Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Haka dae tayi wanka ta zo ta kwanta ko abinci bata nema ba zuciyar ta fal tunani, washegari da safe bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar taji alamun tashin mota, da sauri ta miƙe taje jikin window se ta hangi motar shi na fita, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta zauna da gaske fushi yayi? Ta tambayi kanta don ba zata Iya tuna sadda ya fita be gayamata ba tunda suka ɗan fara shiri.
Gari yayi haske taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin jalbab ɗinta dogo har ƙasa don tana da lectures, fitowa tayi bayan ta sha cereal ta zuba chocolates masu yawa a jakan bayanta, Fatima ta gani zaune tana karyawa.
Kaman ba zata mata magana ba se kuma tace
“mun tashi lafiya?”
Ko kallonta Fatima bata yi ba, zama tayi tana jiran ta ko don ta san tana jiran ta ne ita kuwa ta fara jan lokaci, ganin zata ɓata mata lokaci har a shiga lectures yasa ta miƙe ta fice.
Mai gadi ya gaida ta yana buɗe mata gate ta taka da kafa har ta samu taxi ta ɗauki shata ta wuce school.
Se karfe huɗu ta dawo gidan nan ma da taxi don bata ga Fatima ba, Seda tayi sallah ta zo ta shiga kitchen ta fara girki sanin itace yau da girkin, tuwo tayi mishi na doya da miyar ɗanyen kifi bayan ta gama taje tayi wanka tare da sallar magrib ta shirya cikin kananun kaya, ba karamin kyau tayi ba tayi isha kan ta fito ta zauna a parlorn saman Dukda bata ji motsin shi ba.
Se a lokacin Fatima ta shigo basu tankawa juna ba, ita dae Fatima ganinta yasa ta san bata san mijin da ake yiwa kwainanen baya ma ƙasar ba, dariya ta sheke dashi tana cewa
“lallai kuwa za’a yi jiran gawon shanu”
Tana kai nan tayi wucewarta ciki, ganin har karfe tara be shigo ba yasa tayi Tunanin ko baya ƙasar, ranta dae ba daaɗi kaman yadda tun safe yake har Afnan take tambayarta tace babu komai, yau gabaɗaya abu mai nauyi be shiga cikinta ba, tuwon ta dibi ɗan kaɗan ta ci kan ta tattara taje ta adana a frigde daga nan ta haura tayi shirin kwanciya ta kwanta.
Washegari bata yi breakfast ba miyan kifin ta yi microwaving ta ci da bread, yau ma bata jira Fatima ba tayi ficewarta yau ma dae haka ta kashe ranar da tunani, lectures ɗin ma bata wani fahimta..
A kwana na ukun har kuka tayi, ta rasa gabaɗaya me ke damunta da fushin shi, da a gidansu ne da yanzu in duka ne an daketa an wuce wurin amma shi ba duka ba zagi kawai ya ɓace mata ba tare da ta san inda yayi ba alhali yana fushi da ita.
Hadari ne sossai ya haɗe garin har ana iska, Afnan ta riga ta wuce ita kuma tana tsaye tana neman taxi da sauri ta sanya hannu ganin motar Fatima amma ko bata tsaya ba tayi wucewarta kuma ta tabbatar ta ganta ba bata ganta ba, da kyar ta samu wani taxi Dukda ya tsula mata kuɗi bata damu ba ta shige da sauri sbd ita bata son ruwa ya taɓa ta, ko yaya ya jiƙata se tayi mugun zazzaɓi.
***
Karfe shidda ya iso gidan yayi parking motan shi da dama Airport ya kan bari yayi tafiyar shi, Gaisawa suka yi da gate man kan ya wuce ciki yana kallon motar Fatima dake nuna alamun bata jima da shigowa ba.
Gidan ya shiga yana jin wani kewa chan ƙasan ranshi da duk yadda yayi kokarin dannewa ya ƙi dannuwa, lumshe idanu yayi ya buɗe a sadda ya shaki sassanyar turaren wutan da ta kan yi anfani dashi wa gidan, a natse ya haura yana jin yadda aka tsuge da ruwan kaman da bakin ƙwarya.
Ɗakin Fatima ya fara shiga tana ganinshi cikin farin ciki ta tare shi tana mishi sannu da dawowa, ya amsa fuskanshi a sake kan yace bari ya duba Fauza se yaje yayi wanka.
Tace
“Ai ina ga bata dawo ba fa…”
“Bata dawo ba?” Ya watsa mata tambayar cikin mamaki.
Kanta ta mayar ƙasa tace
“eh bata dawo ba don ban ji shigowarta ba”
Yace
“ban gane ba, ina ce tare kuke tafiya ku dawo? Ya aka yi ke kike gida ita bata nan? Me ze ajiye ta a waje har an yi magrib?”
Tace
“ni dae wlh ban sani ba, abunda na sani dae tunda ka tafi bata sake tsayawa mun tafi tare ba taxi take fita ta hau haka dashi take dawowa Dukda nayi kokarin jan hankalinta akan baka son ɗabi’ar shine ma musababbin da yasa ka saya min mota amma taki saurare”
Be tanka ba sbd yadda ya sake jin sabon ɓacin rai na rufe shi a kanta, duk yadda yake kokari akan yarinyar nan me yasa take so ta fara bashi matsala? Sau nawa ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi? Ɗakinta ya wuce kamshin ta na tashi a ɗakin wadda ya dawo mishi da sabon kewanta kaman yadda ya kashe kwanaki biyun cikin kewar nata ko abincin kirki bai iya ci.
A balcony ɗinta ya tsaya dake shine ke facing gate, ya rasa hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, sheɗan ke ta wassafa mishi kila tana chan da Zubair tunda har ta fara ambatarshi, hangar taxi yayi ya sauke ta, ba lema hannunta hakan yasa cikin hanzari ta iso gate ɗin ta fara bugawa saide gate man ɗin kaman baya kusa don baya jinta, ta kai mintuna biyu tsaye cikin ruwan tana knocking da ƙarfi sede ƙaran ruwa ya hana gate man ɗin ji, ya so ya kyale ta ruwan yayi ta jiƙata se kuma ya ga baze iya ba.
Da sauri ya juya ya nufi fita ganin ta juya itama ta bar gate ɗin da sauri sauri, da hanzari ya buɗe gate ɗin ya fara duba ta, chan ya hangota tana tafiya tana dube dube ko zata samu inda zata fake kan ruwan ya tsagaita..
Sam bata san da isowar mutum ba se ji tayi an ɗaura mata wani suede me kauri wadda a take ta dena jin Sauƙar ruwan jikinta, a hankali ta ɗaga kai se suka Haɗa idanu ruwan na zuba a jikinshi sossai.
“Yaa…”
Be bata daman magana ba ya riƙo hannunta suka juya suka yi gida, a kofan ɗakinta ya saketa ba tare da ya bi ta kan suede ɗinshi ba ya shige dakinshi.
Ta ɗan jima tsaye a wurin kan ta shige ta cire suede din ta ajiye ta wuce toilet ta cire kayanta da ya jike gabaɗaya ta hada ruwa me zafi sossai tayi wanka, a ɗakin ta Haɗa tea me kauri da zafi ta sha jin jikinta ya fara rawa alamar zazzaɓi.
Da kyar ta iya gabatar da sallah kan ta hau gado ta ja bargo ta shige tana rawar dari.
Yayi wanka shima ya sauya kaya ya fito ya duba Fatima yace ta sama mai wani abu marar nauyi don yana jin yunwa, ranta fal farin ciki sanin yayi fushi da fauza ne tunda girkin ta ne amma ya saka ita tayi mishi.
Kitchen ta shiga ta sama mai abinci yana zaune a parlor yana kallon Tvc news ta shigo ta ajiye mai, kallon kofan Fauza yayi kan ya maida kan abincinshi ya fara ci yana Tunanin me ya hanata fitowa ta nemi wani abu ta ci?
Har ya gama ci suna tare da Fatima, tana ta kokarin jan hankalinshi sede idanunshi ne kawai gareta, tana tattare kwanukan ya miƙe ya nufi ɗakin Fauza ɗin.
Kwance ya tarar da ita tana rawar ɗari sossai, yaye bargo yayi ya taɓa gefen wuyanta wani irin zafi jikinta yayi da har yayi saurin zare hannunshi, da kyar ta buɗe idanu ta kalleshi..
Harara ya zabga mata, kan yayi tsaki ya wuce toilet ɗinta towel ya samo da ruwa ya zo ya karasa yaye bargon yana ɗauke idanunshi daga kan santala santalan cinyoyinta da suka bayyana, ɗagota yayi ya fara saka Towel nan a ruwa yana shafa mata, wani irin numfashi take saukewa wadda ke rikirkitashi ganin ruwan baze Sauƙar mata da zazzaɓin ba gashi ta fara mishi kananun kukan fita hayyaci ya sa ya rufe ta da faɗa don abubuwa dayawa ne suka haɗu mai.
Sossai yake mata faɗan abubuwan da ta aika ta ɗin, harda taurin kanta take shirin dawo mai dashi to baze ɗauka ba, shi ba lusarin namiji bane da ze ke gindaya mata sharudda tana tsallakewa he could remember vividly yadda ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi amma me ta aikata? Har tana tuna wani katon gardi ɗan shaye shaye cikin gidanshi.