Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Wani arnen material lace aka yi mata fitted gown dashi wadda ya fitar da duk wani surarta yadda ya kamata ko numfashi me kyau bata yi amma dayake har ya fara bin jiki bata damu ba, kanta ko ɗan kwali babu se wani gyara da ta mishi jelar na reto a bayanta wani high hill shoe da inches ɗinshi ya kusa huɗu ta saka ta rike wayanta suka fito jewelrys ɗinta se dauke idanu suke.
A cikin hotel ɗin ne za’a yi sede ta chan baya, ba su isa wurin ba saida aka fara da ɗan jimawa.
Kwas Kwas Kwas haka karan takalmansu ya karaɗe ilahirin wurin wadda hakan ya saka celebrant ɗin da ya fara bayani cikin ƙasaita da ji da kai dakatawa.
Chak ya tsayar da fitilun ganinsa bisa kanta, Grey eyes ɗinta da ya ji liner se ɗauke hankali yake, Zubair be taɓa ganin halittar da ya tafi dashi a kallo ɗaya ba sai Akan wannan, don kasa cigaba da bayanin godiyan yayi Dukda su Fauxa har sun sama wa kansu mazauni, class ɗin yarinyar ya burgeshi kwarai don har ta zauna kaman bata san ta fisgi hankalin mutane dayawa daga wurin ba.
Taɓa shi da suhail yayi ya saka shi farga da ya ɓace a duniyar fauxa Dukda ko sanin ta be yi ba, bayanin ya karasa aka mishi tafi.
Yana ba da mic ya koma ya zauna mazaunin shi yana kallon suhail yace
“wacece wanchan? Na ganta da buduruwarka”
Suhail yace
“Zubair in zaka ɗauke kwalamarka kan wannan ka ɗauke sbd ta fi karfin duk yadda kake tunani”
Wani banzan kallo Zubair ya yiwa suhail ze yi magana Najeeb yace
“kaman yadda suhail ya faɗa nima shawaran da zan baka kenan…”
A fusace yace
“saboda ita ɗin ƴar waye kenan? Ta kaini? Ni da na Haɗa sarauta da mulki? Karka manta duk wata kwangila Indai daga fadar shugabar kasa ze fita hannuna yake zuwa, ina juya dala da euro so babu wannan magana, ko ka manta ni ɗin Burin kowacce macece da ta san rayuwa da abunda ya kunsa? Kalli ku ga duka en matan da suka taru anan sun yi ado da kwalliya ne sbd su burgeni har su sace zuciyata kuma kun san babu wacce babanta yake ƙaramin mutum me kuke min tsoro? har ta isa ta yarfa ni?”
Suhail ya ce
“ita ba ƴar kowa ba amma fa uncle ɗinta babu wadda be yi mishi tayin matsayi ba daga mulkin har sarauta ya ƙi, in kana jin Prof kaka to ƴar gidan ce, yarinya ce amma tana da kwarjinin manya daga jininsu ne”
Shiru ya ɗan yi, kan ya ce
“ni kuma zan baku mamaki akan yarinyar nan Dukda aurenta nake son yi amma na muku alkawari kan ta bar Abuja se na saye zuciyarta da gwagwalan laffuza da salo na”
Ihu suka mai, suka yi dariya a tare yana kara cin alwashi akan Fauxa ɗin.
Kowa kan shi yake serving sede Fauza bata motsa ba bare ta tashi ta ɗiba, kanta na kan waya tana kallon wani necklace da yayi mugun tafiya da ita..
“Wow wannan tayi! gashi kuwa ba ƙaramin haskata za kiyi ba da zaran ta hau wuyan ki”
Ɗagowa tayi ta kalleshi ba laifi kyakyawa ne ajin karshe, magananshi kuma ya ɗan bata dariya Tace cikin basarwa
“sai kuma ya kasance bana neman tayin zaɓin kowa kan abunda na san ze yi min kyau ko akasin hakan”
Yayi murmushi ya ce
“in kin min izini zan iya zama?”
Tace
“Allah sarki ai bani da hurumi da kujerun nan ɗin don nima a gayyar soɗi na zo”
Yayi murmushi me kyau yace
“Ai zuwanki ya fi min zuwan shugaban ƙasar Ingila don ni kaɗai na san irin farin cikin da na shiga da ganinki”
Ta ɗan ɓata fuska tace
“farin ciki??”
Yace
“yeah, farin cikin na samu matar aure”
Kanta ta mayar kan wayanta kaman ba ita ce tayi tambayar ba, kaman ma bata ji amsar da ya bayar ɗin ba, shima shiru yayi yana jan class ɗinshi.
Sun shafe mintuna kusan talatin kan yace
“Wow! Zaki yi kyau da sarauta”
Idanu ta ɗago ta watsa mai kan ta ɗaga tana kallon mutanen wurin da aka fara watsewa ana komawa cikin hadaddiyar club na hotel ɗin inda anan ne asalin chasun, nan an rage lokaci ne da ɗan abinci da snacks. Ba tare da ta ce mishi komai ba ta sake maidawa kan wayanta.
“Princess let’s go in its time for the real fun”
Mikewa kawai tayi suka jera, yace
“sunana Zubair turaki am the celebrant, dukda baki tambaya ba”
Se sannan tace
“oh happy birthday”
Yace
“thank you! Where’s my gift?”
Dan murmushi tayi kawai daidai lokacin suka shiga cikin club ɗin da mata suke ta rawan sanda kida na tashi sai de ba sauti sossai.
“What do you want as the gift?”
Tayi mishi tambayar.
“Just ur heart, kina ban zuciyarki kin yi kyautar da ba zan taɓa manta ta ba”
Dariya tayi gayen nan na da aiki, basu sake magana ba saboda kiɗar da aka sauya sauti har wani baya jin maganan wani ana ta rawa color bulb na Juyawa daga blue zuwa yellow zuwa red.
Cikin ihu yace
“Do you mind a drink??”
Itama da karfi kaman yadda yayi tace
“Non-alcoholic”
Kallon mamaki ya mata, kan ya juya hanyar toilet da ya hango suhail yayi yace
“bata shan komai?”
Kai suhail da yake ba a hayyacinshi ba ya gyaɗa mai, murmushi yayi kawai ya juya ya tafi gaban bar, inda ya sa aka yi mishi mixing kalar fine wines da yake sha, ita kuma yace coke, ana tsiyaya rabi ya sa aka sa mata whiskey marar taste yadda ba zata ji ba, ya riƙo ya kawo mata tace
“thanks!”
Shan Nashi ya fara yana ganin yadda take rike da nata tana rausayawa a hankali, bakinta na bin waƙar dake tashin.
Suuu ta tafi zata zube a sadda ta gama shan drinks ɗin yayi hanzarin sa hannunshi ya rungumo kwankwasonta cup ɗin hannunta ya faɗi ya fashe, murmushi yayi yana shafa fuskanta da Ɗayan hannun nashi yana Juyawa da ita.
“Ashe jininki bashi da ƙarfi” ya faɗa a kunnenta in a whisper.
Sossai ta bugu tun tana luuu luuu har ta fara ihu da ƙarfi kaman wacce ke jin daaɗin club ɗin ta fara rawa sossai yana rike da ita yana ƙare mata kallo cikin murmushi, be taɓa Tunanin birthday ɗin shin nan ze zama fun haka ba se yanzu.
Sun yi rawa har sun gaji en mata dayawa sun kwashi takaicin ganin shi da ita, ita kam gabaɗaya ta rasa hankalinta.
Da sauri sakina ta riƙo hannunta tana Kallonshi tace
“Zubair kayan maye ka sa mata?”
Sakina tace
“mun shiga uku! Haba Zubair ka kuwa san me ka aikata?”
Yana smirking yace
“normal ne fa, am very sure zata ji daaɗin hakan idan ta dawo hayyacinta”
“me nufin ka?”
Suhail ya jefa mishi maganan, basu kula da surutan ba..
“Guys calm down ba fa abunda nake nufi, kuma babu abunda zan mata..! A hankali time ɗin da kuke yiwa tsoro ze zo, am very sure nan kusa da kanta zata neme ni da soyayyar abunda kuke yiwa tsoro it’s just a matter of time”
Ya karashe yana dariya sossai, ajiyar zuciya suka sauke sakina tace
“ka bi a hankali wallahi baka san kalar haukan Fauxa bane”
Riko ta yayi yana cewa
“kuyi abunda ke gaban ku”
Yana kai nan ya janye ta suka fice.
Da sassarfa yake sauƙowa daga matakalar jirgin idanunshi kan tsadaddiyar agogon dake ɗaure a farar fatanshi, sanye yake da baƙin wando da kuma farin shirt wadda kallo daya zaka mishi ka san pilot ne, baƙin necktie ɗaure a wuyan shi, jacket da karamin brief case a hannun hagunshi.
Sauƙar su kenan daga Adis Ababa, da sauri aka buɗe mai gaban wata Prado dake Parke don shi ya shige, drivern dake sanye da kaya me tambarin jirgin da ya tuƙon ya ja suka fice da gudu daga airport ɗin.
“Sir ina muka nufa?”
Ɗan kallon hanya yayi kan yace
“transcope hotel”
Saita hanya yayi saboda shirun da garin ya ɗauka yayi ta tsuga gudu bai tsaya ko ina ba se harabar na transcope, sauƙa yayi yana furta
“thanks”