Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Wucewa Fauza tayi ta buɗe back seat ɗin motan shi ta zauna yayinda yake rike da hannun husna yana nuna Fatima da hannu wacce ta fara cewa

“A’a ina zakuje? Ga fa keys ɗin na dawo dasu…”

“Ki tabbatar kin tanadi furucin kare kanki a gareni kan in dawo don wallahi wallahi ranki se yayi mummunan ɓaci akan wannan abunda kika aikata, ko babu aure Fauziyya da husna sun fi karfin yunwa a gidana Fatima…”

Yana kai nan ya zagaye da husna ya buɗe mata gaba ta shiga, ya dawo side ɗin driver ya ja motar ya fice da gudu.

Hannu Fatima ta ɗaura a kai tace
“na shiga uku!”
Da gudu tayi cikin gidan don kiran Auntyn ta ta nemi mafita kan ya dawo, garin neman gira tana shirin rasa idanu, ita da ya kamata ta nisanta su gashi tana shirin kawo kusanci tsakaninsu, ina zasu je? Me zasu je suyi? Shine kawai tambayar dake ta mata kai kawo.

Driving yake yana sauraron sheshekar kukan da fauza ke yi, husna ganin Fauza bazata yi shiru ba yasa itama ta fara kuka tana waigawa ta kalli Fauza da ta ɗaura fuskanta a tafin hannunta ta kuma kwantar bisa cinyar ta tace
“Aunty yunwa kike ji ko? Kiyi haƙuri yanzu zamu je mu ci abinci ko uncle?”

Shima Fauzan yake kallo a kai a kai ya gyaɗa kai yace
“in shaa Allah Husna”

Restaurant mafi kusa ya kaisu, husna na fita ya zagaye ya buɗe mata kofan.

A hankali ta sanya kafa ta fito yace
“kukan nan shi ze kosar dake ne?”

Bata tanka shi ba suka nufi ciki tana tafiya a hankali sbd cikinta da ya kama, tea me zafi ya fara ordering Allah ya sa VIP ɗinsu room ne so in ka shiga babu me ganinka, suna shiga ta nufi zubewa yayi saurin tarota suka karasa kan lallausan shimfidun dake wurin ya ajiyeta ta zame ta kwanta, sake kiransu yayi a landline dake wurin cikin mintuna se gasu da shayi kan ya basu ordern abincin da zasu kawo musu.

Da kanshi ya ɗagota ya miƙa mata shayin, kurbi biyu zuwa uku tayi se amai.. Da gudu ta karasa washing hand base dake wurin ta fara kwala amai, yana riƙe da kafadanta hannunshi ɗaya na shafa bayanta cikin tsantsar tausayi yake furta
“sorry! Sannu am so sorry”

Daga ka ga aman ka san na wahala da yunwa ne, bayan ta gama suka sake dawowa ya bata tea ɗin ta sha, bayan ta shanye ya matsar mata da abincin da aka kawo ɗin tuwo ne da miyar vegetable, yatsina fuska tayi tana kallon tuwon, husna har tayi nisa a cin nata.

“Bakya so?”
Kai ta gyaɗa don ita bata son tuwo, janyewa yayi ya sake kiransu tana ta Kallonshi da idanunta da suka kara girma, yadda duk tausayinsu ya kasa boyuwa a fuskanshi kaman ze yi kuka, tambayarta yayi tace rice and stew with plantain. Nan take ya faɗa musu suka kawo.

Zama yayi yana kallon yadda take cin abincin Dukda yunwa da take ji amma cin ba wani sauri ko hargagi a natse take kaiwa bakinta, ganin zata ɗago yasa ya ɗauke kai ya fara cin tuwon da taki ci ɗin.

Ba su suka dawo gidan ba don ya biya dasu sahad sun sayi abubuwa snacks masu yawa dangin su biscuit da su drinks da kayan tea su custard da oat, golden morn, coco pops ba abunda be saya ba.

Don anan ma yaga laifinshi da be ajiye musu abubuwa haka a ɗaki ba, tunda daga dakinshi har na Fatima akwai snacks da drinks kuma a fridge.

Pizza da shawarma spot suka je ya sake saya musu kan suka nufi dawowa gida, duk abubuwan da yake yi ɗin sede suyi hira da husna amma ita kam tak bata ce ba, tana jingine da jikin motar daga karshe ma bacci ne ya kwashe ta.

Ko da suka dawo gidan a gate ya tsaya ya cewa gate man ɗin ya janye maganan da ya faɗa duk sadda Fauza ta nemi fita ya barta ta fita.

Daga haka suka karasa ciki, zata ɗauki kayan yace ta bari.

Haka ta wuce ta Barsu da husna, bata ko kalli Fatima dake zaune a parlorn kasan ba ta haura abunta, kayanta kawai ta sauya ta kwanta akan gado sbd wani irin bacci da take ji.

Shi kam dashi da Husna suka kwashi kayan zuwa sama saida ma yayi sawu biyu, da kanshi ya shirya abubuwan inda suka kamata, kan ya kama hannun husna suka yi ɗakinshi tana cin shawarma.

“Yaya..!”
Fatima ta kirashi ko kallonta be yi ba, tayi saurin binshi ɗaki ya juya ya daka mata wani hargitsatsen tsawa
“get out of my sight tun baki sanya ni yin abunda zamu zo duka muna dana sani ba..”

Zata sake magana yace
“outt!”
Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta fice tana kuka.

Duk abubuwan da ya kamata yayi yayi har wanka yayi ya sauya kaya kan lokacin husna tayi bacci, ɗaukanta yayi ya fito zuwa dakin Fauza.

Saida ya sauya mata kaya kan ya nufi gadon da ita ya kwantar idanunshi kan Fauza dake bacci peacefully, Adu’a yayi musu kan ya fito.

A hankali ta buɗe idanunta ta bi bayanshi da kallo har ya maida kofa ya rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta gyara kwanciyarta cikin nazarin yadda zata ci uban Fatima na abunda tayi mata…

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

21

Kimanin sati biyu kenan da faruwar abunda ya faru amma ta lura har yanzu ba wani shiri suke yi da Fatima ba, ya bata key ɗin kitchen na ƙasan gabaɗaya sbd rashin zamanshi don sun koma aiki ka’in da na’in, bata shiga harkar Fatima da take ji kaman ta hadiye zuciya ta mutu sbd yadda Faizan ya ɗauki fushi da ita akan abunda take ganin be taka kara ya karya ba, ita da ya kamata yanzu ya tarairayeta ya bata kulawa.

Ita dae Fauza tunda tana da husna bata da matsala don yarinyar na debe mata duk wani kewa, tare suke koman su cikin hira da dariya lokuta dayawa gani take kaman husnan sa’ar ta ce in gujel gujel ne ma duk haka suke zagewa su yi kayansu.

Kaman yau a parlorn ƙasa suka yi la’asar sbd cookies da suke yi kar ya ƙone, bayan sun idar suka zuba shi a tray me kyau, da Homemade pineapple juice tayi musu har zasu haura dashi se husna tace
“Aunty mu je garden pls you promised fa cewa weekend nan zamu je ni kam I want to play with swing”

Fauza ta kalleta tace
“ke kam kina da aiki mutum baya mantuwa? To mu je”

Juyawa suka yi suka fito, daga hannun hagunsu akwai wani ƙofa suka shige sun ɗan yi tafiya kaɗan se ga garden ɗin masha Allah kore sharrr, akwai lilo sbd hutawa, gefen shi akwai table da chairs, nan ta ajiye snacks ɗin, suka je suka hau Lilon suna lilawa Fauza na tsoron juwa bata so da karfi amma da gangan husna ke wullawa da karfi wadda ke saka Fauza ihun kiran sunanta ita kuma ta watse da dariya.

Zaune yake a balcony ɗinshi bayan ya dawo daga sallar la’asar sanye da farar jallabiya wacce bata kai kasa ba don kana iya hangen black trouser da ya sa daga ciki, fuskanshi yayi wasai yayi wani irin kyau, dariyar su da kuma ƙarar Fauza shi ya saka shi miƙewa tsaye, chan ya hange su suna ta lilo, lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan tray ɗin dake gefensu, ba karya his tongue have been craving for the tatse of her food again barin ma tea ɗin nan da sati biyu kenan da yake so yace ta mishi yana fuskewa.

Jaridar ya ɗauka ya koma ɗakinshi ya buɗe kofa ya sauƙa ƙasa, a natse yake tafiya cikin ƙasaitacciyar tafiyar shi da already ya zamar mishi jiki ya isa garden ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected