Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“wai me yake damunki ne Fatima?? Me yasa bakya so kiga an zauna lafiya? Meyasa kika kasa sakawa zuciyarki salama? Kullum ƙorafi an yi miki kaza an yi miki kaza? Yanzu da zan yi baƙi ban taka har ɗakinki na faɗa miki ba amma me kika musu? Babu. da babu Fauziyya haka zan kunyata? Ke baki san zuru ba? To karki yarda ki kai ni bango ba zan lamunci wannan ba, ki sani na raba muku kwana jiya da yau kwanan ta ne gobe ke zaki ci gaba, kaman yadda bata sa miki ido a naki ba karki saka mata a nata bana son fitina… Kin gane ko?”
Kallonshi kawai take kaman bakonta tunda ta shiga gidan yau ne rana na farko da ya zage ya rufe ido yake ta mata faɗa Dukda ita har lokacin bata ga laifinta ba, son shi da take kawai yayi yawa shine laifinta, irin attention da yake ba Fauza da take so kawai shine laifinta?
Kuka take yi sossai tana jin kaman tayi hauka.
Lallai Mahaifiyarta bata kyauta mata ba da ta kwadaitar da ita Faizan tun bata gama sanin menene so ba, son shi yayi mata zurfi wadda bazata iya Daena ƙorafi ba in har akan wata macece.
Fita kawai yayi ya kyale ta.
Be koma kitchen ɗin ba se yayi ɗakinshi kawai, Fatima na da matsala abubuwa dayawa da tayi tayi a farkon aurensu se yanzu yake ganin rashin dacewarshi ko dama sbd ita kadai ce kuma he was new in the system yasa be gani ba amma yanzu duk asalin halayyar ta kishi ke hankaɗosu.
Har dare ma be sake haduwa da kowaccensu ba, se da ya dawo isha ne ya shiga ɗakin Fauza itama ganin ranshi har lokacin ba’a sake ba yasa bata ce komai ba ta gabatar mai da abinci da tea ɗinshi.
Yana Ci ya dube ta yace
“gobe zan koma wurin Fatima pls idan tayi kwana biyu ki cigaba da naki and ki dinga ajiye mana a dining zamu ke haɗuwa muna ci mu duka that should be the policy”
Tace
“Toh”
Yace
“jibi da safe zamu tafi yiwa Husna shopping”
Ta amsa
“Allah ubangiji ya kaimu”
Ya so ya kawo maganar waya don Jafar ya kirashi wai matarshi na son layin Fauza don sun manta basu yi exchanging ba se kuma ya fasa don har yanzu be jin ze iya saya mata waya tukuna.
Ranar dae kam kowa ɗakinshi ya kwana, tayi kwanciyarta da husna.
Sunday ma ya ɗan yi short tafiya kwata kwata basu haɗu ba se dare shima abinci ya ci wadda Fatima ne ta karɓa tunda yamma ya riga ya shiga, saida ya tabbatar basu da wani matsala kan ya wuce room ɗinshi Fatima ta bi bayanshi Fauza kam ko a jikinta ta kama husna suka yi ɗakinta.
Washegari Fatiman ce tayi breakfast itama tayi wanka ta shirya cikin Atampha dinkin bubu, sanye da kaftan dinkin zamani ruwan ƙasa ya fito, ya haɗu har ya gaji.
Itama Fauza Abaya ta saka milk and brown tayi kyau sossai barin ma ɗan face ɗinta da ya fita a Tarhan da tayi, ta gaishe shi kan ta gaida Fatima a dakile ta amsa, baki Fauza ta taɓe tare da serving husna tayi serving kanta tunda Fatima tayi serving mijinta ne kaɗai.
Quitly suka ci abincin Dukda ita kam Fauza kaɗan taci ta miƙe ta koma parlor tana jiran shi.
Kallon Fatima yayi yace
“Am kin kuwa san yau da yamma husna zata bi iyayenta?”
Kai ta girgiza tace
“ban sani ba tunda babu wadda ya faɗa min”
Kallonta yayi kaman ze yi magana se kuma kawai ya fasa, ya lura harshen Fatima ba a kame yake ba Sam bata san yadda zata ke mai magana ba.
Mikewa yayi yana goge bakinshi da tissue hannunshi rike da husna suka fito parlorn yace
“mu je ko?”
Mikewa Fauza tayi Fatima tayi saurin cewa
“Ina zaku? Ko ka manta kana cikin girki na ne?”
Yace
“don ina cikin girkin ki se aka ce ba zan fita da fauza ba? Ko ke kika ajiyeni da dole se kin san duk inda zani?”
Fauza dae bata ce musu komai ba ta kama hannun husna suka nufi ƙasa.
Yace
“yarinyar nan husna kaman yadda take ƴa a wurin mu haka kema amma ko kallon arziki da mutunci ba zan ce ya taɓa hada ki da ita ba, ina faɗa miki zata tafi yau amma me? Kina wani bada amsa cikin gatse to in miki yaya kike so?”
Yana kai nan ya nufi gangarawa abunshi.
A gaba ya samu husna ita tana zaune baya ya ja motar suka fice, shopping sossai suka yi mata tana ta basu dariya da hirarrakinta, they all enjoyed the moment Har azahar don Fauza bata da lectures kan suka biya suka ci abincin rana a yadda Fatima ta gayamai bazata dawo ba se huɗu tun jiyan yasa be ma tuna wani jira ta koma ta mai girki ya ci ba.
Daga nan suka yi gida Fauza ta haɗe mata kayan tsab.
Sam Faizan be so ta koma ita ɗaya ba amma baze iya kaita ba don akwai tafiyar da ze yi Tuesday da safe kuma ze yi 2-3 days.
Da farko ya tuna ko su je da fauza sede bata da visa, ko international passport be yi tunanin tana da shi ba, Seda suka yi la’asar kan suka fito suka tafi Airport… Suna tsaye wata cabin crew ta iso a shirye cikin irin shigar sun nan bakinta ya ji hot red lipstick se yanga take yi..
“Sir good evening”
Ya amsa fuskanshi ba yabo ba fallasa yana nuna mata husna yace
“she’s my niece nd she will be flying with you guys pls take good care of her”
Ita ce shugabar crew ɗin na yau hakan ya sa yake bata amana kuma sun san shi bashi da wasa, baya shiga harkarsu idan har ba maganan aiki bane, gasu Allah ya ɗaura musu maitarshi da kwaɗayinshi, a yangance tace
“Worry not sir, we will make sure we give her all the care and attention from the boarding to departing”
Yace
“Good”
Fauza ya kalla se yaga duk fuskanta ba fara’a kaman ɗazu, ya san duk kewar Husna zata yi, dukawa tayi tana rike da hannun husna take ce mata ta gaida kowa da kowa in ta isa.
Kaman kar su Rabu haka tayi ta ɗaga musu hanu seda suka bace kan Fauza ta fara sauke hawayen da take rikewa dama bata son yin kukan ne sbd husnan.
Kawai ji tayi lallausar hannunshi ya shiga cikin nata yana matsewa a hankali alamar rarrashi.
Zare hannunta tayi suka nufi mota, har suka isa gida bata ce mishi komai ba kewan husna duk ya dameta, hakan ya sa suna isa ya je ya duba wayan nan ya bata akan ta kira su jadda.
Ɗakinta ta shiga ta kira su kuwa sun jima suna ta waya har Amminta ta kira suka gaisa saide bayan nan bata ce komai ba ta kashe wayan, tsintar kanta tayi da gwada saka layin sakina ta kira, ringing na karshe ta dauka
“Ke! Fauza ce”
Ihu sakina ta saki tana cewa tana ina ne a Abujan? Sun yi ta neman layinta shiru wannan ne sabon layinta? Tace na mijinta ne.
Rahama ce ta karɓa take ce mata Zubair ya kusa haukace musu akan ta kuma har yanzu be hakura da neman location ɗinta ba har fa cewa yake ze kai su baba court sbd an mata auren dole.
Dariya tayi tace
“Zubair kenan”
Sam bata san ya shigo ba se ji tayi ya zare Wayanshi daga hannunta yana yi mata wani irin kallo kan ya juya a fusace ya fice yana buga kofan da karfi…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
27
Ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin yadda ya fita a mugun fusace..
“Innalillahi wainna ilahi rajiun na shiga uku! Yanzu me ze yi tunani?”
Ta furta tana mikewa tsaye, bata taɓa jin buƙatuwar wani ya fahimce ta ba kab rayuwarta se yau, ta san yanzu Fatima ta riga ta shiga ɗakinshi da kyar ta iya barin wa gobe ta ga abunda hali ze yi, wlh Allah ya gani ba da wani niyya mummuna ta kira sakina ba kuma ita yanzu Zubair baya cikin rayuwar ta don har ta mance dashi ma.