Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Ta amsa da
“lafiya kalau ya gidan naki? Fatan dae baki bari ana hawa kanki kaman yadda kike da?”

Meyasa kowa ke mata nasiha ta zauna lafiya da mijinta amma mahaifiyarta kuma na shirin kawo rabuwar hankalinta?

“Ammi ai babu abunda suke min, muna zaune lafiya”

“mene? Ashe dama karyar kiyayya kike yiwa Faizan ɗin kenan, na tabbatar shi kuma a wurinshi ba haka take ba don kiyayyar namiji bata taɓa gushewa, kuma bata sauyawa, kiyi tunani dae… Sannan ki sani mijinki ba ke kaɗai ba har ni ba ƙaunata yake ba ke hatta mahaifinki don gani yake mahaifinki kusan rabi da kwatar dukiyarshi na Mahaifinsu ne shiyasa yanzu yake saka idanu akan harkokin business na babanki fiye da yadda yake sakawa Faraj da ya fara kula da na babansu”

Shiru tayi cikin dan nazari kan tace
“Ammi wannan duk ba wani abu bane, kilan ba yadda kike tunani bane don na san dukkaninmu da Baba Alhj da Baba prof duk iyaye muka ɗaukesu kuma matsayin abu guda babu banbanci, sannan Ammi ai maganan yaya Faizan baya kaunarki tun da nake na san yana zuwa gaishe ki amma baki taɓa buɗe baki kin amsa ba kuma har yau har gobe kenan be tsane ki b…..”

“Rufe min baki, ina nuna miki gabas kina yamma… Ke kika sani”
Tana kai nan ta kashe wayan..

Da idanu tabi wayan cikin mamakin Amminta, ta jima sossai tana nazari dayawa daga cikin ɗabi’un Ammin nata sede ta rasa a wani mataki ko matsayi zata ɗaura shi.

Baba prof ta kira shima yayi farin cikin jin tana cikin ƙoshin lafiya ya kuma yi mata albishir da result ɗinta na neco ya fito kuma yayi kyau don har yayiwa Faizan maganan yi mata registeration na jamb.

Taji daaɗi sossai tayi ta godiya da Adu’a ga baban, nasiha ya sake mata ya kuma gargadeta da Adu’a kaman yadda ya bata wani takarda da ke ɗauke da Adu’o’i masu yawa ya kuma umurceta da ta lazimcesu kuma tana yi ɗin sossai.

Bayan sun gama ta kira babanta shima ya ji daaɗin jinta lafiya ƙalau Dukda kullum a tsorace yake kar ta shukawa Faizan abunda ze zama silar tsinkewar zumuncinsu, idan har ze ga wayan Faizan se gabanshi ya faɗi da Tunanin ze ce mishi Fauza ta yi wani abun sede duk be ji ba, tun yana tsoracen yanzu har ya fara sakewa.

Nasiha shima yayi mata wadda be mata a lokacin barin ta gidan ba kuma ta ji daaɗi suka yi sallama tana ji matar nan na Mtn na cewa one minute remaining.

Sosa kai tayi bayan ta sauke tana kallon wayan yau ƙaniyarta Faizan ze ci ta ƙarar mai da katin waya.

Balcony ɗinta ta fita tana kallon harabar gidan da Gidajen unguwar da yawanci kusan irin nasu ne benaye, wayan ta sake ɗagowa ta shiga camera tare da Juyawa ya bata background ɗin unguwar Ta fara pictures style kala kala tana murmushi barin ma da taga yadda tayi kyau.

Seda ta gaji ta dawo ɗakin ta zauna a coffee chair ɗin tana kallon pictures ɗinta, tana cikin scrolling taga nata sun ƙare sun shiga na wayan, bata tsaya ba ta cigaba da scrolling yawanci hotunanshi ne wasu ya sani wasu be sani ba, daga yanayin hotunanshi zaka san yana da zafin kai don kusan duk babu wadda yake cikakken dariya banda na fuskan wayan.

A kan wani ta tsaya wadda aka dauke shi be sani ba shima da uniform ɗinne hannayenshi rike da abun tuka jirgin kunnenshi sanye da headphones ɗinsu ya ɗan wai go kaman ze yi magana ne aka ɗauka ba karamin kyau yayi ba.

Scrolling tayi ta wuce se taga hotonshi da Fatima, Fatiman ce ta ɗauka kwance a jikinshi kaman a wani wurin shakatawa ne, se wasu a bakin ruwa wadda ba tantama Legos ne don ta san chan ne kaɗai za’a samu beach haka, yana sanye da kananun kaya tana sanye da wasu hoodies orange, baki ta taɓe zata wuce se wayan ya ɗauki ringing.

‘My number’ ta ga an saka, to wani number kuma? Har wayan ya kusa katsewa kan tayi kundunbala ta ɗaga
“Fauziyya… Ina ta kiran Fatima bana samunta ki fita ki kama mata aiki su Faahim zasu kawo mana yini da yaran nima Ina dawowa nan ba da jimawa ba”

Kusan rikicewa tayi da sauri kuma tace
“Toh”
Kashe wayan yayi ba tare da ya sake furta komai ba.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke…a fili ta maimaita sunan nata
“Fauziyya..”
Sai de bata ji ya mata kaman yadda shi ya kira ɗin ba don har faɗar mata da gaba yayi.

Tuna su Ya fadyaa ne zasu zo yasa tayi saurin mikewa ta fito parlorn saman babu motsin Fatima don haka kasa tayi, ba wai tana tsoron Fatima ne yasa bata shiga kitchen ɗin saman ba, kawai tana tsayuwa ne limits ɗinta gudun fitina da tadawa iyayenta hankali, Allah kaɗai ya san yadda zuciyarta yayi haske da taji yadda suke farin cikin da jinta ba kaman da da a duk sadda za’a kira sunanta se gabansu ya fadi ba.

Abinci ta fara Haɗawa me rai da lafiya, Allah ya sa ma komai za’a kawo gidan a gyare ake kawo shi kuma cooker ɗin me kai har shidda ne a take ta Haɗa pineapple rice kamshinshi duk ya cika kitchen ɗin, bayan ta gama ta yi mishi pepper chicken, tayi grilling fish manya guda biyu se ta Haɗa zobo, karfe sha ɗaya da rabi lokacin kuma har lokacin bata ji motsin Fatima ba.

A dining na sama ta shirya su kan ta shiga ɗakinta tayi wanka, ta sanya wani material lace riga da skirt yayi mata kyau sossai ta fita shar da ita, lip gloss kawai ta shafa ta ɗaura dankwali harda sarka da abubuwan hannu ta saka.

Daidai lokacin take jin shigowar mota, farin ciki sossai ne ya ratsa ta yau zata kalli mutane, mutane su kalleta ko da basu wani yi shiri da ya fadyaa ba sbd rashin jinta yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya tana son ta kuma har ranta kaman yadda take jin sauran en uwanta

“oyoyo”
Ta faɗa tana rungume ya fadyaa, ya fadyaa ma na murmushi tace
“oyoyo Fauzan jadda, masha Allah.. Kin ganki kuwa?”

Da gudu yaranta biyu Asma’u(husna) da Sameer suka zo suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin daaɗi ta tarbesu, tana cewa ya Faahim
“sannu da zuwa yaya Faahim”

Yace
“uhm karki yi ya Faizan ya jiki ni yanzu ƙani nake, Aunty Fauxan Jaddah yauwa sannunki”

Dariya duk suka yi ta musu iso ciki dukkansu biyu kallonta suke yadda ta sauya, a parlorn sama suka baje suka fara Gaisawa ta kawo musu ruwa da fruits.

“Ina Fatima ne naji gidan shiru”
Fadyaa ta tambaya.

Fauxa na barewa husna lemon ɓawo tace
“nima fa tun safe bamu haɗu ba kilan tana ɗaki kila kuma ta tafi school”

Bayan ta bata ta dubi ya fadyaa tace
“ya fadyaa tun fa wanchan sati Jaddah tace min zaku dawo shine baku zo ba har se yau”

Ya Faahim yace
“ba gashi mun zo ɗin ba dae, Ya Faizan ya ce ya shiga wurin Faisal ko?”

Tace
“eh ya de ce gashinan zuwa”

Kallon juna Faahim da fadyaa suka yi suna gulma, yadda ake zaton jin hayaƙi a gidan Faizan ba haka ba, ashe igiyar aure na natsar da mutum?

“Kinga muna ta shirin tafiya ne zan ga Dr shi kuma ya Faahim ze yi wani course to har yanzu visa ɗin husna ne bamu samu ba gashi ma lokaci na ta tafiya”
Cewar Fadyaa

“ai na ce miki mu hakura mu barta wurin su mammi kin ce za’a kara mata dawainiya ga rashin lafiya”
Cewar Ya Faahim

Fauza tace
“to don Allah ni ku bar min ita kan ku je ku dawo Allah zata debi min kewa dama zaman kaɗaici ya isheni”

Zaro idanu fadyaa tayi tace
“Fauza rufa min asiri da mijinki…”

“Me mijinta yayi ne?”
Faizan ya faɗi yana shigowa cikin parlorn, duk ɗago idanu suka yi suna Kallonshi…

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected