo and Juliet an gama Zaku iya ɗagowa”
Da sauri ya saketa yana ɗan matsawa ya zabgawa Jafar harara, ita kuma ta dukar da kanta.
An sha gumurzu kan aka cire kwalban tayi kuka sossai wadda har saida yaji a ƙasan ranshi be kyauta ba, bayan an gama ya ɗan Harare ta yace
“taɓararriya kawai”
Bakinta ta tura mishi ya kai hannu kaman ze ɗalle mata bakin tayi saurin saka duka hannunta biyu ta tare tana zare idanu wadda ya saka shi sakin murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko ɗaya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura.
Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa.
Ita kuwa tana zuwa motan ta buɗe baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya ɗauke ta.
Haka ya sa hannu ya ɗauke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buɗe mai gaba ya sanyata.
Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace
“Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?”
Yana gyara Fauza yace
“kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls”