Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Albashinka na wata nawa kake so?”
Ta watso mishi tambayar, wani fitinanniyar kallo ya watsa mata kasa kasa yace
“just one night stand please Fauxa na jima da ƙishirwanki”
Wani banzan kallo da ya kara kunna shi kanta ta mishi tace
“am not that kind in baka sani ba ma ya kamata ka sani just say your price!”
Rahama tace
“Sir please just say your price Fauxa ba irin waennan cheap matayen bane….”
“Before the count of three say your price or you loose the opportunity! And I must leave to Abuja”
Dukkansu uku kallonta suke da tsantsar mamaki, barin ma malamin wata iriyar yarinyace wannan? Me take nufi? Ba de hatsabibancin nata take shirin sauke mishi ba!
Be hankara ba ya ji ta ce “3”
Tana murmushi ta danna play a wayanta se ga muryarshi yana faɗin just one night stand please Fauxa wlh na jima da ƙishirwanki…
A razane yake kallonta zufa na yanko masa rahama da sakina suka saki murmushi lallai Fauxa ta ci lakabin da ake mata na
“Hadari malafar duniya, punkasau babban girki, biri da gatari ajalin mai gona, jan ƙasa na bayan ɗaki kowa ya ganki ya tuna Allah. Kadangaren bakin tulu; a barki ki ɓata ruwa a taɓa ki kuma a fasa tulu. Ba a banza ba, biri ke shan duka a rani, kowacce ze hadiye gatari zamu riƙe masa Kota…..”
Wannan kirari ne da babu wadda be san Fauxa dashi ba kuma har yanzu idan ana son ganin fara’arta cikakke to ka yi mata wannan kirarin shiyasa yawancin ƴan korensu da hakan suke cin kuɗin ta.
Cikin dage gira tace
“zaka rubuta mana takarda da sunan zuwa excursion na kwana biyar kuma mu uku kaɗai aka zaɓa daga makaranta. Sannan ka sani ka yi wa kanka don ko biyar ba zaka samu ba! Ka yi abinda na ce kan a tashi or else…”
Daga haka ta miƙe ta kaɗa mishi idanu ta juya ta fice suka bi bayanta suna murmushin irin zufan da yake Haɗawa….
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
09039206763
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na Goma*
*PAID BOOK*
*LAST FREE PAGES*
Babu yadda wannan malami da ya shiga tasku ya iya haka ya rubuta don tabbas ya san ƙaramin aikinta ne playing wannan audio wa school authorities daga nan kuma ya san aikinshi gabaɗaya ya rasa, time da ta bashi na cika ta zo ta karɓa tana yi mishi murmushin wulakanci irin nata.
Aiko tana isa gida Momma ta kaiwa don ta san daga momma ta amince to Baba Prof ma ya amince ta ci sa’a kuwa babu wadda ya hanata tafiyan suka shirya suka wuce akan ma Gombe ne bayan flight aka biya musu zuwa Abuja.
Karfe biyar na yamma suka sauka a birnin tarayya Abuja Motoci har biyu suka zo ɗaukar su Dukda duka duka su ukun ne kuma mota ɗaya suka shiga ɗaya na take musu baya, babban masaukin baƙin da har gomnoni da kusoshin gomnati ke sauƙa matukin motar tasu ya taka birki, masaukin baƙin ba baƙon su bane hakan yasa suka fito kowacce janye da karamar akwati mai taya suka yi ciki.
A reception suka haɗe da samarin sakina da rahama suka tarbe su har zuwa masaukin su me ɗauke da parlor da kuma ɗaki daga gani ka san na manya ne, a kujera ta yada zango tana bin su sakina dake lafe jikin samarin su da sunan oyoyo da idanu kan ta taɓe baki ta maida kanta ga wayanta tana cigaba da dannawa.
“Ƙawarmu kiyi ordering duk abunda kike so za’a kawo bari mu je mu zo”
Najeeb yaron ɗan majalisar tarayya kuma consultant saurayin sakina ya faɗa, kai kawai ta ɗaga musu su sakina suna daga mata hannu kan suka fice.
“Wallahi rahama kawarkun nan ta cika ji da kai kamar ƴar sarki”
Sakina ta taɓe baki tace
“kuma ba ƴar kowa ba ba”
Saurayin ta suhail wadda ɗa ne ga ministan lantarki kuma engineer yace
“ya zaki ce ba ƴar kowa ba ina gidan Prof kaka ne gidansu? Waye be san su ba a Nijeriya?”
Rahama tace
“sani daban wayewa daban, gidan kaman rijiya haka yake don ta samu mun fito da ita shine fa ta fimu feleke, ka ga kuwa manyan guys da take Juyawa? Iskancinta na da girma wallahi”
Anan suka bar maganan suka cigaba da harkokinsu na baɗala tsantsan rashin ilimin addini da rashin tarbiya suke nunawa a Filin Allah, ba kuma su damu da su su huɗu ne ɗakin ba.
Basu dawo masaukin su ba se dare lokacin fita partyn, sun sameta kwance ɗaure da towel tana bacci, tashin ta suka yi kan suka fara shiri suna hiran irin ɗauke hankali da suke son yi barin ma suhail da yace Zubair din jiji da kanshi na dayawa kuma en matan da zasu je wurin are high class hakan yasa suka ƙara zakewa kowacce ta fita fesss kaman ka sure ka gudu.
Wani arnen material lace aka yi mata fitted gown dashi wadda ya fitar da duk wani surarta yadda ya kamata ko numfashi me kyau bata yi amma dayake har ya fara bin jiki bata damu ba, kanta ko ɗan kwali babu se wani gyara da ta mishi jelar na reto a bayanta wani high hill shoe da inches ɗinshi ya kusa huɗu ta saka ta rike wayanta suka fito jewelrys ɗinta se dauke idanu suke.
A cikin hotel ɗin ne za’a yi sede ta chan baya, ba su isa wurin ba saida aka fara da ɗan jimawa.
Kwas Kwas Kwas haka karan takalmansu ya karaɗe ilahirin wurin wadda hakan ya saka celebrant ɗin da ya fara bayani cikin ƙasaita da ji da kai dakatawa.
Chak ya tsayar da fitilun ganinsa bisa kanta, Grey eyes ɗinta da ya ji liner se ɗauke hankali yake, Zubair be taɓa ganin halittar da ya tafi dashi a kallo ɗaya ba sai Akan wannan, don kasa cigaba da bayanin godiyan yayi Dukda su Fauxa har sun sama wa kansu mazauni, class ɗin yarinyar ya burgeshi kwarai don har ta zauna kaman bata san ta fisgi hankalin mutane dayawa daga wurin ba.
Taɓa shi da suhail yayi ya saka shi farga da ya ɓace a duniyar fauxa Dukda ko sanin ta be yi ba, bayanin ya karasa aka mishi tafi.
Yana ba da mic ya koma ya zauna mazaunin shi yana kallon suhail yace
“wacece wanchan? Na ganta da buduruwarka”
Suhail yace
“Zubair in zaka ɗauke kwalamarka kan wannan ka ɗauke sbd ta fi karfin duk yadda kake tunani”
Wani banzan kallo Zubair ya yiwa suhail ze yi magana Najeeb yace
“kaman yadda suhail ya faɗa nima shawaran da zan baka kenan…”
A fusace yace
“saboda ita ɗin ƴar waye kenan? Ta kaini? Ni da na Haɗa sarauta da mulki? Karka manta duk wata kwangila Indai daga fadar shugabar kasa ze fita hannuna yake zuwa, ina juya dala da euro so babu wannan magana, ko ka manta ni ɗin Burin kowacce macece da ta san rayuwa da abunda ya kunsa? Kalli ku ga duka en matan da suka taru anan sun yi ado da kwalliya ne sbd su burgeni har su sace zuciyata kuma kun san babu wacce babanta yake ƙaramin mutum me kuke min tsoro? har ta isa ta yarfa ni?”
Suhail ya ce
“ita ba ƴar kowa ba amma fa uncle ɗinta babu wadda be yi mishi tayin matsayi ba daga mulkin har sarauta ya ƙi, in kana jin Prof kaka to ƴar gidan ce, yarinya ce amma tana da kwarjinin manya daga jininsu ne”