Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Be ƙi ba haka suka dawo cikin garin Yola wadda ya kasance dawowar kenan, wasa wasa Ibrahim yayi wani irin kafuwa sbd mutum ne me zafin nema Sam baya kwanciya kawai yaji daaɗi, a tafiyan su wani kauye ne na mayo belwa ya samo Aisha(Mammi) gani ɗaya ya mata yaji nan duniya itace macen da ta dace dashi ko da ya dawo kan yayi magana Sulaiman ya tare shi da zancen ya samu mata, shima nan ya faɗa musu yayi mata farin ciki wurin jadda harda hawaye.

fili babba ya saya ya samu architecture ya tsara mishi yadda yake so gidansu ya kasance na dindin din kuɗi ya zube aka soma aiki, wata uku aka gama komai sashe uku ne se masallaci da islamiyya babba daga jikin gidan, a lokacin aka yi bukin su.

Yadda faɗan boko haram ke tsamari a Maiduguri yasa yake ta sayan kananun Gidaje a unguwan yana saka ƴan uwa da abokan arziki kusan almost rabin unguwan shi ya mallaka musu Gidajen su kuma in har ya kiraka akan ka dawo yola to wannan gida naka ne halak malak.

Wani irin buɗi yake samu sbd alkhairanshi dake da matukar yawa, basu shekara biyu da Mammi ba ta haifi Yaron su na farko da ya ci suna FAIZAN(Genorous/Me karamci ko kuma beneficence wato me aikata mai kyau), bayan wata uku da haihuwar Faizan ruqayya(Matar Sulaiman) itama ta haihu ta samu ɗiya mace wacce ta ci sunan Fadeelah(Virtuous wato tagari).

Ba’a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo da ake kira Sunkani, itama Fulani ce ba’a ɓata lokaci ba aka yi bukin nasu, shekaranta ɗaya Mammi kaman yadda Faizan ke kira ta sake haihuwar ɗa namiji Faahim(me ilimi or mai fahimta).

Ammi itama ta sake haihuwar Falaq(Ketowar Alfijir), Anan hankalin Ruqayya ya soma tashi, dama wani irin zama suke yi marar daaɗi da Maa wadda musabbabin abun Ruqayya ce, tunda ta saka kafa gidan ta fahimci nisan dake tsakanin Ibrahim da Sulaiman kaman nisan dake tsakanin sama da ƙasa ne, wai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau.

Bata kara shiga tunani ba seda taga irin girmamawar Sulaiman ga Ibrahim kai tsaye zaka iya cewa matsayin mahaifi ya bashi don ko ratar dake tsakaninsu rata ne me girma, randa ta haihu kuwa taga Sulaiman ya ɗauki yarinyar musamman ya kaiwa Ibrahim shi ya mata huɗuba ya sa mata suna alhali ta riga ta faɗawa Sulaiman sunan da take so a sawa yarinyar, ba karamin rikici suka yi ba akan sunan Fadeelah sede Sulaiman ya fi karfinta haka ta bari, sede daga ranar maganan arziki ita da Mammi babu dama chan sama sama ne, se kuma gashi Mammi na jera maza Ita kuma tana jera mata alhali Ibrahim da Sulaiman basu bambanta dukiyar su ba.

Zaman doya da manja ake yi a gidan har Amaryar baba prof itama ta haihu ta samu mace, Falusha(Haske).

Bayan haihuwan Falusha Baba prof yayi tafiya Maiduguri inda ya dawo da Auren Zainab, ba karamin rikici aka yi da Hussaina ba kan ta saduda, Mammi kam fatan alkhairi kawai tayi mishi, a lokacin ma tana da tsohon ciki inda ta haifi Fahad(Damisa) ba’a ɗau lokaci ba Ammi ta sake haihuwan Fadyaa(sadaukarwa).

Hussaina da yaran suke kira Maami ta sake haifan Farrah(Florence nau’in haske), har lokacin zainab bata haihu ba, Baba prof ya karo aure cikin ƴan gudun Hijira Sakinah itama barebari ce usul, a tare suka fara haihuwa da Zainab wacce su Faizan ke kira Umma, ita ta samu Faraj(cure, waraka kenan) yayinda sakina ta samu Farzan(me wayau).

Daga nan dukkansu basu sake haihuwa ba seda aka ɗau lokaci Ammi kuwa ta haifi maza biyu a tsakani Farhan(farin ciki) da Faris (horseman).

A lokacin Baba prof ya kara sashe a gefe da masallaci sbd matasan yaran da suka fara tasowa, Mammi ta sake haihuwar Farida(ta musamman ko lu’ulu’u me daraja) daga nan har yau bata sake haihuwa ba.
Bayan nan Sakinah (umma) ta sake haihuwan Farhuddeen(farin cikin addini).
Sulaiman ya ƙara aure inda ya auri sumayya ta zo gidan da ƴarta Fatima, sumayya sun haihu tare da Ammi(ruqayya), Ammi ta haifi Fauza (triumphant wato nasara) yayinda sumayya ta haifi fa’iza (Gain, wato samu).

Bayan su Fauxa, sumayya ta kara yara uku Fadiyah(me kyau), Fakiha(fruits) se Faazila(gaskiya) su kenan yaran gidan karan katakap.

Mammi na da huɗu Faizan, Faahim, Fahad da farida.
Maami na da biyu Falusha da Farrah.
Umma na da guda biyu Faraj da Farhuddeen.
Daada na da guda ɗaya Farzan.
Gabaɗaya yaran na Baba prof guda 9 ne Allah ya bashi.

Se Alhaji wato Sulaiman.
Ammi na da shidda Fadeelah, Falaq, Fadyaa, Farhan, Faris se Fauxa.
Aunty Amarya na da huɗu Fa’iza, fadhiya,Fakiha da Faazila.
Gaɓadaya yaranshi 10.

Gidan na da wani irin dokoki ne wadda duk tsari na addini ne, yaran kuwa akwai matukar shakuwa, tausayi da kauna irin ta ƴan uwantaka a tsakaninsu Baba prof baya wasa da tarbiyar su ko na miskala zarratin, duk kuma abunda ze shimfiɗa hannu bibbiyu Alhaji ke karɓa.

Ya ƙara samun wani girma ne a unguwan sbd yadda baya banbance ƴaƴanshi da na dangin shi Dukda ba komai yake da iko akai ba sede fa ya san duka yaran don dole a islamiyya ɗinshi zasu yi karatu kuma shi da kanshi yake koyar dasu sbd dumbin falala dake cikin koyarwa da yara addini babban sadaqatul jariya ce wacce bata gushewa har se me wannan ilimi ya gushe idan kuma akwai wadda ya koya daga wurin ɗaya haka ze yi ta gudana har illa ma shaa Allah.

Wannan al’ada itace zaɓarwa yara abokan zama masu nagarta, kawai ze kira ka a waya akan Zaku yi baƙo ze zo wurin wacce kaza, ko kuma wane kaza na gidan ka yaje wurin wacce kaza na gidan wane, a haka ya Haɗa wani irin bond me girma tsakanin kaɓilarsu ta barebari da suke nan unguwar, kuma duk zaɓin shi suna alfahari dashi sbd baya taɓa zaɓin banza.

Mata da mazan gidanshi kan yi karatu har matakin degree ma idan har maneminki be fito ba, sbd ya san muhimmancin karatu ya kuma san karatu wani makami ne da zaka barwa yaro wadda ba ze taɓa tagayyara ba hakan ne dalilin da ya sa ko maneminki ya fito baki fara makarantar gaba da jami’a ba dole akwai yarjejeniyar ci gaban karatun ki don gudun halin rayuwa.

Faizan pilot ne wato matuƙin jirgi wadda aka fi sani da Captain Faizan matashi me jini a jika, kyaun fuska da na hali, ilimi both Islamic and western, his father’s favorite, the first born to the house of F, har yau Allah be yi yayi aure ba kaman ba Baba prof ne ya haife shi ba.

Fadeelah tana auren wani businessman suna zama a Australia with kids.

Faahim Navy ne, an aura mishi Fadyaa suna da ƴaƴa biyu. Auren da saida aka kai ruwa rana da Ammi ta saduda.

Falaq har yau bata yi aure ba sbd rashin lafiya da take fama dashi.

Fahad na aiki da inland revenue with a wife and a kid.

Farida tayi aure some months ago with a costume officer suna zaune Lagos.

Falusha and Farrah duk tare aka yi aurensu su biyun duk suna yola suna auren ma’aikatan Gomnati.

Faraj, Farhan da Farzan duk suna final year of their studies a Apti American University mabanbantan courses.

Farhuddeen da Faris suna SS3

Fatima na SS2

Fauxa da fa’iza na SS1

Fadhiya js1, Fakiha pri5 and Faazila pri3.

Tou readers ya kuka ji GIDAN F? A tunaninku duk wani haɗin kai da kaunar juna da zaman lumana dake wakana a wannan gida me cike da addini me ɗaurewa ne har abada? Sheɗan ze iya barin ɗaurewar wannan haɗin kan da kaunar kuwa? Akwai wasu abubuwan da ban sa cikin tarihin gidan ba a hankali a hankali Zaku fahimta in shaa Allah, mu je zuwa‍♀️‍♀️‍♀️.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected