Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Sanye da doguwar hijabi har ƙasa ta shigo gidan, idan ba ka mata farin sani ba bazaka gane ta ba, tayi baƙi sossai ta rame kaman ba Fatima ba, kai tsaye inda aka yi decorating don taron sunan ta karasa, a gaban Fauziyya kawai ta zube tare da kama kafafunta ta fashe da wani irin kuka da ya ja hankalin mutane masu yawa.

Faizan yayi saurin mikewa yana kallonta, Fauza ta ganeta tayi saurin tare shi ganin ze taɓa ta don rabata da jikinta.

“Fatima???”

Kowa sunan ya maimaita yana kallonta da mamakin yadda ta koma

“Don darajar Allah ku yafemana Fauziyya, ke da Ammi da mammi ku dubi Allah ku yafe mana ko zamu ga da kyau, Don Allah ku yafewa Auntyna ta tafi tana rokar gafararku sede babu halin zuwa nan ɗin…”

“Ta rasu??”

Fa’iza tayi tambayar idanunta duka waje

Kuka me ciwo Fatima ta cigaba da yi wadda ya saka su jin tausayinta.

“Ta rasu Fa’iza, ta ce don Allah in ce kuma ku yafe mata, ku rokar mata Allah gafara, ta kamu da cutar dajin kwakwalwa ba tare da mun sani ba aka mata allura, tayi jinya me tsawo wadda kan ta rasu seda kamannin fuskanta ya sauya, fatar fuskanta da naman haka suke zazzagowa suna zub…..”
Kuka ne ya kwace mata, fa’iza ma nayi.

Fauza seda ta zub da hawaye jin irin wahalar da Aunty ta sha kan mutuwa lallai wadda yace ruwan wani baze tafasa ba nashi ko zafi baze yi ba, yanzu wa gari ya waya? Arziki, kuɗi babu abunda baya jawowa.. Allah ya tsarremu da son zuciya.

Sun ce sun yafe sauran ita da ubangijinta, Fatima tayi ta godiya ko da Baba prof ya tambayi ina take zaune ita nan ta gaya musu ai Aunty ɓoye iyayenta tayi suna fama da baƙar rayuwa, kilan da ta taimaka musu sun zama wasu abu kan barinta gidan Sulaiman ɗin da sun iya sun Haɗa mata kudin aikin da ya gagara har ta mutu da azabar ciwon cancer.

Ta sheda musu itama zata koma gidan nata mahaifin dama Aunty ne taki sam ta bari su wani shaku sbd burinta a gidan prof ɗin..

Kyauta me yawa suka mata, Faizan dae be ce komai ba, se Kallonshi take da yaranshi rungume kirjinshi tana jin yadda azabar sonshi ke huda zuciyarta sede ya ta iya ba komai kake so kake samu ba.

***

Yau suke gama wanka, ita da su faazila suka fita zagayen arba’in sun zazzaga wuraren en uwa da abokan arziki, sun zo ta wurin gidansu Sakina tayi parking motar ta sauka tana tambayar me gadi mutanen gidan.

Yace ai iyayen sakina sun rasu se ita kaɗai da masu aiki, itama ta tafi islamiyya ne.

“Islamiyya”
Fauza ta maimaita.

Bata gama rufe baki ba se ga Sakina ta taho ita da wani a gefenta kanta ƙasa hannunta rungume da Alqur’ani.

Ɗaga kan da zata yi se taga Fauza da sauri suka rungume juna sakina na fashewa da kuka sossai, Gaisawa suka yi da mutumin nan kan ta cewa su Faazila su karasa ciki.

Sakina ta cika musu gaba da abun motsa baki kan ta zauna tana ta kallon su Arwa yaran bul bul gwanin sha’awa kaman yaran labarawa.

“Sakina ina rahama?”
Ta tambaya, Sakina na kuka tace

“Fauzaa na ji tsoron Allah naji tsoron rayuwa, na rasa iyayena a hatsarin jirgin ruwa hakan me makon ya saka min natsuwa Dukda kaɗaici da rashin wani dangi yasa na sake samun duniya yadda na so nake yi, Fauziyya mun tafi Gombe kusan mu shidda muna dawowa muka haɗu da wani mummunan hatsari, da idanu na na ga mutuwa Fauziyya, kowa ya mutu a gabana har rahama… Tun daga sannan tsoron Allah ya saukarmin na fara tuba.

Kaɗaici ya min yawa, se masu aikin gidanmu da da nake wulakantawa suka zama en uwana, su suka sa na shiga islamiyya yanzu haka wadda kuka gaisa dashi malami na ne kuma shi zan aura”

Ajiyar zuciya me nauyi Fauza ta sauki, Sakina ta nemi yafiyar ta bisa hanyar da suka jefa ta a baya, tace ta yafe kuma in shaa Allah auren ya tashi zata halarta.

kaman kar su Rabu bayan sun yi exchanging numbers Fauza ta wuce gida, sati ɗaya bayan nan ya zo ya ɗaukesu da wata da Jaddah ta sama mata me taya ta renon yara suka wuce Abuja.

Maternity leave ɗinta ya riga ya kare so makaranta kawai ta koma, tana kuma kula da yaranta da mijinta a gefe guda.

***

Bayan tsawon lokaci.

Cikin bacci yaji barinta jikinshi ya zata ma bayi zata shiga se yaga ta nufi kofa ta buɗe ta fice.

Mikewa yayi yabi bayanta, ƙasa gabaɗaya ta sauƙa a dining ta zauna bayan ta ɗauko ruwa ta zare bowl ta Haɗa cornflakes ta fara sha.

Daga saman stairs ya tsaya yana kallonta da mamaki karfe biyun dare?

Zuwa yayi ya zauna gefenta tare da d’aura hannunshi d’aya kan ha’barshi zuwa bakinshi ya karkace sossai yana kallonta ba tare da ta sani ba.

Tayi nisa wurin shan cornflakes d’inta sbd yunwar da take ji d’aga kan da zatayi kawai ta ganshi bazata hakan ya mugun Bata tsoro tayi Baya luuuu zata fad’i daga ita har kujeran yayi azamar tarbota tare da kurawa firgitattun idanunta ido, a hankali ya mayar kan lips d’inta da suke d’an bud’e kad’an sbd tsorata.

Daidaitata yayi yana cewa
“Easy precious ni ne”

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta shagwaɓe tace
“Abban twins ka tsorata ni wlh”

Yace
“sorrie! Ina mamakin yadda daaɗin cornflakes ya sa kika kasa jin zuwana ma gabaɗaya”

Cigaba da shan kayanta tayi ba tare da tace komai ba, ya jira ta gama kan suka koma seda suka leƙa yaransu da yanzu suke shekara da wata shidda babu abunda basa ci babu kuma inda basa zuwa kan suka koma ɗaki.

Da asuba kan tayi sallah seda ta sake shan cornflakes shi dae be ce komai ba, suna breakfast ita cornflakes take sha.

“Anya lafiya Fauza?”

Tace
“me ka gani?”

Yace
“shan cornflakes ɗin nan haka kawai nake jin ba ƙalau ba”

Gabanta ne ya faɗi, ita dama ta ɗauko Ammi ne in tana shayarwa bata period to haka itama bata taɓa yi ba tun samun cikin su, goyo me tsafta ake cewa ko, to amma kwata kwata en biyu yaushe suka girma? Gashi karatun ta ya ɗauko gangara yanzu duk bata da wani lokaci na kanta.

Bata ce komai ba, bayan ta sallami su twins ta fito da niyar wucewa school ta biya asibiti, abunda take tsoro ne ya tabbata ciki take dashi na tsawon sati biyar.

Kasa zuwa school ɗin tayi ta komo gida ta shige ɗaki ta fara kuka, yana tsaye balcony ɗinshi ya ga shigowar motan ta shiru shiru ya dauka mantuwa tayi sede be ga fitar ta ba ya sa ya fita ya nufi ɗakinta.

Hankalinshi ya tashi ganin tana kuka ya hau lallaɓata da kyar ta ce mishi wai wani ciki ne da ita.

Da tsantsar mamaki yake kallonta
“saboda kina da ciki shine kike kuka Fauziyya?”

“Yaya ka kuwa san wahalar renon ciki da nakudar? Kwata kwata yaushe na haifi twins? Ga school ni dae wlh ba zan iya b….”

“Kul Fauziyya!!”
Ya daka mata tsawa.

“Karki kuskura wlh karki fara kawo koma menene yake ranki ki binne shi, ciki ne ya riga ya shiga don haka se kin haife shi”
Yana kai nan ya miƙe ya fice yana banko mata kofar.

Sossai tayi kuka kan bacci ya ɗauke ta.
Gabaɗaya ranar ta fita harkar su twins ɗin da baban ko fita daga ɗakinta ta ƙi yi, tana ji yadda suke kiran
“mommy! Mommy!!”
Bata ko kula su ba seda daddyn nasu ya fita daga nashi ɗakin ya ɗaukesu yayi nashi dasu.

Wasa wasa seda suka kwana uku a haka, bata shiga harkarsu banda kuncin rai da ta sawa kanta ko makarantar bata zuwa, bata taɓa kai hannu jikin yaran ba amma a tsakanin seda ta make Arwa wadda ya sake saka matsala tsaninsu seda yayi kaman itama ze daketa.

Jafar yake faɗawa matsalar tashi don basu taɓa samun damuwa haka ba, wlh ko bacci baya iya yi tunda suka raba makwanci, Jafar ya kirata a waya ya mata nasiha sede be wani shige ta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected