Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Tana kai nan ta tashi ta wuce fuuuu, girgiza kai Jaddah tayi tana furta
“Allah ya shirya Fauziyya”
Ita kuwa tana shiga ta rufe ɗakin tare da yin wurin pillow ta dauki wayanta ta kira Zubair, shagwabewa tayi tana faɗa mishi abunda Faizan yayi mata.
Lallashinta yayi tayi, dukda duk sun sha mamakin yadda aka yi ya ganta, tace ita bazata kara tafiya wani garin ba kuma amma shi Zubair ya tabbatar mata akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ba me ganinta.
Satin Faizan biyu aka sanya bukin su da Fatima nan da wata biyu, sbd har sun fara waec.
A take duk bangarori aka fara shiri, ita dae Fauza kaman bata san ana yi ba harkokinta kawai take, ko da Fa’iza ta zo mata da maganan anko ma kai tsaye tace bazata yi ba, su karata chan daga Amaryar har Angon babu abunda ya Haɗata dasu..
Jadda ce ta bada kuɗin nata, Zubair ne yake shirin zuwa Dukda ta ƙi ya ki, wai yayi missing ɗinta Dukda sukan yi waya, su yi video call duka.
Gabaɗaya ya lalatata da soyayyarsa, a gefe ɗaya babu abunda ya sauya daga abubuwan da take yi sai giyar da bata sake sha ba tun daga ranar da abunnan ya faru.
Babanta kuwa ta kan je kullum ta gaida shi, iyaka abunda ke hadasu kenan, wurin mammi ne take girke girkenta hakan ya sa mammi fahimtar abubuwa dayawa daga gareta, har yau bata manta wayar da suka yi da Faizan ba, hakan yasa lokuta dayawa ta kan ja ta da nasihu kala daban daban wadda ya kan kashe mata jiki amma daga ta bar sashen shikenan.
Faizan ya koma bakin aikinshi inda ya Haɗa Fadila da haɗe haɗen kayan aure, dukda ta ce bazata samu zuwa ba sede zata turo ta jirgi se ya karɓa.
Wasa wasa buki ya ƙarato, Amarya da mahaifiyarta ana ta shiri, mutanen Maiduguri sun cika gidan kai ka ce bukin farko kenan a zuri’ar, ba karamin takura Fauza suka yi ba Dukda ta tsaya kai da fata tace babu me saukar mata a ɗaki bukin munafuka da azzalumi, hakan ko aka yi sbd gudun jarabar ta babu wadda ya sauka a ɗakin nata.
Walima, saukar Qur’ani se reception wadda maza ne kawai zasu yi bayan ɗaurin aure aka shirya kaman yadda ake kowani buki a gidan.
Zaune take kan dressing mirror hannunta riƙe da waya tace
“ka fa san irin gidan da na fito Zubair, yanzu in bar gidan nan in same ka hotel kana Tunanin babu wadda ze fahimta?”
Yace
“ni dae ki san yadda zaki yi, Haba sweetheart in taso tun daga Abuja in zo har Adamawa don ke kaɗai abinda zaki saka min da shi kenan? Ganinki ma yayi min wuya?”
Tace
“kayi hakuri! Zan san yadda za’a yi na fito”
Yace
“ko ke fa, ina Green land”
Tace “Toh”
Tsab ta shirya cikin wando jeans crazy da wani armless shirt, ta gyara gashinta sossai ta feshe jikinta da turaruka kan ta ɗauki karamin jacket ta ɗaura saman Rigan ta zumbula hijab ta fito, duk an shiga sallar isha masallaci ga muryar Faizan na tashi cikin nataatsiyar karatunshin nan haka ta fice babu wadda ya lura.
Napep ta tara tayi Jimeta, kai tsaye ɗakin da ya faɗa mata ta wuce, tayi knock ya zo ya buɗe mata tana shigowa ya rungumeta
“oh my babe, I really miss you wlh”
Ta zame tana furta
“miss you more”
A kujera ta zauna tana zare hijab ɗin jikinta, shishar da yake sha ya mastar mata dashi gabanta ba tare da yace komai ba.
Ta karɓa ta ɗan zuƙa kan tace
“Wow the flavor is giving.. Wanne da wanne ka Haɗa?”
Ya mata bayani yana karawa da
“karki damu ba wai bugarwa yake ba kawai dae zaki jiki fresh out of ko wani irin tunani na damuwa ko kunci”
Tace
“kaman ka san bana cikin daaɗin rai wai yarinyar nan Fatima tun fa da ta sa na bar sashenmu ban sake mata magana ba haka itama, shine yau na shiga wurin Ammi ina fitowa kawai naji tace min wai ina kwana Fauxa, ashar na lailaya mata kawai na ji rankwashe babu faɗar da Baba Alhj be min ba, harda zata bar mini gidan in jika a ruwa in sha, wlh na tsani abu da munafuki in ba don ta kalli baban ba na tabbatar haka zata goge ni mu wuce juna”
Yace
“Ki kwantar da hankalinki ina ce jibi ne zata bar miki gidan kowa ya huta?”
Kai ta gyaɗa tace
“bana fata har abada mu sake haduwa in ta tafi kai daga ita har mijin nata ma”
Tana sha ne take ta wannan masifar, lallaɓata yayi tayi da kalamai, daga karshe se gata jikinshi dukda yadda take nuna mai bata so, haka yayi ta rinjayarta, da gasken gaske shedan ke shirin tasiri wurin, tayi saurin mikewa tace
“bari na zo na tafi kar a kula bana gida”
Yace
“mu je dae mu ɗan ci abinci kan ki wuce ko?”
Hijab ta dauka yayi saurin karɓa ya ajiye yace
“me haka? A ganni ni Zubair turaki dake da wannan zumbuleliyar hijabin? Inaaa”
Gashinta ya gyara mata ya riƙe hannunta suka fito, da gaske Fauza na da kyaun fusgan hankalin jama’a, shigar ta kuma ya sa kowa ya kalleta se ya sake kallo, kaman ba ƴar musulma ba.
Restaurant suka shiga, yayi musu order har da su fine whiskey, sun yi nisa a cin abincin kaman daga sama taji wata razananniyar murya ta Furta
“FAUZIYYA!!!”
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
13
Kamar yadda rugugin aradu ke sauƙa haka sunan nata ya saukar mata barin ma a sadda idanunta suka gane mata wadda ya ambaci sunan, wani irin razana da tsorata tayi har bata san ta miƙe kan kafafunta ba, sake ambatar sunan nata da yayi da irin yadda jikinta ke rawa yasa Zubair mikewa yace
“wai waye wannan ɗin ne?”
Takaici ya hana Faizan cewa komai, wani irin fisga yayi mata da saida ta buge da jikinshi ya janye ta suka yi waje saboda idanu dake kansu, motar shi ya karasa ya buɗe ya cillata ciki har Seda ta bugu ta saki kara, be damu ba ya sawa motar key, ya juya ya koma cikin hotel ɗin Zubair dake tsaye yana kallansu zafin ran dake kan fuskan Faizan kaɗai ya hanashi fuskantar shi Dukda kasancewar shi shima namijin ne, amma an ce wargi ma wuri yake samu.
Shi kuwa Faizan wurin abokananshi ya nufa dama abunda ya kawo shi hotel ɗin kenan, abokananshi da suka zo ɗaurin aure duk a hotel ɗin ya kama musu masauki shine ya zo ya ɗan rage dare yaji kuma if they are comfortable with the suits se idanunshi suka mishi mummunar gani, don mummunar gani zai ce dama ya riga ya ɗaura alamar tambaya akan wannan yarinya don fitsararta ma kaɗai ya ishi ta fara bin maza, in ba ta san maza ba babu yadda za’a yi ta bushe idanunta akan kowa har uban da ya kawo ta duniya, amma bata yi a wurin da ya kamata ba don yau kakkanninta zata ci.
Runtse idanunta tayi gam gam, gumi na tsatsafo mata na laifin da ta aikata da kuma na rufe ta a motar da yayi babu iska don be sauke window ba, dunkulewa tayi wuri guda kaman sardine ga kanta dake sarawa na abun maye da ta sha wadda ta sha ne don ya ce mata ba wani bugarwa yake yi ba.
Yau dae ta san me kwatarta a gidansu se Allah, dama an ce kwana 99 na ɓarawo kwana 1 na me kaya yau dubun ta ya cika, ta maimaita innalillahi wainna ilahi rajiun ya fi cikin chasbi.
Saida ya shafe mintuna sama da hamsin kan ya fito lokacin har bata iya jan numfashi me kyau don azabar zafi, wayanta ne ya fara ruri, ɗauka tayi tace