Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Sun gama kenan sun kara sa turaren wuta a burner ya shigo da sallama, kwanciya tayi tare da juya baya, be ma san tana yi ba don ko inda take be kalla ba, akan kujeran ɗakin ya zauna ya gaishe da ya kaka tare da mata ban gajiya, ya kuma tambayi ko akwai wani abunda suke so, suka ce babu yanzu ma shirin tafiya suke.
Se lokacin Fauza tayi saurin ɗagowa
“Ya fadeela yau Zaku tafi wai?”
Se a lokacin ya kalleta babu ɗan kwali kanta gashinta ya sha kananun kitso irin na kanuri yiri yiri ya zuba a bayan wuyan ta wasu ta baya wasu sun sauƙa a kirjinta, doguwar riganta na Holland babba ya tattare daga sharabarta sbd irin kwanciyar da tayi.
Tsaki ya kaka ta ja tace
“yo to dama zama zamu yi? Yau zamu koma tunda mun kawo ki fatan dae Allah ya baku zaman lafiya”
Rau Rau tayi da idanu tana jiran jin amsar yaya fadeela, shi kuwa tun kallon farko da ya mata ya ɗauke kanshi, ya fadeela tace
“zamu tafi Fauxa, haka kowacce mace take hakuri a duk randa aka kawo ta ɗakinta amma ba gaki ga fadyaa ba zaku ke haduwa nima kan in koma Australia zan zo kin ji?”
Kanta ta mayar kasa tana jin kewan gidansu na shiganta, duk yadda ta so tayi dauriya a sadda suka fito tayi musu rakiya kasawa tayi ta fashe da kuka tare da rungume ya fadeela, barin ta yanzu zasu yi da wannan munafukar da kuma azzalumi? Yanzu kenan kowa baya son ta? A haka zata zauna dasu su biyun su kasheta a banza?
Ya fadeela ne ta kalleshi tace
“Ya Faizan se fa ka tayamu riƙeta”
Haɗe fuska yayi yace
“ke! Ban fa son hauka me haka? Se kace wacce za’a bari a gidan yankan kai?”
A zuciyar ta tace
“kaman ka sani wallahi babu maraba”
Ganin bazata sake fadeelan ba yasa ya taka ya sanya hannu ya zarota daga jikinta suka shiga mota driver ya ja suka fice daga gidan, suna fita ya saketa ba tare da ya ce mata ci kanki ba ya juya ya koma, don Fatima bata fito ba wai ta sha magani kuma bacci me nauyi yake sakata shine suka ce kar a tasheta ai tayi kokari ma.
Ta jima tsaye a wurin tana share fuska kan ta juya ta nufi steps na parlorn tana dan kallon black rumfa da aka yiwa mashigar yayi kyau sossai ba kaman normal da ta saba gani ba, koda ta turo parlorn ta shigo babu kowa.
Stairs ta nufa ta fara hawa se a lokacin ta lura da dining area na parlorn kasan da daga saman stairs kana hango shi daga sama, akwai washing hand base da console a wurin shima, se kofa wadda babu tantama na kitchen ne, ba laifi gidan ya mata kyau ya burge ta.
Parlorn saman ma ba kowa se kawai ta shige ɗakinta ta maida kofa, bata kwanta kaman ɗazu ba ta hau kalle kalle da taɓe taɓe kaman ba itace ke kuka yanzu ba, babu abunda bata duba ta taɓa ba, duk da yadda take zabga kamshin humra da turaruka haka tayi ta sake fesa na kan mirror ɗinta wai tana jin kamshin su, bayan ta gama tsab ta wuce bayi nan ma tayi ta dube dubenta, ba laifi bayin ya tsaru ta kan yi mamakin toilets na hotels da suke zuwa musamman irin su transcorp sede wannan ya ci uban waenchan haɗuwa.. Ita bata san ma akwai kayan bayi ruwan gold ba se anan ɗin kusan komai ruwan gold ne Fararen kaɗan ne.
Bayan ta gama tayo fitsari dama bata sallah, ta ma yi mamakin wannan period nata be zo mata da ciwon da ya saba ba ko don sbd tashin hankalin da ta shiga ne oho.
Fitowa tayi ta cire Rigan jikinta don ya ishe ta ta duba leggings da vest ta saka abunta ta zauna ta ci tayi Nak kan ta hau gado tayi ɗaiɗai ta fara bacci.
(Su Fauza an samu duniya)
Chan cikin baccin ta me daaɗi taji ana buga kafafunta, bata da nauyin bacci hakan yasa ta mike zaune tana ɓata fuska hasken bulb da ɗakin ya dauka ya tabbatar mata da dare har ya shiga bata sani ba tana baccin da ta kwana biyu bata yi ba.
Kallon Fatima da ta tashetan take yi tana jira taji me zata ce sede shiru tayi tana sake kallon Fauxan zuciyarta na hautsinewa da wani zazzafar kishin yarinyar ta ko ina.
“Lafiya zaki wani tasheni ina baccina kuma ki tsaya kina kare min kallo kaman yau kika saba ganina?”
Haɗe rai Fatima tayi tace
“kul ki soma min rashin kunya daga shigowanki gidana, idan baki sani ba ya kamata ki sani da ba yanzu bane, a da ina kallonki ne kawai a matsayin shashasha wacce bata san me ke mata ciwo ba shiyasa nake kyaleki kike abunda kike so, amma a yanzu da kika amsa sunan kishiyata yanzu ne zaki sake yanke rago ki tabbatarwa da duniya cewa Fatima munafuka ce duk na baya wasa ne”
Murmushi Fauza ta saki tace
“kishiya? Mtseww ke kika san wannan, in baki sani ba ya kamata a ce na saka wannan a bayan tosheshen kwakwalwarki, ban shigo gidan nan da niyyar komai ba don daga ke har mijin naki ba kwa gabana, amma daga sadda kika bari na harzuƙa zan nuna miki cewa kin riga kin bar kari tun ran tubani, zan zame miki kadangariyar bakin tulu se kin yi nadamar fara auren mijin kaddarana. Don haka ki kiyayeni”
Yunkurawa Fauza tayi zata miƙe daidai lokacin da aka turo kofa hakan ya sa Fatima yin baya baya zata faɗi cikin zafin nama yayi hanzarin isowa ya tarota yana aikawa Fauza dake tsaye tsakiyar gadon bata kai ga Sauƙar da tayi niyya ba wani irin dead look.
*Yanzu wasan ya soma*
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
17
*Assalamu Alaikum warahmatullah barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya? Alhamdulillah na gode sossai da adu’o’inku gareni Allah ya saka da alkhairi jiki yayi sauƙi se a ɗaura daga inda aka tsaya in shaa Allah.*
A hankali ta samu wuri ta zauna akan kujeran parlorn saman chan nesa da inda suke, dukda zuciyarta a tsinke yake don har Ga Allah Faizan na daga cikin waenda take jin shakkarsu don tana tsorace dashi ne tun tana ƴar ƙaramarta, matarshi kawai ya kama suka fita daga ɗakin nata bayan ya ce ta same su a parlor.
Ya ɗan yi shiru kan yace
“Fauziyya kike ko?”
Kai ta ɗago tana Kallonshi wai ita yake tambaya sunanta? Bata amsa ba seda yace
“wai ba da ke nake magana ba? Kin san Allah ki rufawa kanki asiri ki zauna lafiya da mu tun muna sheda juna, ba zan lamunci rashin kunyarki da fitsaranki ba, ba a kaina kaɗai ba har da matata”
Kallon Fatima yayi yace
“Daga yau ki sallami Baaba ta dinga tsabtace gidan nan tana girka muku abunda Zaku ci da ke da ita, ba zan iya cin jagwagwalonta ba don haka ke zaki kula da nawa abincina da gyaran ɗakina”
Fatima na murmushi tace
“in shaa Allahu habeeby”
Ya sake kallon Fauziyya yace
“Daga ni har Fatima akwai wadda kika fi shekaru?”
Girgiza kai tayi yace a ɗan zafafe
“baki da baki ne?”
A hankali tace
“A’a”
Yace
“madalla! Saboda haka duk safe ke zaki gaisheta, karki kuskura in sake ganin abunda ya faru yau ya faru don bazaki ji da daaɗi ba Fauziyya, matata ta fi karfin wulakantarwanki, Abu na ƙarshe shine babu wani zancen rabon kwana don zaki zauna ne a matsayin ƙanwarmu..”
Kallon Fatima yayi yace
“ko kina da abun cewa?”
Tace
“ya Faizan na ga baka ja kunnenta akan shan kayan maye da kuma bin maza ba!”