Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Ciki ya nufa ba tare da ya jira amsar drivern ba, daga yadda yake tafiya zaka san wannan ɗin zakin namiji ne, fuskanshi a kame sai de be hana kyaunshi bayyana ba.

Reception ya dakata ya biya room VVIP, ya karbi key ya nufi elevetor daidai lokacin su kuma sun bi ta bayanshi sun shiga, yana shirin rufuwa yayi saurin saka hannu tare da sanya kai ciki…

**Tou Readers anan na kawo karshen free pages ɗin Diddigar ƙaya da Naira ɗari uku kachal zaki mallaki sauran ki sha karatu cikin kwanciyar hankali**

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

11

Sau ɗaya ya sauke ganinshi kan su ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, yana rasa me matasa suka ɗauki baɗala suka ɗaurawa kan su a yanzu, in har kana da kuɗin kama suit a hotel ɗin nan kayi sharholiya why not ka ajiye ka fara shirin aure ko mata nawa ne? Duk takaicin shiga cikin elevator ɗin ya cika shi, a hawa na sha ɗaya elevetorn ya tsaya tare da buɗewa.

“Babe mu je ko?”
Zubair ya faɗa yana ɗago Fauxa da gabaɗaya jikinta ke sake, ture shi tayi ya sake saurin tarota ganin tana shirin faɗuwa garin haka ne gashinta ya sunce ya rufe mata fuska daidai lokacin da Faizan ya sake waiwayowa ganin suna ɓata mai lokaci.

A hannunta dake cikin na Zubair ya fara sauke idanu kan ya kai jikinta zuwa fuskar ta da gashi ya rufe kana ganinta ka san ba karamin buguwa tayi ba, Jan ta Zubair yayi ganin elevatorn na shirin rufuwa, da wani irin disgusting look yake bin su har suka fita, ita da fuskanta ke facing elvetor ɗin ta sa hannu ta gyara gashin nata daidai lokacin da elevatorn ya gama rufuwa.

Gabanshi ne ya faɗi, ko tantama babu wannan fuskan ɗan gidansu ne Dukda kai tsaye baze ce wacece ba amma tabbas wannan yarinyar tana da alaka da gidansu, floor na 13 elevatorn ya kaishi haka ya fasa sauka ya sake danna na sha ɗaya, da sauri ya fito daga elevatorn yana dube dube, sai de babu su ba alamar su, ya jima tsaye yana tunani a wurin kan ya koma ɗakin da ya kama, zuciyarshi na faɗa mishi Fauziyya ce sai de taya zata bar gida ta zo har Abuja babu wadda yayi noticing kuma ta sha kayan maye? With this her young age? Kai be amince da abinda zuciyarshi ke faɗa mai ba.

Bai gansu ba amma ya sha alwashin sakawa floor ɗin idanu sossai ko ze sake ganinta.

Ɗaki ya koma ya watsa ruwa yayi sallar isha da shafa’i da wutiri, haka ya kwanta da tunane-tunane a ranshi sbd idan har tabbas yarinyar chan ne lallai ta tabbata annoba kuma se inda karfinshi ya kare wurin ganin an hukunta ta daidai da abunda tayi a cikin zuri’ar su.

Da sassafe ya danna kiran Mammi, gama azkar ɗinta kenan tana shirin shiga kitchen sama ma mai gidanta abincin safe ta ga call nashi, ta ɗan yi mamaki kam kan ta ɗaga
“Assalamu Alaikum warahmatullah mammi barka da safiya”

Ta amsa tana zama bakin gado
“Wa’alaikumussalam warahmatullah barka ka dae babana, ka sauƙa lafiya?”

“Alhamdulillah mammi, ya ciwon kafafunki hope da sauƙi?”

Ta amsa da
“Alhamdulillah”

Ɗan shiru yayi kan yace
“mammi ni kam yarinyar nan tayi tafiya ne?”

Shiru mammi tayi cikin tunani kan tace
“wace yarinyar kuma?”

Yace
“wannan na gidan baba Alhj, marar jin.”

Girgiza kai mammi tayi kan tace
“Fauziyyar ce baza’a ka iya faɗa ba sai ka yi ta juye juye? Eh sun tafi excursion Gombe daga makaranta”

Da sauri ya miƙe tsaye kenan ba gizau idanunshi ke yi ba ita ɗin ce, yace
“mammi yarinyar nan ba Gombe ta tafi ba, jiya na ganta da wani a halin maye da shigar banza!”

“Faizan!”
Mammi ta kirashi daga jin muryarta ya san ranta ne ya soma ɓaci.

“Faizan don baka son yarinyar nan shine zaka ɗauko hanyar yi mata sharri? Buguwa fa ka ce? Sannan da namiji a hotel?”

Yace
“kin san ban taɓa miki ƙarya ba, kuma a kan wannan annobar ba zan fara ba. Ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, zan kira Farhan ya je min makarantar ya bincika don bazamu lamunta ta ɓata mana sunan gida ba, Never!”

Mammi tace
“sunanta Fauziyya, kada ka sake ce mata annoba, sannan takarda da tambarin makaranta da kuma stamp da sa hannu ta kawo ni ta fara kawowa kuma tafiyar ba ita kaɗai ba ce, kar in sake jin irin wannan zance daga bakinka, karka manta ƙanwarka ce kuma karka manta tarbiyar gidan da ka fito”

Tana kai nan ta kashe wayan, hannunta har rawa yake, ta san Faizan be taɓa yi mata karya ba, idan ba akwai abunda ya tsana karya ne, sai dae bazata taɓa yardar wa zuciyarta Fauza ya gani a hotel a Abuja ba, kila kama ce kawai.

Har ta gama girki tana nazari, Farhan na shigowa gaisheta bayan sun gaisa tace
“Farhan ina so ka je min makarantar yaran nan ka samu vice wadda ya sanya hannu a tafiyar su Fauza ya sake tabbatar maka da tafiyar, sannan ya kira wani a Haɗa ku kaji lafiyarta”

Farhan yace
“mammi wani abun kuma ya faru ne? Na san Fauza sarai yadda kike maganan nan kuma kaman kina ɓoye damuwa ne a ƙasan ranki”

Tace
“Babu komai Farhan, ka tabbatar kayi duk abunda nace maka”

A ladabce yace
“To mammi”

Mikewa yayi ya fice.

***

Yana sauke wayan daga kunnenshi yayi shrugging kafadanshi, a ranshi yana furta
‘ina ma ruwana’

Ya gyara kwanciyar shi ya fara bacci gajiya tuni ya mance ma da wata Fauza.

Ita kuwa a ɓangarenta bacci take yi kaman gawa, ko Asuba bata iya ta tashi tayi ba, karfe takwas na safe wani irin amai ya tashe ta, da gudu ta nemi bayi ta fara kwararawa cikinta na Juyawa, saida ta gama tsab tana dafe da kanta dake sarawa kaman zae rabe gida biyu, a hankali ta wanke bakinta kan ta mike tsaye tana kallon bayin da take ɗin.

A hankali Tunanin abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo mata.

Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata, jarabar masifarta ta sa har bata gani da kyau, bata san sadda ta lalubo Kalmar “innalillahi wainna ilahi rajiun” ta fara ambata ba.

“He drugged me!” Da sauri ta kai idanunta jikinta, tana taɓawa hankalinta in yayi dubu ya tashi.

Da sauri ta fito daidai lokacin shima yake shigowa, kanta yayi yana furta
“Babe kin tash….”

Zazzafar Marin da ta sauke mishi hagu da dama ne ya saka magananshi ɗaukewa. Cikin ihu da masifa tace
“Zubair or what so ever, who the hell did you think you are da zaka yi drugging ɗina? U even had the audacity na bani kayan maye?”

Yace
“am sorry babe! Am so sorry don’t be mad I knew I messed up, but listen….”

“Ba zan yi listening ɗin ba, get the he’ll out of my way!”

Ta faɗa da karfi tana nufan waje, hannunta ya riƙo ta juya ta mishi wani wawan tura da saida ya faɗi kan kujerar ɗakin, da sauri ta fice tana danne hawayenta..

Tana fita ta nufi room da aka fara kama musu, abun takaici Bacci ta samu suke yi, toilet ta faɗa ta sakarwa kanta shower kan ta fashe da kuka, abu guda ya saura mata a hanyar da ta ɗauko shima yana zuwa, tunda har ta iya ɗanɗana kalar buguwa watarana zata faɗa zina.

Ta fi mintuna talatin kan ta fito, ta samu Sakina na waya, gata nan sir.

“Yayanki Farhan ne yaje office na vice wai yana son Magana dake”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected