Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

“Don Allah yaya ka ɗauke kifin chan bata son gani”

Taimaka mata yayi ta zauna ya karasa ya ɗauke kifin zuwa kitchen yana mamaki.

Hannunta ya riƙe yace
“baki da lafiya ne shine baki faɗamin ba? Tun yaushe? Me ke damunki?”

Tace
“lafiya ta ƙalau kawai gajiya ce se kuma kifin nan bana son warin”

Yace
“wari kuma? Amma I thought kifi da nama na daga cikin abubuwan da kike so?”

Kai ta gyaɗa, yana ta kallonta se kuma yace
“wait..! Fauza”
Da sauri ta kalleshi, rabon da ya kirata da sunanta tun a yola, tace
“Na’am”

“when last kika ga jininki?”

Idanunta na kanshi ta tafi tunani, da sauri ta sanya hannu a kan cikinta tana cewa
“could it be possible?”

Yace
“sure, When last kika yi period?”

A hankali tace
“tun kan in bar nan in tafi yola, satin da ya kamata na fara kuka je kai da Fatima”

Ai da wuri ya tafi ya ɗauko mata hijab ya zo ya kama hannunta suka yi asibiti, bayan dogon gwaje gwaje Jafar ya musu albishir da ciki na tsawon wata uku bata taɓa sani ba se ranar, farin cikin da suka shiga baya misaltuwa barin ma shi da har Seda yayi hawaye, ze kira gida tayi saurin kwashe wayar tana shagwaɓewa.

“Eyyaaa yaya karka gayamusu don Allah”

Yace
“Meyasa bayan abun farin ciki ne ya same mu love?”

Tace
“Ai to ba zasu san abunda aka yi ba, ni dae bana so”
Dariya sossai ya saki, Fauza har yanzu taɓara irin na yara na damunta.

“Fine my baby mama, ba zan faɗa ba”

Daga asibiti yawon neman abunda zata ci suka fara, a wani tsadadden restaurant suka yada zango a gabansu aka ajiye abun gashi yana gasa mata nama tana ci, ta ci sossai kan aka kawo mata milkshake ta jingina da jikinshi.

Kwanciya tayi jikinshi tare da kai mishi cup d’in bakinshi yayi sipping ta dawor dashi nata ta sha tana sake murmushi.

Rayuwa ta sake yi musu daaɗi sossai, a week after suka fara exams ya ɗan yi tafiya bayan ya dawo lokacin ta gama ya shirya musu tafiya, Allah ya sa cikin nata ba wani laulayi me wahalarwa, ƙasar Greece suka tafi suka baje kolin soyayyarsu a chan, sati uku suka yi a chan kan suka wuce Australia se ganinsu Ya fadeela tayi.

Sun matukar burge ta soyayyarsu ya tafi da ita ga wani kyau da kowannensu ya kara da girma alamar hankalinsu kwance yake, daga nan suka wuce wurin Ya fadyaa husna tayi ta murnan ganinsu suma kwana biyu suka musu suka tattara suka dawo sbd hutun ta ya kare.

BAYAN WATA HUƊU

A hankali take sauƙowa daga jirgin sbd yadda cikinta yayi wani mugun girma Dukda kwata kwata wata bakwai kenan, kafafunta da kyar take ɗaga su sanye da wani bubu Abaya me stones ta yafa gyalen, yana rike da jakanta a hannu daya yana rike da ita suka nufi farhan dake ta zabga murmushin ganinsu.

Se kallonta ake sbd Fauza fa ciki be hanata gayunta ba, wani lokacin in su firdausi na tsokanarta ta kan ce ciki ne fa da ita ba hauka ta soma ba, suyi ta mata dariya, shi karan kanshi ya kan yaba kokarin ta Dukda kankantar shekarunta bata taɓa gazawa a kanshi ba daga cimarshi, tsabtarshi da hakkinshi babu abunda ta dena ga karatu.

Gidan cike yake da mutane sbd yaune ake walimar Fa’iza da Faraj se Falaq da itama se yanzu lokacin yayi, a haka suka ratso mutane duk yadda take sunne kai shi kam ko a jikinshi se kara mannata da jikinshi yake har parlorn Jaddah.

Farin ciki ne ya cika ta fall ko a hira basu san da cikin ba se ganin abu kawai suka yi, daga Amminta har mammi ba karamin farin cikin ganinta haka suka yi ba hankali kwance, kar iyayenta mazan su ji labari.

Duk yadda ta ci Burin bukin se gashi ita a zaune tayi komai sbd kafafunta da suka ƙi, har aka sada su da gidajensu jama’a suka watse.

Tana kwance kan gadon Amminta hannunta waya ne tana dubawa taga saƙonshi.

Mikewa tayi zaune ta dubi Ammi tace
“Ammi akwai abinci kuwa a sashen nan?”

Ammi tace
“eh a kawo miki ne?”

“A’a Yaya za’a Haɗawa faazila ta bini dashi na tabbatar be ci komai ba”
seda ta faɗa kuma kunya ya kamata, Ammin murmushi kawai tayi tare da miƙewa ta hado ta ba faazila tuni Fauza kam ta lallaɓa ta wuce.

Tun daga kofa ya tarbeta ya ɗan rungumeta
“Sannu baby mama… Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya miki albarka”.

Kusan kalaman da ta saba ji kenan daga gareshi tunda cikinta ya fara girma
“Ameen Daddyn baby thank you”

Zama suka yi yana nuna mata wasu gadajen yara masu kyau sossai wai ta zaɓa order ɗinshi zasu zo wani sati, tace
“yanzu duk waenda muka yi ta jida a Abuja be isa ba hubby?”

Yana murmushi yace
“ko duka shagunan Abuja muka saye ni dae be min ba… Uhmm na fa ba da aikin ɗakin nan da muka yi magana”

Ɗakin Fatima ne ya sa aka fidda komai za’a gyarawa baby, tayi murmushi kawai se ga faazila da abinci, shi ya karɓa suka ci tare sbd ya Santa idan ba shi yake bata ba bata wani ci me yawa.

Duk yadda ya so tafiyarsu tare haka ya hakura ya barta sbd ya san yanzu tana bukatar babba kusa da ita, sede suna manne a waya.

Watanta ɗaya da sati biyu a gida ranar ta tashi da nakuda me tsanani, yana kwance tun dare yake ta juye juye bayan mafarkin ta da yayi, ya kirata bata yi picking ba.

Hankalinshi gabaɗaya ya tafi yola, haka dae da yaga baccin ba ze yiwu ba ya tashi ya fara nafilfili yana rokar mata sauka lafiya.

Bayan ya dawo sallar asuba ya danna kiran Jaddah, ta ɗaga daga yadda yaji muryarta ya rikice yana tambayar lafiya? Ta sanar mishi Fauza ke labor.

Hmm Allah ne kadai ya kaishi Airport lafiya don ma akwai available flight karfe takwas haka yayi ta safa da marwa a Airport ɗin hankalinshi duk a tashe.

Har ya isa yola ya isa asibitin bata haihu ba, kuma wai ta kwana a haka, ai be jira wani jawabi ba ya banka kofar ya shige, duk ta galabaita kaman jira nakudar ya sake taso mata.

A jikinshi ya sanyata yana mata Adu’a, wani riƙo da ta mishi seda ya runtse idanu be buɗe ba se da kukan jariri ya cika kunnuwanshi, Alhamdulillah! Yake ta nanatawa yana mata sannu a lokaci ɗaya yana shafa kanta.

Wani Sabon nakuda ne ya sake tasar mata, ba bata lokaci ta sake sulbiyo wani babyn.

Shikam Sam hankalinshi na kanta irin wahalar da ta sha se zufa take yi yana share mata.

Mika mishi yaran aka yi bayan an tsaftace su. Ya rungumesu hawaye na zubar mishi..

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!!”
Lallai Allah me kyauta da ƙari shine yau rungume da ɗan shi ba ma guda ɗaya ba har biyu, wani irin godiya ze yiwa ubangiji? Fitowa yayi dasu su Jaddah kowa farin ciki a take Fa’iza da tun asuba ta iso asibitin ta ɗaukesu hoto ta turawa su ya fadila kowa murna mata ne Duka kaman babansu yayi khaki ya tofar har hasken fatar.

Wani irin so da kauna da Faizan yayi ta nuna mata a asibitin sede ita ta ji kunya shi kam ko a gyalenshi, Kwananta ɗaya aka sallameta, Faizan ya kusa cika parlorn Jaddah da saye saye, duk.abunda aka ce ya dace me jego ta ci se ya je ya sayo, kan saniya har uku ya kawo ga manyan bindi yace ayi ta mata psoup tana sha.

Ranar suna yara suka ci sunan Jaddah da mammi, fa’iza ce ta musu inkiyar Arwa da marwa, me jego ta samu kyaututtuka masu dumbin yawa, ta shiga ta fita a wanka da ado kam masha Allah, shima angon karni ba’a barshi a baya ba suka dinga chanza dressing ana daukar su hotuna take suka baza ko ina latest parents of the month ba, kyautar tsaleliyar mota me rai da motsi Faizan yayi mata da wani set ɗin gold me tsada tukuicin kyautar da ta mishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected